+ All Categories
Home > Documents > Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? -...

Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? -...

Date post: 12-Apr-2018
Category:
Upload: hoangthu
View: 864 times
Download: 11 times
Share this document with a friend
226
MENENE Ainihi LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA?
Transcript

MENENE AinihiLITTAFI MAITSARKI YAKEKOYARWA?

LITTA

FIM

AI

TSA

RK

IYA

KE

KO

YA

RW

Abh

-HA

MENENE AinihiLITTAFI MAITSARKI YAKEKOYARWA?

Photo Credits: ˛ Shafi na 7: Courtesy American Bible Society ˛ Shafi na 19:Earth: NASA photo ˛ Shafuffuka na 24-25: WHO photo by Edouard Boubat

˛ Shafuffuka na 88–89: Explosion: Based on USAF photo;child: Based on WHO photo by W. Cutting

� 2005Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania

What Does the Bible Really Teach?

� 2005Wachtturm Bibel- und Traktat-Gesellschaft der Zeugen Jehovas, e.V.

Selters/TaunusMenene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

Bugun Satumba na 2013

Wannan littafin ba na sayarwa ba ne. Sashe ne na aikin ilimantarwa na Littafi Mai Tsarki adukan duniya wanda ake tallafa wa da gudummawar da aka ba da da son rai.

Sai dai ko an ba da alama, dukan wani Nassi an yi �aulinsa ne daga Litafi Mai-Tsarki.

What Does the Bible Really Teach?Hausa (bh-HA)

Made in GermanyAn Buga a Jamus

Druck und Verlag: Wachtturm-Gesellschaft, Selters/Taunus

WANNAN LITTAFIN NA

BABI SHAFI

Abin da Allah Ya Nufa Ke Nan? � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � 3

1. Mecece Koyarwa ta Gaskiya Game da Allah? � � � � � � � � � � � 8

2. Littafi Mai Tsarki—Littafi ne Daga Allah � � � � � � � � � � � � � � 18

3. Menene Allah ya Nufa ga Duniya? � � � � � � � � � � � � � � � � � � 27

4. Wanene Yesu Kristi? � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � 37

5. Fansa—Kyauta Mafi Girma Daga Allah � � � � � � � � � � � � � � � 47

6. Ina Matattu Suke? � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � 57

7. Bege na Gaskiya ga �aunatattunka da Suka Mutu � � � � � � 66

8. Menene Mulkin Allah? � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � 76

9. Muna Rayuwa ne a “Kwanaki na �arshe”? � � � � � � � � � � � � 86

10. Halittun Ruhu—Yadda Suke Shafanmu � � � � � � � � � � � � � � 96

11. Me Ya Sa Allah Ya �yale Wahala? � � � � � � � � � � � � � � � � � � 106

12. Rayuwa a Hanyar da Take Faranta wa Allah Rai � � � � � � � � 115

13. Ra’ayin Allah Game da Rai � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � 125

14. Yadda Za Ka Sa Rayuwar Iyalinka ta ZamaMai Farin Ciki � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � 134

15. Bauta da Allah Ya Amince da Ita � � � � � � � � � � � � � � � � � � � 144

16. Ka Dage Domin Bauta ta Gaskiya � � � � � � � � � � � � � � � � � � 154

17. Ka Kusaci Allah Cikin Addu’a � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � 164

18. Baftisma da Kuma Dangantakarka da Allah � � � � � � � � � � 174

19. Ka Tsare Kanka Cikin �aunar Allah � � � � � � � � � � � � � � � � 184

Rataye � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � 194

ABIN DA KE CIKI

KA KARANTA kowace jarida. Ka kalli te-libijin ko kuma ka saurari rediyo. A cikesuke da labarai na yin laifi, ya�i, data’addanci. Ka yi tunanin naka matsa-lolin. Wata�ila ciwo ko kuma mutuwarwanda kake �auna yana tada makahankali. Za ka ji kamar yadda mutuminarziki Ayuba ya ji, wanda ya ce “ina ba-�in ciki �warai.”—Ayuba 10:15.

Ka tambayi kanka:

ˇ Abin da Allah ya nufa mini da sau-ran ’yan Adam ke nan?

ˇ A ina zan sami taimako domin injimre wa matsalolina?

ˇ Da begen za mu ta�a samun sala-ma kuwa a duniya?

Littafi Mai Tsarki ya ba da amsoshimasugamsarwagawa�annantambayoyi.

Abin da Allah Ya Nufa Ke Nan?

GA ABIN DA ALLAH YA NUFAZAI YI GA DUNIYA KAMAR YADDA

LITTAFI MAI TSARKI YA KOYAR.

“Za ya share dukan hawaye kumadaga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta�ara kasancewa ba; ba kuwa za a �arayin ba�in zuciya, ko kuka, ko azaba.”

—Ru’ya ta Yohanna

“Gurgu za ya yi tatsalle kamar barewa.”

—Ishaya 35:5, 6.

“Za a bu�eidanun makafi.—Ishaya 35:5.

4

“Dukan wa�anda suna cikinkabarbaru za su . . .fito.”

—Yohanna 5:28, 29.

“Ba wandazai . . . �ara yin

kukan yana ciwo.”—Ishaya 33:24.

“Za a yi albarkar hatsi a �asa.”—Zabura 72:16.

KA AMFANA DAGA ABIN DA LITTAFIMAI TSARKI YAKE KOYARWA

Kada ka yi tunanin abin da akagabatar a shafuffuka na baya kamarkyakkyawan zato ne kawai. Allah yayi alkawarin zai yi wa�annan abubu-wa, kuma Littafi Mai Tsarki ya yibayani game da yadda zai yihakan.

Bugu da �ari, Littafi MaiTsarki zai taimake mu ahanyoyi masu yawa. Ma-bu�inenahanyar samunrayuwa mai gamsar-wa da gaske har a yanzu.Ka �an yi tunani gameda damuwanka da kumamatsalolinka. Wata�ila sunha�a da matsalar ku�i, matsala taiyali, rashin lafiya, ko kuma rasuwarwanda kake �auna. Littafi Mai Tsarki zaiiya taimakonka ka magance matsalolinka a yau, kuma zai iyakwantar maka da hankali ta wajen amsa tambayoyi irin su:

ˇ Me ya sa muke wahala?

ˇ Ta yaya za mu jimre wa damuwa na rayuwa?

ˇ Ta yaya za mu kyautata farin cikin iyalinmu?

ˇ Menene yake samun mu sa’ad da muka mutu?

ˇ Za mu sake ganin ’yan’uwanmu da suka rasu kuwa?

ˇ Ta yaya za mu tabbata cewa Allah zai cika wa�annanalkawuransa game da rayuwa ta nan gaba?

6 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

Ganin cewa kana karanta wannan littafin ya nuna cewakana so ka fahimci abin da Littafi Mai Tsarki yake koyar-wa. Wannan littafin zai taimake ka. Ka kula cewa kowanesakin layi yana da nasa tambaya a �asan shafin. Miliyoyinmutane sun ji da�inwannan salon nazari na tambayoyi daamsoshi wajen nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jeho-bah. Muna fatan kai ma za ka ji da�insa. Allah ya yi makaalbarka sa’ad da kake fahimtar abin da ainihi Littafi MaiTsarki yake koyarwa!

KA SAN LITTAFINKA MAI TSARKI

LITTATTAFAI da wasi�u 66 ne suke cikin Littafi Mai Tsarki. Wa-�annan an rarraba su zuwa surori da ayoyi domin sau�inkaratu. Sa’ad da aka ja aya a wannan littafin, lamba ta far-ko bayan sunan yana nufin sura na littafi na Littafi Mai Tsar-ki ko kuma wasi�a, bayan kuma yana nufin aya. Alal misali,“2 Timothawus 3:16” yana nufin wasi�a ta biyu ga Timo-thawus, sura 3, aya 16.

Ba da da�ewa ba za ka saba da Littafi Mai Tsarki ta wajenbincika nassosi da aka ja a wannan littafin. Kuma me ya sa baza ka kafa tsarin karatun Littafi Mai Tsarki kullum ba? Ta wa-jen karanta sura biyu ko uku kowace rana, za ka karanta Litta-fi Mai Tsarki gaba �aya a cikin shekara �aya.

Abin Da Allah Ya Nufa Ke Nan? 7

KA TA�A lura da yadda yara suke yin tambaya? Da yawasuna fara tambaya da zarar sun fara magana. Da idanunsu abu�e su dube ka su yi tambaya kamar su: Me ya sa gajimareyake shu�i? Da me aka yi taurari? Wa ya koya wa tsuntsayekuka? Za ka yi �o�ari �warai ka ba da amsa, amma ina, yanada wuya. Kyakkyawar amsa da za ka bayar, za ta sa su saketambaya: Me ya sa?

2 Ba yara ba ne kawai suke yin tambayo-yi. Sa’ad da muke girma, muna ci gabada tambayoyi. Muna yin haka ne dominmuna neman tafarkinmu, domin munaso mu fahimci ha�ari da za mu guje wa,ko kuma domin mu gamsar da �wa�-warmu. Amma mutane da yawa sunadaina yin tambayoyi, musamman mamafiya muhimmanci. Ko kumasu daina neman amsoshi.

3 Ka yi tunanin tambaya datake bangon wannan littafin,

1, 2. Me ya sa yake da kyau a yi tambayoyi?3. Me ya sa mutane da yawa suke daina �o�arinneman amsoshin tambayoyi da suka fi muhim-manci?

BABI NA �AYA

Mecece Koyarwa ta GaskiyaGame da Allah?

Allah ya damu da kai kuwa da gaske?

Yaya kamanin Allah? Yana da suna kuwa?

Shin yana yiwuwa a kusaci Allah kuwa?

da wa�anda suke shafin gabatarwa, ko kuwa wa�anda akayi a farkon wannan babin. Wa�annan sune tambayoyi ma-fiya muhimmanci da za ka yi. Duk da haka, mutane dayawa sun ba da gari wajen neman amsoshin tambayoyin.Me ya sa? Littafi Mai Tsarki zai iya ba da amsoshin kuwa?Wasu suna jin cewa za su yi wuyar fahimta. Wasu kuma sundamu cewa yin tambayoyi zai kai ga jin kunya. Wasu kumasun ce irin wa�annan tambayoyi ya kamata a �yale su gamalaman addini da shugabanninsu. To me kake tsammani?

4 Wata�ila, kana so ka sami amsoshi ga muhimman ma-tsaloli na rayuwa? Babu shakka wani lokaci kana mamaki:‘Menene manufar rayuwa? Wannan shi ne muhimmancinrayuwa? Yaya ainihi kamanin Allah?’ Yana da muhimmancimu yi irin wa�annan tambayoyin, yana kuma da muhim-manci ka ci gaba da neman amsa har sai ka sami amsa tagaskiya mai tabbaci. Babban malami Yesu Kristi ya ce: “Kuro�a, za a ba ku; ku nema, za ku samu; ku �wan�wasa, za abu�e muku.”—Matta 7:7.

5 Idan ka ‘yi ta neman’ amsoshi ga wa�annan tambayo-yi masu muhimmanci, za ka sami alheri. (Misalai 2:1-5)Ko menene mutane suka gaya maka, ana samun amsoshi,kuma kana iya samunsu—a cikin Littafi Mai Tsarki. Amso-shin ba su da wuyar fahimta. Mafi muhimmanci ma, sunaba da bege da farin ciki. Kuma za su iya taimakonka ka yirayuwa mai gamsarwa a yanzu. Da farko, bari mu bincikatambaya da ta dami mutane da yawa.

SHIN ALLAH MARAR �AUNANE MAI TAURIN ZUCIYA?

6 Mutane da yawa suna tsammanin amsar wannan tam-bayar e ce. Suna tunani ‘Idan Allah yana �aunar duniya, ba

4, 5. Wa�anne tambayoyi ne suke da muhimmanci �warai a rayuwada za mu iya yi, me ya sa za mu nemi amsa?6. Me ya sa mutane da yawa suke tunanin cewa Allah bai damu damatsalolin mutane ba?

Mecece Koyarwa ta Gaskiya Game da Allah? 9

za ta kasance kyakkyawar wuri ba?’ Duniya wuri ce da takecike da ya�e-ya�e, �iyayya, da wasu matsaloli. Kuma dukan-mu, muna yin rashin lafiya, muna wahala, muna rashinwa�anda muke �auna. Saboda haka, mutane da yawa sukance, ‘Idan Allah yana �aunarmu kuma ya damu da matsalo-linmu, da ba zai hana wa�annan abubuwa faruwa ba?’

7 Fiye ma da haka, malaman addini a wasu lokatai sunasa mutane su yi tunanin cewa Allah mai taurin zuciya ne.Ta yaya? Sa’ad da masifa ta fa�o, sai su ce nufin Allah ne.Wato, irin wa�annan malamai suna �ora wa Allah alhakinmunanan abubuwa da suke faruwa. Amma hakan gaskiyane game da Allah? Menene ainihi Littafi Mai Tsarki yake ko-yarwa? Ya�ub 1:13 ta ba da amsa: “Kada kowa sa’anda yajarabtu ya ce, Daga wurin Allah ne na jarabtu: gama Al-lah ba shi jarabtuwa da mugunta, shi kuwa da kansa ba shijarabci kowa ba.” Saboda haka ba Allah ba ne sababin mu-gunta da kake gani a duniya. (Ayuba 34:10-12) Hakika, yana�yale miyagun abubuwa su faru. Amma da bambanci tsaka-nin �yale abu da kuma haddasa shi.

8 Alal misali, ka yi tunanin mutum mai hikima mai �au-na da yaronsa ya girma amma suna tare a gida �aya.Sa’ad da yaron ya yi tawaye, ya nemi ya bar gidan, baban-sa zai hana shi ne?. Idan yaron ya shiga muguwar rayuwaya fa�a cikin masifa. Babansa ne ya jawo masa masifar?A’a. (Luka 15:11-13) Hakazalika, Allah bai hana mutane basa’ad da suka za�i muguwar rayuwa, amma ba shi ne saba-bin matsalarsu ba. Hakika, ba zai dace ba a �ora wa Allahalhakin matsalolin ’yan Adam.

9 Allah yana da kyakkyawan dalili na �yale mutane su bi

7. (a) Ta yaya malaman addini suka sa mutane da yawa suka yi tuna-nin cewa Allah mai taurin zuciya ne? (b) Menene ainihi Littafi MaiTsarki yake koyarwa game da jarabta da muke fuskanta a yau?8, 9. (a) Ta yaya za ka kwatanta bambanci da ke tsakanin �yale mu-gunta ta wanzu da kuma haddasa ta? (b) Me ya sa bai dace ba mu �orawa Allah alhaki domin ya �yale ’yan Adam su bi mugun tafarki?

10 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

mugun tafarki. Tun da Mahalicci ne mai hikima mai iko, badole ba ne ya yi mana bayanin dalilinsa na yin haka. AmmaAllah ya yi haka ne domin �auna. Za ka fahimci wa�annandalilai a Babi na 11. Amma ka tabbata cewa ba Allah yake daalhakin matsaloli da muke fuskanta ba. Maimakon haka, yayi mana alkawarin magance su!—Ishaya 33:2.

10 Bugu da �ari, Allah mai tsarki ne. (Ishaya 6:3) Wannanyana nufin cewa marar aibi ne mai tsabta. Babu ko �igonmugunta a gare shi. Saboda haka za mu iya dogara sosai agare shi. Ba za mu iya dogara ga mutane ba haka, dominwani lokaci suna lalacewa. Mutum mai gaskiya da yake sa-rauta sau da yawa ba shi da ikon gyara abin da miyagunmutane suka yi. Amma Allah yana da iko marar iyaka. Zaiiya gyarawa kuma zai gyara dukan yadda mugunta ta shafi’yan adam. Sa’ad da Allah ya yi haka, zai yi hakan ne a han-yar da za ta kawo �arshen mugunta har abada!—Zabura 37:9-11.

YAYA ALLAH YAKE JI GAME DA RASHINGASKIYA DA MUKE FUSKANTA?

11 Yaya Allah yake ji a yanzu game da abin da yake faruwaa duniya da kuma a rayuwarka? Littafi Mai Tsarki ya ko-yar da cewa Allah “yana son shari’a.” (Zabura 37:28) Sabodahaka ya damu �warai game da abin da ke mai kyau da abinda ke mugu. Yana �in dukan rashin adalci. Littafi Mai Tsar-ki ya ce sa’ad da mugunta ta cika duniya a da “abin ya �atamasa [Allah] zuciya kuma.” (Farawa 6:5, 6) Allah bai sakeba. (Malachi 3:6) Har yanzu yana �in irin wahala da yakegani a dukan duniya. Kuma Allah ba ya son ganin muta-ne suna wahala. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yana kula da ku.”—1 Bitrus 5:7.

10. Me ya sa za mu gaskata cewa Allah zai gyara dukan matsalar mu-gunta?11. (a) Yaya Allah yake ji game da rashin adalci? (b) Yaya Allah yakeji game da wahalarka?

Mecece Koyarwa ta Gaskiya Game da Allah? 11

12 Ta yaya za mu tabbata cewa Allah ba ya son ganinmuna wahala? Ga �arin tabbaci. Littafi Mai Tsarki ya koyarda cewa Allah ya halicci mutum a kamaninsa. (Farawa 1:26)Muna da halayen kirki domin Allah yana da halayen kirki.Alal misali, kana damuwa idan ka ga mutane marasa laifisuna wahala? Idan ka damu da irin wannan rashin adalci,ka tabbata cewa abin ya ma fi damun Allah.

13 Wani abin da ke mai kyau game da mutane shi necewa suna iya nuna �auna. Wannan yana nuna koyi da Al-lah. Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa “Allah �auna ne.”(1 Yohanna 4:8) Muna �auna domin Allah mai �auna ne.�auna za ta iya motsa ka ka kawo �arshen rashin adalci

da kake gani a wannan duniyar? Idankana da ikon ka yi haka, ba za ka yi bane? Hakika, za ka yi hakan! Ka tabba-ta cewa Allah zai kawo �arshen wahalada rashin adalci. Alkawura da aka am-bata a gabatarwa ta wannan littafin bamafarki ba ne ko kuma bege marar tu-she. Alkawuran Allah hakika za sukasance gaskiya! Domin ka ba da gas-kiya ga irin wa�annan alkawura, kanabukatar ka fahimci Allahn da ya yi su.

ALLAH YANA SO KA SAN KOWANENE SHI

14 Idan kana so mutum ya san ka,menene za ka yi? Ba za ka gaya wa mu-tumin sunanka ba? Shin Allah yana

12, 13. (a) Me ya sa muke da halayen kirkiirin su �auna, kuma ta yaya �auna take sha-fan ra’ayinmu game da duniya? (b) Me ya saza ka tabbata cewa Allah zai yi wani abu gameda matsaloli na duniya?14. Menene sunan Allah, kuma me ya sa zamu yi amfani da shi?

Idan kana somutum ya san ka,ba sunanka za kagaya masa ba?Allah ya sanar damu sunansa cikinLittafi Mai Tsarki

12 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

da suna kuwa? Addinai da yawa za su amsa cewa sunansa“Allah” ne ko kuma “Ubangiji,” amma wa�annan ba su-naye ba ne. Sunayen sarauta ne kamar yadda “sarki” da“shugaban �asa” suke sunayen sarauta. Littafi Mai Tsarki yakoyar da cewa Allah yana da sunayen sarauta masu yawa.“Allah” da “Ubangiji” suna cikin wa�annan. Amma kuma,Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa Allah yana da suna:Jehobah. Zabura 83:18 ta ce: “Domin su sani kai, wan-da sunanka Jehovah ne, kai ka�ai ne Ma�aukaki bisa dukanduniya.” Idan fassarar Littafin Mai Tsarki naka bai �unshiwannan sunan ba, kana iya tuntu�ar Rataye a shafuffukana 195-197 na wannan littafin domin ka fahimci abin da

Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewaJehobah shi ne Mahalicci mai �auna

na sararin samaniya

ya sa. Gaskiya ita ce, sunan Allah ya bayyana sau dubbaia cikin Littafi Mai tsarki na da. Saboda haka, Jehobah yanason ka san sunansa kuma ka kira shi da shi. Ana iya cewa,ya yi amfani ne da Littafi Mai Tsarki wajen gabatar maka dakansa.

15 Allah ya bai wa kansa suna da yake cike da ma’ana. Su-nansa, Jehobah, yana nufin cewa Allah zai iya cika dukanwani alkawari da ya yi kuma zai yi dukanwani nufi da ke ci-kin zuciyarsa.� Sunan Allah ba na biyunsa. Shi ka�ai yakeda wannan suna. Jehobah ya bambanta a hanyoyi masuyawa. Ta yaya?

� Domin �arin bayani game da ma’ana da kuma yadda za a furtasunan Allah dubi rataye a shafuffuka na 195-197.

15. Menene sunan nan Jehobah yake nufi?

�auna da uba yakeda ita ga yaransa

tana kwatanta�auna mai yawa

da Ubanmuna samaniya yake

da ita a gare mu

14 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

16 Mun gani a Zabura 83:18 cewa Jehobah: ‘Kai ka�ai neMa�aukaki.’ Hakika, Jehobah ne ka�ai ake cewa “Ma�auka-ki.” Ru’ya ta Yohanna 15:3 ta ce: “Ayyukanka masu-girmane, masu-ban al’ajabi, ya Ubangiji Allah, Mai-iko duka;halullukanka kuma masu-adalci ne, masu-gaskiya kuma, yaSarkin zamanai.” Sunan sarautan nan “Ma�aukaki” ya koyamana cewa Jehobah shi ne ya fi kowa iko. A iko ba wan-da ya yi daidai da shi; shi ne mafifici. Sunan sarauta ‘Sarkinzamanai’ ya nuna mana cewa Jehobah ya bambanta a watahanya kuma. Shi ka�ai ya wanzu a dukan lokaci. Zabura90:2 ta ce: “Tun fil’azal kai ne Allah har abada.” Wannanbatu ne mai ban tsoro, ko ba haka ba?

17 Jehobah ya kuma bambanta domin shi ka�ai ne Maha-licci. Ru’ya ta Yohanna 4:11 ta ce: “Kai ne mai-isa ka kar�i�aukaka da daraja da iko, ya Ubangijinmu da Allahnmu:gama kai ka halicci dukan abu, saboda nufinka kuma sukakasance, saboda nufinka aka halicce su.” Duk abin da ka yitunaninsa, daga halittun ruhu marasa ganuwa zuwa taurarida ke sararin samaniya zuwa ’ya’yan itatuwa zuwa kifaye dasuke iyo cikin teku da koguna dukansu sun wanzu ne do-min Jehobah ya halicce su!

ZA KA IYA KUSANTAR JEHOBAH KUWA?18 Karatu game da halaye masu ban tsoro na Jehobah ya

sawasu sun �an razana. Suna jin cewa Allah ya fiye fifita, sa-boda haka suna ganin ba za su ta�a kusantarsa ba, dominba zai �auke su wani abu ba. Amma wannan ra’ayin gaski-ya ne? Littafi Mai Tsarki bai koyar da haka ba. Ya ce game daJehobah: “Ba shi da nisa da kowane �ayanmu ba.” (AyukanManzanni 17:27) Littafi Mai Tsarki ya aririce mu: “Ku kusa-to ga Allah, shi kuwa za ya kusato gareku.”—Ya�ub 4:8.

16, 17. Menene za mu koya daga wa�annan sunayen sarauta na Je-hobah: (a) “Ma�aukaki? (b) “Sarkin zamanai”? (c) “Mahalicci”?18. Me ya sa wasu mutane suke jin cewa ba za su ta�a kusantar Allahba, amma menene Littafi Mai Tsarki ya koyar?

Mecece Koyarwa ta Gaskiya Game da Allah? 15

19 Ta yaya za ka kusaci Allah? Da farko, ka ci gaba daabin da kake yi a yanzu, koya game da Allah. Yesu yace: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah maka�ai-ci mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.”(Yohanna 17:3) Hakika, Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewasanin Jehobah da kuma Yesu zai kai ga “rai madawwa-mi”! Kamar yadda ka sani, “Allah �auna ne.” (1 Yohanna4:16) Jehobah har ila yana da kyakkyawan halaye masuda�a�awa. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah “Al-lah ne cike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi,mai-yalwar jin�ai da gaskiya.” (Fitowa 34:6) “Nagari nekai, ya Ubangiji, mai-hanzarin gafartawa.” (Zabura 86:5)Allah mai ha�uri ne. (2 Bitrus 3:9) Shi mai aminci ne.(Ru’ya ta Yohanna 15:4) Sa’ad da ka ci gaba da karantaLittafi Mai Tsarki, za ka ga yadda Jehobah ya nuna cewayana da dukan wa�annan halaye da kuma wasu masu bansha’awa.

20 Hakika, ba za ka iya ganin Allah ba domin shi ruhu nemarar ganuwa. (Yohanna 1:18; 4:24; 1 Timothawus 1:17) Tawajen koyo game da shi daga Littafi Mai Tsarki, za ka sanshi �warai. Kamar yadda mai zabura ya ce za ka “dubi jama-lin [Jehobah].” (Zabura 27:4; Romawa 1:20) Da zarar ka koyigame da Jehobah, haka nan za ka fahimce shi kuma haka zaka �ara �aunarsa kuma ka kusace shi.

21 A hankali za ka fahimci abin da ya sa Littafi Mai Tsar-ki ya koyar da mu mu �auki Jehobah a madadin Ubanmu.(Matta 6:9) Ba domin shi ya ba mu rai ba kawai ammakuma domin yana so mu sami rayuwa tagari, kamar yad-da uba mai �auna zai so ga yaransa. (Zabura 36:9) LittafiMai Tsarki kuma ya koyar da mu cewa mutane za su

19. (a) Ta yaya za mu fara kusantar Allah, kuma ta yaya za mu amfa-na? (b) Wane hali ne na Allah ya fi burge ka?20-22. (a) Domin ba ma ganin Allah wannan zai hana mu ne mu ku-sace shi? Ka yi bayani. (b) Menene wasu mutane masu nufin kirki zasu ce ka yi, amma me ya kamata ka yi?

16 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

iya zama abokanan Jehobah. (Ya�ub 2:23) Kana iya zamaabokin Mahaliccin dukan sararin samaniya—abin ma-maki!

22 Sa’ad da ka ci gaba da koyo daga Littafi Mai Tsarki, zaka ga cewa wasu mutane masu nufin kirki za su ce makaka daina nazarin. Za su damu cewa za ka sake abin da kagaskata. Amma kada ka bar kowa ya hana ka �ulla wannanabota mafi kyau da za ka iya �ullawa.

23 Hakika, da akwai abubuwa da ba za ka fahimta ba dafarko. Neman taimako zai bukaci laushin hali a gare ka,amma kada ka �i yin haka domin kunya. Yesu ya ce yana damuhimmanci mu �as�antar da kai, kamar �an yaro. (Matta18:2-4) Yara kuma kamar yadda muka sani, suna da yawantambaye-tambaye. Allah yana son ka sami amsoshi. LittafiMai Tsarki ya yabi wasu da suka yi �okin su koyi game daAllah. Sun yi bincike cikin Nassosi a tsanake domin su tab-bata ko abin da suke koya gaskiya ne.—Ayukan Manzanni17:11.

24 Hanya mafi muhimmanci na koyo game da Jehobahita ce bincika Littafi MaiTsarki. Ya bambanta da dukanwanilittafi. A wace hanya? Babi na gaba zai yi bayani a kan wan-nan batun.

23, 24. (a) Me ya sa ya kamata ka ci gaba da tambayoyi game da abinda kake koya? (b) Menene za a yi bayani a babi na gaba?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

ˇ Allah yana �aunarka.—1 Bitrus 5:7.

ˇ Sunan Allah Jehobah ne.—Zabura 83:18.

ˇ Jehobah yana gayyatarka ka kusace shi.—Ya�ub 4:8.

ˇ Jehobah yana da �auna, da alheri, da jin�ai.—Fitowa 34:6.

Mecece Koyarwa ta Gaskiya Game da Allah? 17

KA TUNA lokacin da abokinka abin �auna ya yi maka kyau-ta? Wata�ila, wannan ta faranta maka rai matu�a kuma tasa ka yi godiya. Hakika, kyautar ta nuna maka wani abugame da mai bayarwa, mai bayarwan yana ko tana mutun-ta abota da ke tsakaninku. Babu shakka, ka yi godiya dominzurfin tunanin abokinka.

2 Littafi Mai Tsarki kyauta ne daga Allah, wanda ya kaimu yi godiya gaya. Wannan littafin ya bayyana abubuwanda ba za mu ta�a sani ba idan ba domin sa ba. Alal misali,ya gaya mana game da halittar taurarin samaniya, game daduniya, game da mata da miji na fari. Littafi Mai tsarki ya�unshi mizanai da za su taimake mu mu jimre wa matsalo-li da damuwa na rayuwa. Ya yi bayani game da yadda Allahzai cika nufinsa kuma ya kawo yanayi mai ni’ima a duniya.Hakika Littafi Mai Tsarki kyauta ne mai ba da farin ciki!

3 Littafi Mai Tsarki kyauta ne mai ban sha’awa, domin ya

1, 2. A wa�anne hanyoyi ne Littafi Mai Tsarki kyauta ne mai ba dafarin ciki daga Allah?3. Menene muka koya game da Jehobah daga kyautar Littafi Mai Tsar-ki da ya yi mana, kuma me ya sa wannan yake da ban sha’awa?

BABI NA BIYU

Littafi Mai Tsarki—Littafi Ne Daga Allah

A wa�anne hanyoyi ne Littafi Mai Tsarki yabambanta da dukan wani littafi?

Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai taimake ka kamagance matsalolinka?

Me ya sa za ka yarda da annabce-annabcen dasuke rubuce cikin Littafi Mai Tsarki?

bayyana wani abu game da mai bayarwa, Jehobah Allah.Da yake ya ba da irin wannan littafin, hakan ya tabbatar dacewa yana so mu san shi da kyau. Hakika, Littafi Mai Tsarkizai taimake mu mu kusaci Jehobah.

4 Idan kana da Littafi Mai Tsarki, da mutane da yawakamar ka. An fassara Littafi Mai Tsarki cikakkensa ko rabin-sa cikin fiye da harsuna 2,300, saboda haka yana samuwaga fiye da kashi 90 na mutanen duniya. A matsakaicinsaana raba Littafi Mai Tsarki fiye da miliyan kowane mako! Anbuga biliyoyi a cikakkensa ko kuma rabinsa. Hakika, babuwani littafi kamar Littafi Mai Tsarki.

5 Bugu da �ari, Littafi Mai Tsarki “hurarre daga wurin Al-lah” ne. (2 Timothawus 3:16) A wace hanya? Littafi MaiTsarki kansa ya amsa: “Mutane suka yi magana daga wurinAllah, Ruhu Mai-tsarki ne yana motsa su.” (2 Bitrus 1:21)Alal misali: �an kasuwa yana iya sa sakatarensa ya rubutawasi�a. Wannanwasi�ar za ta �unshi lafazi da umurnin �ankasuwan. Saboda haka, wasi�ar hakika ta �an kasuwan ne,

4. Menene ya burge ka game da yadda Littafi Mai Tsarki ya bambanta?5. A wace hanya ce Littafi Mai Tsarki “hurarre daga wurin Allah” ne?

The “New World Translation of the Holy Scriptures”ana samun sa a cikin harsuna da yawa

19

ba ta sakatarensa ba. Hakazalika, Littafi Mai Tsarki ya �un-shi sa�on Allah ne, ba na mutanen da suka rubuta shi ba.Saboda haka, Littafi Mai Tsarki gaba �ayansa “maganar Al-lah” ne.—1 Tassalunikawa 2:13.

CIKAKKE NE KUMA MAI JITUWA6 Rubuta Littafi Mai Tsarki ya �auki fiye da shekara 1,600.

Marubutansa sun rayu a zamani dabam dabam kuma sunfito ne daga yanayin rayuwa dabam dabam. Wasunsu ma-noma ne, wasu mas

¯unta, wasu kuma makiyaya ne. Wasu

annabawa ne, wasu mahukunta, wasu sarakuna. Marubu-cin Linjila Luka likita ne. Duk da bambance bambancenmarubutansa, Littafi MaiTsarki ya jitu daga fari har �arshe.�

7 Littafi na farko na Littafi Mai Tsarki ya fa�a mana yaddamatsalar ’yan Adam ta fara. Littafi na �arshe ya nuna manayadda dukan duniya za ta zama aljanna, ko kuma lam-bu. Dukan littattafai na Littafi Mai Tsarki sun ba da tarihinshekaru dubbai na rayuwa da kuma yadda suka shafi cikarnufin Allah. Jituwa na Littafi Mai Tsarki tana da ban sha’a-wa, kuma haka littafi daga Allah ya kamata ya kasance.

8 Littafi Mai Tsarki cikakke ne a batun kimiyya. Ya �unshibayani ma da ya wuce na zamaninsa. Alal misali, Leviticusyana �auke da dokoki domin Isra’ila ta d

¯a game da ke�ewa

da kuma tsabta sa’ad da al’ummai da suke ma�wabtaka dasu ba su san kome ba game dawannan. Sa’ad da ba a fahim-ci siffar duniya ba, Littafi Mai tsarki ya ce duniya tana kamada �wai. (Ishaya 40:22) Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ya ‘ra-

� Ko da yake wasu mutane sun ce wasu �angarori na Littafi Mai Tsar-ki ba su jitu da wasu �angarori ba, wannan da’awar ba ta da tushe. Kadubi babi na 2 na littafin nan Sanin da ke Bishe Zuwa Rai na Har Aba-da da Shaidun Jehobah suka wallafa.

6, 7. Me ya sa jituwa ta littattafai na Littafi Mai Tsarki abin kula nemusamman?8. Ka ba da misalin da zai nuna cewa Littafi Mai Tsarki cikakke ne abatun kimiyya.

20 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa

taye duniya ba bisa kome ba.’ (Ayuba 26:7) Hakika, LittafiMai Tsarki ba littafin kimiyya ba ne. Amma sa’ad da ya yimagana a kan batun kimiyya daidai yake. Ba haka za mu yitsammanin littafi daga wurin Allah ba?

9 Littafi Mai Tsarki abin dogara ne wajen tarihi. Labaransatakamammu ne. Ya �unshi sunayen mutane har da tarihinzuriyarsu.�Yabambanta da ’yan tarihi, wa�anda saudayawaba sa fa�an yadda aka ci mutanensu a ya�i, marubutan Lit-tafi Mai Tsarki masu gaskiya ne, sun rubuta har kurakuransuda na al’ummarsu. Alal misali a cikin littafin Lissafi, maru-buci Musa ya fa�i kurensa mai tsanani wanda ya sa aka yimasa horo. (Littafin Lissafi 20:2-12) Irin wannan gaskiya bata samuwa a cikin wasu littattafan tarihi amma tana samu-wa cikin Littafi Mai Tsarki domin littafin Allah ne.

LITTAFI CIKE DA HIKIMA10 Domin Littafi Mai Tsarki hurarre ne daga Allah yana da

amfani wajen “koyarwa, ga tsautawa, ga kwa�ewa, ga horokuma.” (2 Timothawus 3:16) Hakika, Littafi Mai Tsarki litta-fi ne mai amfani. Ya nuna fahimi sosai ga yanayi na ’yanAdam. Ba abin mamaki ba ne—Mawallafinsa Jehobah Allah,shi ne Mahalicci! Ya san tunaninmu da motsin zuciyarmufiye da yadda muke tsammani. �ari ga haka, Jehobah ya sanabin da muke bukata domin mu yi farin ciki. Ya san kumatafarkin da ya kamata mu guje wa.

11 Ka yi la’akari da jawabin Yesu da ake kira Hu�uba bisa

� Alal misali, ka kula da cikakken zuriyarar Yesu da aka rubuta aLuka 3:23-38.

9. (a) A wa�anne hanyoyi ne Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa tari-hinsa cikakken ne kuma abin dogara? (b) Menene fa�in gaskiya namarubutansa ya nuna maka game da Littafi Mai Tsarki?10. Me ya sa ba abin mamaki ba ne cewa Littafi Mai Tsarki littafi nemai amfani?11, 12. (a) Wa�anne batutuwa Yesu ya yi magana a kan su a Hu�u-ba a kan Dutse? (b) Wa�anne batutuwa aka yi maganarsu cikin LittafiMai Tsarki, kuma me ya sa wannan garga�i ba shi da lokaci?

Littafi Mai Tsarki—Littafi ne Daga Allah 21

Dutse, da ke rubuce a Matta surori 5 zuwa 7. A cikinwannanfitacciyar koyarwarsa, Yesu ya yi magana game da abubuwada yawa, har da yadda za a sami farin ciki na gaske, yadda zaa yi sulhu, yadda za a yi addu’a, da yadda za a �auki abinduniya. Kalmomin Yesu suna da amfani a yau kamar yaddasuke sa’ad da ya fa�e su.

12 Wasu mizanan Littafi Mai Tsarki suna magana ne gameda zaman iyali, yadda za a yi aiki, da kuma dangantaka da

Marubucin LittafiMai Tsarki Ishayaya annabtahalakar Babila

wasu. Mizanan Littafi Mai Tsarki ya shafi dukan mutane,kuma garga�insa a kullayaumi yana da amfani. Hikima datake cikin Littafi Mai Tsarki an ta�aita ta cikin kalmar Allahta bakin annabi Ishaya: “Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda yake koya maka zuwa amfaninka.”—Ishaya 48:17.

LITTAFI NE NA ANNABCI13 Littafi Mai Tsarki ya �unshi annabce-annabce masu

yawa, da yawa kuma cikinsu sun riga sun cika. Ga wanimisali. Ta bakin annabi Ishaya, wanda ya rayu a �arni natakwas K.Z., Jehobah ya annabta cewa birnin Babila za a ha-laka ta. (Ishaya 13:19; 14:22, 23) An ba da bayani dalla-dallaa nuna yadda za a halaka birnin. Sojoji mahara za su jan-ye ruwan kogin Babila kuma su shiga cikin birnin ba tareda �auki ba da�i ba. Da �ari ga wannan. Annabcin Ishayahar ya ba da sunan sarkin da zai ci Babila—Cyrus.—Ishaya44:27–45:2.

14 Shekaru 200 bayan haka—a daren 5 ko 6 ga Oktoba,539 K.Z., dakaru suka yi zango a kusa da Babila. Waye neshugabansu? Sarkin Fasiya mai suna Cyrus. Hanya ta bu�ena cika annabci da ban mamaki. Amma sojojin Cyrus za sushiga Babila ne ba tare da sun yi �auki ba da�i ba kamaryadda aka annabta?

15 A wannan daren mutanen Babila suna cikin biki kumasuna jin babu dalilin tashin hankali domin manyan ganu-wansu. Cyrus kuma cikin hikima ya kawar da ruwan koginda ya bi cikin birnin. Ba da da�ewa ba ruwan ya janye yaddasojojinsa za su iya ketare kogin da �afa su tunkari ganuwarbirnin. Amma ta yaya sojojin Cyrus za su sami wuce ganu-war Babila? Dominwasu dalilai awannan daren anyi sakacian bar �ofofin birnin a bu�e!

13. Wane bayani ne dalla-dalla Jehobah ya huri annabi Ishaya ya ru-buta game da Babila?14, 15. Ta yaya wasu bayanai game da annabcin Ishaya suka cikagame da Babila?

Littafi Mai Tsarki—Littafi ne Daga Allah 23

16 Game da Babila, an annabta: “Ba za ta zama da muta-ne a cikinta ba da�ai, ba kuwa za a zauna a cikinta ba dagatsara zuwa tsara: Ba-larabe ba za ya kafa tent nasa a wurinba; makiyaya kuma ba za su yi makwantar garkensu awurinba.” (Ishaya 13:20) Wannan annabci na halakar birnin ne,da kuma yadda zai kasance bayan haka. Ya nuna cewa Ba-bila za ta halaka har abada abadin. Za ka ga tabbacin cikarwannan annabcin. Inda Babila ta d

¯a take mil 50 ne yamma

da Bagadaza ta Ira�i kuma babu wanda yake zaune cikin-ta, hakan ya tabbatar da abin da Jehobah ya fa�a ta bakinIshaya ya faru: “[Zan] share ta kuma da tsintsiyar hallaka.”—Ishaya 14:22, 23.�

17 Ganin yadda Littafi Mai Tsarki littafi ne na annabci daza a dogara da shi abin �arfafa bangaskiya ne, ko ba haka

� Domin �arin bayani game da annabcin Littafi Mai Tsarki, ka dubishafuffuka na 27-29 na mujallar nan Littafi Don Dukan Mutane, Shai-dun Jehobah ne suka wallafa.

16. (a) Menene Ishaya ya fa�a game da �arshen Babila? (b) Ta yayaannabcin Ishaya game da halakar Babila ya cika?17. Ta yaya ne cika annabcin Littafi Mai Tsarki yake �arfafa bangas-kiya?

24 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa

ba? Hakika, Jehobah Allah ya cika alkawuransa na d¯a, muna

da kyawawan dalilai na gaskata cewa zai cika alkawuransana aljanna a duniya. (Littafin Lissafi 23:19) Babu shakka,muna da “bege na rai mara-matu�a, wanda Allah, da ba shiiya yin �arya, ya alkawarta tun gaban madawaman zama-nu.”—Titus 1:2.�

“MAGANAR ALLAH MAI-RAI CE”18 Daga abin da muka riga muka bincika a wannan babi,

ya bayyana sarai cewa Littafi Mai Tsarki ba na biyun-sa. Duk da haka, muhimmancinsa ya fice jituwarsa kawai,�warewarsa a kimiyya da kuma tarihi, da hikima da kuma

� Halakar Babila misali ne guda kawai na annabcin Littafi Mai Tsar-ki da ya cika. Wasu misalai sun ha�a da halakar Tyre da Nineveh. (Eze-kiel 26:1-5; Zephaniah 2:13-15) Har ila, annabcin Daniel ya nuna dau-loli da za su mallaki duniya da za su bayyana bayan Babila. Wa�annansun ha�a da Media da Persia da kuma Hellas. (Daniel 8:5-7, 20-22)Dubi Rataye, a shafuffuka na 199-201, domin �arin bayani game daannabce-annabce masu yawa game da Almasihu da suka cika ga YesuKristi.

18. Wane bahasi mai �arfi manzo Bulus Kirista ya yi game da “maga-nar Allah”?

Kango na Babila

Littafi Mai Tsarki—Littafi ne Daga Allah 25

annabcin abin dogara. Manzo Bulus Kirista ya rubuta: “Ma-ganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa, ta fi kowane takobimai-kaifi biyu ci, tana kuwa hudawa har zuwa rarraban raida ruhu, da ga�a�uwa da �argo kuma, tana kuwa dahamzari ga ganewar tunanin zuciya da nufe-nufenta.”—Ib-raniyawa 4:12.

19 Karatun “maganar” Allah, ko kuma sa�on Littafi MaiTsarki zai iya s

¯ake rayuwarmu. Zai taimake mu mu binci-

ki kanmu yadda ba mu ta�a yi ba. Za mu yi da’awar muna�aunar Allah, amma yadda muka amsa kiran hurarriyarKalmarsa, Littafi Mai Tsarki, za ta bayyana tunaninmu, dakuma manufar zuciyarmu.

20 Littafi Mai Tsarki hakika littafi ne daga Allah. Littafi neda za mu yi karatu, mu yi nazari, mu kuma �aunace shi. Kanuna godiyarka ga wannan kyauta daga Allah ta wajen cigaba da bincika abin da ya �unsa. Sa’ad da ka yi haka, zaka fahimci nufin Allah ga ’yan adam da kyau. Za a tattaunaabin da wannan manufa take nufi da kuma yadda za ta ka-sance a babi na gaba.

19, 20. (a) Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai taimake ka ka binciki kanka?(b) Ta yaya za ka nuna godiyarka ga wannan kyauta mai muhimman-ci daga Allah Littafi Mai Tsarki?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

ˇ Littafi Mai Tsarki hurarre ne daga Allah sa-boda haka cikakke ne kuma abin dogara ne.—2 Timothawus 3:16.

ˇ Bayani da ke cikin Kalmar Allah yana da am-fani a rayuwar yau da kullum.—Ishaya 48:17.

ˇ Alkawuran Allah da ke cikin Littafi Mai Tsar-ki a tabbace yake cewa zai cika su.—Littafin Lissafi 23:19.

26 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa

ABIN da Allah ya nufa ga duniya babu shakka abin sha’a-wa ne. Jehobah yana so duniya ta cika da mutane masu�oshin lafiya da farin ciki. Littafi Mai Tsarki ya ce Allah “yadasa gona . . . a cikin Adnin” kumaya sa “kowane itacen dake mai-sha’awan gani, masu-kyau kuwa domin ci.” Bayanda Allah ya halicci mata da miji na farko, Adamu da Ha-wa’u, ya sa su a gida mai ni’ima, ya kuma ce musu: “Kuyalwata da ’ya’ya, ku ri�u, ku mamaye duniya, ku mallaketa.” (Farawa 1:28; 2:8, 9, 15) Saboda haka nufin Allah nemutane su haifi ’ya’ya, su fa�a�a aljanna ta cika dukan du-niya, kuma su kula da dabbobi da ke cikinta.

2 Kana tsammanin nufin nan na Jehobah Allah, muta-ne su rayu cikin aljanna a duniya zai ta�a yiwuwa kuwa?“Na fa�i,” Allah ya ce, “zan kuwa aika.” (Ishaya 46:9-11;55:11) Babu shakka, Allah zai yi abin da ya nufa! Ya ceya halicci duniya “ba wofi ba, ya kamanta ta domin wu-rin zama.” (Ishaya 45:18) Wa�anne irin mutane Allah yakeso su zauna a cikin duniya? Kuma har tsawon wane loka-ci yake so su zauna a cikinta? Littafi Mai Tsarki ya ba da

1. Menene Allah ya nufa ga duniya?2. (a) Ta yaya muka san cewa abin da Allah ya nufa ga duniya zaicika? (b) Wane irin mutane ne Littafi Mai Tsarki ya ce za su rayu harabada?

BABI NA UKU

Menene Allah Ya Nufaga Duniya?

Menene Allah ya nufa ga ’yan adam?

Ta yaya aka �alubalanci Allah?

Yaya rayuwa a duniya za ta kasance a nan gaba?

amsa: ‘Masu-adalci za su g¯aji �asan, su zauna a cikinta har

abada.’—Zabura 37:29; Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.3 A bayyane yake cewa wannan bai faru ba tukuna. A

yau mutane suna tsufa kuma suna mutuwa; suna fa�asuna kashe juna. Akwai abin da ya faru. Hakika, Allah bainufi duniya ta kasance kamar yadda muke ganinta a yauba! Menene ya kawo haka? Me ya sa nufin Allah bai cikaba? Babu wani littafi na tarihi da zai iya ba mu amsa, do-min matsalar ta samo asali ne daga samaniya.

ASALIN MAGABCI4 Littafin farko na Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game

da abokin gaban Allah da ya bayyana a gonar Aidan. Ankwatanta shi da “maciji,” amma ba dabba ba ne. Littafin�arshe na Littafi Mai Tsarki ya kira shi “Iblis da Shai�an,mai-ru�in dukan duniya.” An kira shi ‘tsohon macijin.’(Farawa 3:1; Ru’ya ta Yohanna 12:9) Wannan mala’ikamai iko, ko kuma halittar ruhu, ya yi amfani da maciji yayi wa Hauwa’u magana, kamar yadda mutane masu iya-wa sai su yi magana, muryarsu ta kasance kamar ta fitone daga ’yar tsana. Babu shakka cewa wannan ruhun yanawajen sa’ad da Allah ya shirya duniya domin mutane.—Ayuba 38:4, 7.

5 Tun da dukan halittun Jehobah kamiltattu ne, to, waya halicci wannan “Iblis” “Shai�an”? A ta�aice, �aya dagacikin mala’iku ’ya’yan Allah ne ya mai da kansa Iblis. Wan-nan zai yiwu kuwa? Hakika, a yau mutumin da ya kasanceadali mai gaskiya zai iya juya ya zama �arawo. Ta yayawan-nan zai faru? Idan mutuminya �yale ba�in muradi ya cikazuciyarsa. Idanya ci gaba da sa�a shi a zuciya, wannan mu-

3. Wane irin yanayi ne na ta�aici ya samu a duniya, kuma wace tam-baya wannan ya jawo?4, 5. (a) Waye ainihi ya yi wa Hauwa’u magana ta bakin maciji? (b) Tayaya mutum adali mai gaskiya zai juya ya zama �arawo?

28 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

radin sai ya fi �arfinsa. Sa’ad da kuma ya sami zarafi, sai yabi zuciyarsa.—Ya�ub 1:13-15.

6 Abin da ya faru ke nan da Shai�an Iblis. Hakika ya jisa’ad da Allah ya fa�a wa Adamu da Hauwa’u su haifi ’ya-’ya su cika duniya. (Farawa 1:27, 28) Wata�ila Shai�an saiya yi tunani, ‘Ai, gara wa�annan mutane su bauta minimaimakon su bauta wa Allah!’ Ba�in muradi ya kahu a zu-ciyarsa. Sai, ya bi zuciya ya yaudari Hauwa’u, ya yi mata�arya game da Allah. (Farawa 3:1-5) Saboda haka ya zama“Iblis,” wanda yake nufin “Ma�aryaci.” Haka nan kuma yazama “Shai�an,” wanda yake nufin “Abokin gaba.”

7 Ta wajen �arya da yaudara, Shai�an Iblis ya sa Ada-mu da Hauwa’u suka yi wa Allah rashin biyayya. (Farawa2:17; 3:6) Saboda haka, mutuwa ta same su, kamar yad-da Allah ya ce za ta kasance a gare su idan suka yi rashinbiyayya. (Farawa 3:17-19) Tun da Adamu ya zama ajizidomin zunubi, dukan zuriyarsa suka g

¯aji zunubi daga wu-

rinsa. (Romawa 5:12) Za a iya kwatanta wannan yanayinda gwangwanin gasa burodi. Idan gwangwanin ya lan�wa-she, mai zai sami burodin da za a gasa a cikinsa? Kowaneburodi zai kasance da lan�wasa, ko kuma ajizanci. Ha-kazalika, dukan ’yan adam suka gaji “lan�wasa” ta ajizancidaga Adamu. Abin da ya sa ke nan dukan mutane suke tsu-fa kuma suke mutuwa.—Romawa 3:23.

8 Sa’ad da Shai�an ya ja-goranci Adamu da Hauwa’u suyi zunubi ga Allah, yana ja-gorarsu ne wajen tawaye. Yana�alubalantar yadda Jehobah yake sarauta. Wato Shai�ancewa yake: ‘Allah mugun sarki ne. Ma�aryaci ne azzalumikumayanahana talakawansa abubuwamasukyau.Mutane

6. Ta yaya ruhu �an Allah mai iko ya zama Shai�an Iblis?7. (a) Me ya sa Adamu da Hauwa’u suka mutu? (b) Me ya sa dukanzuriyar Adamu suke tsufa kuma suke mutuwa?8, 9. (a) Menene Shai�an yake nufi a �alubalantar da ya yi? (b) Meya sa Allah bai halaka ’yan tawayen ba a take?

Menene Allah ya Nufa ga Duniya? 29

ba sa bukatar Allah ya mallake su. Za su iya kafa wa kansuabin da ke daidai da abin da ba daidai ba. Kuma ya fi mususu kasance a �ar�ashin mallakata.’ Ta yaya Allah zai yi ma-ganin irinwannan tuhuma? Wasu sun ce da Allah ya kashe’yan tawayen kawai. Amma da wannan zai mai da martaniga �alubalanci na Shai�an kuwa? Da wannan ya tabbatarda cewa yadda Allah yake sarauta daidai ne?

Da Shai�an zai yi wa Yesualkawarin dukan mulkokin duniya

idan ba nasa ba ne?

30 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

9 Kamiltaccen hukuncin Jehobah ba zai �yale shi ya ka-she ’yan tawayen nan da nan ba. Ya yanke shawarar cewaana bukatar lokaci domin a mai da martani ga �alubalan-ci na Shai�an a hanya mai gamsarwa da za ta tabbatar dacewa Iblis ma�aryaci ne. Saboda haka Allah ya �yale mu-tane su mallaki kansu na �an lokaci a �ar�ashin rinjayarShai�an. Za a tattauna abin da ya sa Jehobah ya �yale lo-kaci mai tsawo ya shige kafin ya magance wannan batu aBabi na 11 na wannan littafi. Amma a yanzu, yana da kyaumu yi tunani game da wannan: Shin Adamu da Hauwa’usuna da wani dalilin da ya sa za su yarda da abin da Shai-�an ya ce ne, shi da bai ta�a yi musu wani abin kirki ba?Daidai ne su yarda cewa Jehobah, wanda ya ba su dukanabin da suka mallaka, mugun ma�aryaci ne? Da kai ne meza ka yi?

10 Yana da kyau mu yi tunani a kan wa�annan tambayo-yi domin kowannenmu yana fuskantar irin wannan batua yau. Hakika, kana da damar ka goyi bayan Jehobah do-min ka mai da martani ga �alubalanci na Shai�an. Kanaiya yarda Jehobah ya Mallake ka, kuma ka taimaka katabbatar da Shai�an ma�aryaci ne. (Zabura 73:28; Misalai27:11) Abin ba�in ciki, mutane kalilan ne kawai a tsakaninbiliyoyin mutane da suke wannan duniya suka za�i su yihaka. Wannan ya kawo wata muhimmiyar tambaya, ShinLittafi Mai Tsarki ya koyar ne da cewa Shai�an ne yakemallakar wannan duniyar?

WAYE YAKE MULKIN WANNAN DUNIYAR?11 Yesu bai ta�a yin shakkar cewa Shai�an ne yake mul-

kin wannan duniyar ba. A wata hanya mai ban al’ajabi,

10. Ta yaya za ka goyi bayan Jehobah domin ka mai da martani ga�alubalanci na Shai�an?11, 12. (a) Ta yaya jarabtar Yesu ta nuna cewa Shai�an shi ne mamal-lakin wannan duniya? (b) Menene kuma ya tabbatar da cewa Shai�anshi ne mamallakin wannan duniya?

Menene Allah ya Nufa ga Duniya? 31

Shai�an ya ta�a nuna wa Yesu “dukan mulkokin duniya,da �aukakarsu.” Sai Shai�an ya yi wa Yesu alkawari: “Dukwa�annan ni ba ka, idan ka f

¯a�i, ka yi mani sujada.” (Mat-

ta 4:8, 9; Luka 4:5, 6) Ka yi tunanin wannan. Da wannanalkawari zai kasance jarraba ga Yesu idan ba Shai�an bane yake mallakar dukan wa�annan mulkoki? Yesu bai yimusu ba cewa dukan wa�annan gwamnatoci na duniyana Shai�an ne. Babu shakka, da Yesu ya yi haka idan baShai�an ba ne yake da su.

12 Hakika, Jehobah shi ne Allah Ma�aukaki Sarki, Maha-liccin dukan abu. (Ru’ya ta Yohanna 4:11) Duk da haka,babu inda Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah Allah ko kumaYesu Kristi ke mallakar wannan duniyar. Saboda haka, adarensa na �arshe a duniya, Yesu ya nuna cewa Shai�anshi ne “mai-mulkin wannan duniya.” (Yohanna 12:31;14:30; 16:11) Littafi Mai Tsarki ya kuma nuna mana cewaShai�an Iblis shi ne “allah na wannan zamani.” (2 Korin-thiyawa 4:3, 4) Game da wannan abokin gaba, ko kumaShai�an, manzo Yohanna ya rubuta: “Duniya duka kuwatana kwance cikin Shai�an.”—1 Yohanna 5:19.

YADDA ZA A KAWAR DA DUNIYAR SHAI�AN13 Duk shekara, duniya tana �ara zama wuri mai ha�ari.

Ta cika da sojoji da suke ya�e-ya�e, ’yan siyasa marasa gas-kiya, miyagu masu taurin zuciya. Duniya gaba �ayanta tafi gaban a gyara. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa lokaci yayi kusa da Allah zai kawar da duniyar nan ta mugunta a ya-�insa na Armageddon. Wannan zai share fage ga sabuwarduniya ta adalci.—Ru’ya ta Yohanna 16:14-16.

14 Jehobah Allah ya za�i Yesu Kristi ya zama Sarki a Mul-kinsa na samaniya, ko gwamnati. Tun a d

¯a can, Littafi Mai

13. Me ya sa ake bukatar sabuwar duniya?14. Waye Allah ya za�a ya yi Sarauta a Mulkinsa, kuma ta yaya akaannabta wannan?

32 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

Tsarki ya annabta: “Gama an haifa mana yaro, a garemuan bada �a: mulkin za ya kasance a kafa�arsa: za a ce da su-nansa . . . Sarkin Salama. �aruwar mulkinsa da salama bata da iyaka.” (Ishaya 9:6, 7) Game dawannan mulkin, Yesuya koya wa mabiyansa addu’a: “Mulkinka shi zo. Abin daka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa ci-kin sama.” (Matta 6:10) Kamar yadda za mu gani a nangaba a wannan littafin, Mulkin Allah ba da da�ewa ba zaikawar da dukan gwamnatocin duniya, kuma shi kansa zai�auki matsayin dukansu. (Daniel 2:44) Sa’an nan MulkinAllah zai kawo aljanna a duniya.

SABUWAR DUNIYA TA YI KUSA!15 Littafi Mai Tsarki ya yi mana tabbaci: “Amma, bisa

ga alkawalinsa, muna sauraron sabobin sammai da sabu-war duniya, inda adalci ya ke zaune.” (2 Bitrus 3:13; Ishaya65:17) Sau da yawa idan Littafi Mai Tsarki ya yi maganar“duniya” yana nufin mutane da suke raye a duniya. (Fara-wa 11:1) “Sabuwar duniya” ta adalci tana nufin mutane dasuka sami yardar Allah.

16 Yesu ya yi alkawari cewa a sabuwar duniya mai zuwa,wa�anda Allah ya yarda da su za su sami kyautar “rai nahar abada.” (Markus 10:30) Don Allah ka bu�e LittafinkaMai Tsarki zuwa Yohanna 3:16 da kuma Yohanna 17:3, kakaranta abin da Yesu ya ce dole ne mu yi domin mu samirai madawwami. Yanzu, ka yi la’akari daga Littafi Mai Tsar-ki albarkatai dawa�anda suka cancanta za su samu, kyautamai ban sha’awa daga Allah a Aljanna ta duniya.

17 Mugunta, ya�e-ya�e, yin laifi, da kuma nuna �ar-fi duka za su zama abin da suka shige. “Mai-mugunta ba

15. Mecece ce “sabuwar duniya”?16. Wace kyauta ce mai tamani wa�anda Allah ya yarda da su za susamu, kuma menene za mu yi domin mu same ta?17, 18. Ta yaya muka sani cewa a ko’ina a cikin duniya za a sami sa-lama da kwanciyar hankali?

Menene Allah ya Nufa ga Duniya? 33

shi. . . Amma masu-tawali’u za su g¯aji �asan.” (Zabura 37:

10, 11) Za a sami zaman lumana domin Allah zai “sa ya-�o�i su �are har iyakar duniya.” (Zabura 46:9; Ishaya 2:4)Sa’an nan “mai-adilci za shi yalwata; da salama mai-yawa,har batun wata ya �are,” wato za a yi salama har abada!—Zabura 72:7.

18 Masu bauta wa Jehobah za su zauna cikin kwanciyarhankali. Duk sa’ad da Isra’ilawa na lokacin da aka rubutaLittafi Mai Tsarki suka yi wa Allah biyayya, suna zama ci-kin kwanciyar hankali. (Leviticus 25:18, 19) More irinwannan kwanciyar hankali a Aljanna zai kasance abin bansha’awa.—Ishaya 32:18; Mi�ah 4:4.

19 Ba za a yi �arancin abinci ba. Mai Zabura ya rairawa�a ya ce: “Za a yi albarkar hatsi a �asa a bisa �wan�o-lin duwatsu.” (Zabura 72:16) Jehobah Allah zai albarkacimutanensa masu adalci, kuma “�asa t

¯a bada anfaninta.”

—Zabura 67:6.20 Duniya duka za ta zama aljanna. Za a gina gidaje a

kuma dasa lambuna a wuri da mutane masu zunubi sukalalata. (Ishaya 65:21-24; Ru’ya ta Yohanna 11:18) Da shi-gewar lokaci, �angarorin duniya da aka riga aka mallakaza a fa�a�a shi har sai dukan duniya ta kyawanta ta zamamai amfani kamar gonar Aidan. Kuma Allah zai bu�e han-nayensa ya “biya ma kowane mai-rai muradinsa.”—Zabura145:16.

21 Za a sami salama tsakanin mutane da dabbobi. Dab-bobin daji za su yi kiwo tare da na gida. Har jariri ma ba zaiji tsoron dabbobi ba da yanzu suke da ha�ari.—Ishaya 11:6-9; 65:25.

19. Ta yaya muka sani cewa za a sami yalwar abinci a sabuwar duni-ya ta Allah?20. Me ya sa za mu tabbata cewa dukan duniya za ta zama aljanna?21. Menene ya nuna cewa za a sami salama tsakanin mutane da dab-bobi?

34 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

22 Cututtuka za su shu�e. Sarkin Mulkin sama na Allah,Yesu zai warkar da mutane fiye da yadda ya warkar da susa’ad da yake duniya. (Matta 9:35; Markus 1:40-42; Yohan-na 5:5-9) Sa’an nan “wanda ya ke zaune a ciki ba za ya ce,ina ciwo ba.”—Ishaya 33:24; 35:5, 6.

23 Za a dawo da matattu zuwa rai kuma za su kasanceda begen dawwama. Dukan wa�anda suka mutu da Al-lah yake tunawa da su zai tashe su zuwa rai. Hakika, “zaa yi tashin matattu, na masu-adalci da na marasa-adalci.”—Ayukan Manzanni 24:15; Yohanna 5:28, 29.

24 Wa�anda suka za�i su koyi game da Mahalic-cinmu, Jehobah Allah, kuma su bauta masa, rayuwamai ban sha’awa ta nan gaba na jiransu! Yesu yanamaganar wannan Aljanna ta duniya da take zuwa nesa’ad da ya yi alkawari ga mai laifi da ya mutu a gefen-sa: “Yau kana tare da ni a cikin [Aljanna].” (Luka 23:43)Yana da muhimmanci mu yi koyi game da Yesu Kristi,wanda dukan wa�annan albarkatai za su samu ta han-nunsa.

22. Menene zai faru da cututtuka?23. Me ya sa tashin matattu zai faranta mana rai?24. Yaya ka ji game da rayuwa a Aljanna ta duniya?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

ˇ Nufin Allah ya mai da duniya aljanna zaicika.—Ishaya 45:18; 55:11.

ˇ Shai�an ne yanzu yake mallakar wannan du-niyar.—Yohanna 12:31; 1 Yohanna 5:19.

ˇ A sabuwar duniya da take zuwa, Allah zai sakawa mutane albarka mai yawa.—Zabura 37:10,11, 29.

36 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

DA AKWAI mutane da yawa da suka shahara a duniya.Wasu sanannu ne a yankinsu, a birninsu, ko kuma a �a-sarsu. Wasu kuma sanannu ne a dukan duniya. Amma,sanin sunan shahararren mutum ba shi ne saninsa bada gaske. Ba ya nufin ka san tarihinsa da kuma kama-ninsa.

2 Mutane a duniya sun ji wani abu ne game da YesuKristi, ko da yake ya rayu a nan duniya kusan shekara2,000 da ta shige. Duk da haka, mutane da yawa sun ru�egame da ainihi wanene Yesu. Wasu sun ce shi dai mutu-min kirki ne. Wasu sun ce bai shige annabi ba. Har ilawasu sun ce Yesu Allah ne kuma ya kamata a bauta masa.Ya kamata ne?

3 Yana da muhimmanci ka san gaskiya game da Yesu.Me ya sa? Domin Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Rai na har aba-da ke nan, su san ka, Allah maka�aici mai-gaskiya, da shikuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.’ (Yohanna 17:3) Haki-ka, sanin gaskiya game da Jehobah Allah da kuma YesuKristi zai sa mu sami rai madawwami a aljanna a duni-ya. (Yohanna 14:6) Bugu da �ari, Yesu ya kafa misali mafi

1, 2. (a) Me ya sa sanin sunan mutumin da ya shahara ba ya nunasaninsa ne na gaskiya? (b) Wane ru�ani ne ya kasance game da Yesu?3. Me ya sa yake da muhimmanci a gare ka ka san gaskiya game daYesu?

BABI NA HU�U

Wanene Yesu Kristi?

Menene matsayin Yesu na musamman?

Daga ina ya fito?

Shi wane irin mutum ne?

kyau na yadda za mu rayu da kumayadda za mu bi da mutane. (Yohan-

na 13:34, 35) A babin farko na wannan littafin,mun tattauna gaskiya game da Allah. Yanzu bari mu

tattauna abin da Littafi Mai Tsarki ainihi ya koyar gameda Yesu Kristi.

ALMASIHU DA AKA YI ALKAWARINSA4 Da da�ewa kafin a haifi Yesu, Littafi Mai Tsarki ya yi

annabcin zuwan wanda Allah zai aiko ya zama Almasihu,ko kuma Kristi. Wa�annan sunayen sarauta “Al-masihu” (daga Ibrananci) da kuma “Kristi” (daga

4. Menene sunayen sarauta nan “Almasihu” da kuma “Kris-ti” suke nufi?

Yesu ya zama Almasihu ko kumaKristi a lokacin baftismarsa

Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

Helenanci) duka suna nufin “Shafaffe.” Wanda aka yi al-kawarinsa zai zama shafaffe, wato, wanda Allah ya na�a amatsayi na musamman. A babobi masu zuwa na wannanlittafin za mu koyi game da matsayi mai muhimmancina Almasihu wajen cika alkawuran Allah. Kuma za mukoyi game da albarkatai da Yesu zai kawo mana har ma ayanzu. Kafin a haifi Yesu, mutane da yawa suna mamaki,‘Waye ne zai zama Almasihu?’

5 A �arni na farko A.Z., almajiran Yesu Banazare suntabbata shi ne Almasihu da aka annabta. (Yohanna 1:41)�aya cikin almajiransa, mai suna Saminu Bitrus, ya fitofili ya ce game da Yesu: “Kai Kristi ne.” (Matta 16:16) To,yaya wa�annan almajirai, da mu kanmu, za mu tabba-ta cewa Yesu shi ne Almasihun da aka yi alkawarinsa dagaske?

6 Annabawan Allah da suka rayu kafin Yesu sun yiannabci dalla-dalla game da Almasihu. Wannan bayanidalla-dalla zai taimaki wasu su gane shi. Za mu iya kwa-tanta wannan haka: A ce an aike ka tashar mota ko tajirgin �asa ko ta jirgin sama ka �auko wani mutumin daba ka ta�a saduwa da shi ba. Idan aka yi maka �ankwatancensa hakan ba zai taimaka maka ba? Hakazalika,ta wajen annabawan Littafi Mai Tsarki, Jehobah ya ba dacikakken kwatancin abin da Almasihun zai yi da abin dazai fuskanta. Cikan wa�annan annabce-annabce zai tai-maki masu aminci su gane shi.

7 Ga misalai biyu rak. Na farko, fiye da shekaru 700, an-nabi Mika ya annabta cewa �an alkawarin za a haife shia Baitalami, wani �an �aramin gari a �asar Yahuda. (Mi-�ah 5:2) A ina aka haifi Yesu? Lalle, a wannan garin ne!

5. Menene almajiran Yesu suka tabbata game da shi?6. Ka kwatanta yadda Jehobah ya taimaki masu aminci su gane Al-masihu.7. Wa�anne annabce-annabce ne biyu da suka shafi Yesu suka cika?

Wanene Yesu Kristi? 39

(Matta 2:1, 3-9) Na biyu, �arnuka da yawa, annabci daaka rubuta a Daniel 9:25 ya nuna har shekarar da Almasi-hu zai bayyana, wato shekara ta 29 A.Z.� Cikan wannanda kuma wasu annabce-annabce ya tabbatar da cewa lal-le Yesu shi ne Almasihun da aka yi alkawarinsa.

8 �arin tabbaci cewa Yesu shi ne Almasihu ya bay-yana a �arshen shekara ta 29 A.Z. Wannan shekararce Yesu ya je wurin Yohanna mai Baftisma ya yi masabaftisma a Kogin Urdun. Jehobah ya yi wa Yohanna al-kawarin alama domin ya gane Almasihun. Yohannaya ga alamar a lokacin baftismar Yesu. Ga abin da Litta-fi Mai Tsarki ya ce ya faru: “Sa’anda aka yi masa [Yesu]baftisma, ya fita nan da nan daga cikin ruwa: ga kuwasammai suka bu�e masa, ya ga Ruhun Allah yana sau-kowa kamar kurciya yana zuwa bisansa; ga kuwa muryadaga cikin sammai, ta ce, Wannan �ana ne, �aunata-cena, wanda raina ya ji da�insa sarai.” (Matta 3:16, 17)Bayan ya ji kuma ya ga abin da ya faru, Yohanna ba shida sauran wata shakka cewa Allah ne ya aiko Yesu. (Yo-hanna 1:32-34) Sa’ad da aka zubo masa ruhun Allah, kokuma �arfin ikonsa a wannan rana, Yesu ya zama Alma-sihu, ko kuma Kristi, wanda aka na�a ya zama Shugabada kuma Sarki.—Ishaya 55:4.

9 Cikar annabcin Littafi Mai Tsarki da kuma shaidarda Jehobah Allah ya bayar ya nuna a fili cewa Yesune Almasihu da aka yi alkawarinsa. Amma kuma LittafiMai Tsarki ya amsa wasu tambayoyi biyu masu muhim-manci game da Yesu Kristi: Daga ina ya fito? Wane irinmutum ne shi?

� Domin bayani game da annabcin Daniel da ya cika a kan Yesu, kadubi Rataye, a shafi na 197-199.

8, 9. Wane tabbaci ne ya bayyana a lokacin baftismar Yesu da yanuna cewa shi ne Almasihu?

40 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

DAGA INA NE YESU YA FITO?10 Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa Yesu ya rayu a sa-

maniya kafin ya zo duniya. Mika ya annabta cewa za ahaifi Almasihu a Baitalami kuma ya da�a cewa asalinsa“tun daga zamanin d

¯a.” (Mi�ah 5:2) A lokatai da yawa,

Yesu kansa ya ce ya rayu a samaniya kafin a haife shimutum. (Yohanna 3:13; 6:38, 62; 17:4, 5) Sa’ad da yakehalittar ruhu a samaniya, Yesu yana da dangantaka tamusamman da Jehobah.

11 Yesu shi ne �an Jehobah da ya fi �auna, dominkyawawan dalilai. An kira shi “�an fari ne gaban dukanhalitta,” domin shi ne halitta ta farko na Allah.� (Kolos-siyawa 1:15) Da kuwa wani abin da ya sa ya zama �a namusamman. Shi ne “�ansa, haifaffe shi ka�ai.” (Yohanna3:16) Wannan yana nufin cewa Yesu ne kawai Allah ya ha-litta da hannunsa. Yesu ne ka�ai Allah ya yi amfani da shiwajen halittar dukan wasu abubuwa. (Kolossiyawa 1:16)Saboda haka, kuma ake kiran Yesu “Kalman.” (Yohanna1:14) Wannan ya nuna mana cewa ya yi magana game daAllah, babu shakka ya idar da sa�onni da umarnin ga sau-ran ’ya’yan Uban, ’ya’ya na ruhu da kuma na mutane.

12 Shin �an farin daidai yake da Allah, kamar yaddawasu suka gaskata? Littafi Mai Tsarki bai koyar da hakaba. Kamar yadda muka gani a sakin layi na baya, �an,halittarsa aka yi. Saboda haka, a bayyane yake cewa yana

� Ana kiran Jehobah Uba domin shi ne Mahalicci. (Ishaya 64:8) Tunda Allah ne ya halicci Yesu, ana kiransa �an Allah. Domin wannandalilin wasu halittu na ruhu da ma Adamu an kira su ’ya’yan Allah.—Ayuba 1:6; Luka 3:38.

10. Menene Littafi Mai Tsarki ya koyar game da rayuwar Yesu kafin yazo duniya?11. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Yesu shi ne �an Jehobahda ya fi �auna?12. Ta yaya muka sani cewa �an farin ba daidai yake da Allah ba?

Wanene Yesu Kristi? 41

da mafari, sa’an nan kuma Jehobah Allah ba shi da farkoba shi da �arshe. (Zabura 90:2) �an maka�aici bai ta�ama son ya gwada kansa da Ubansa ba. Littafi Mai Tsar-ki ya koyar da cewa Uban ya fi �an. (Yohanna 14:28;1 Korinthiyawa 11:3) Jehobah ne ka�ai “Allah Al�adiru.”(Farawa 17:1) Saboda haka, ba shi da wanda ya yi daidaida shi.�

13 Jehobah da �an farinsa sun yi zaman tare na she-karu biliyoyi, kafin ma a halicci sama mai taurari daduniya. Kuma suna �aunar juna gaya! (Yohanna 3:35;14:31) Wannan �an abin �auna kamar Ubansa yake.Abin da ya sa ke nan Littafi Mai Tsarki yake kiran �an“surar Allah marar-ganuwa.” (Kolossiyawa 1:15) Hakika,kamar ma yadda �a na mutum zai yi kama da ubansa ahanyoyi masu yawa, wannan �a na samaniya ya nunahalaye na Ubansa da kuma mutuntakarsa.

14 Wannan �an Jehobah maka�aici da son ransa yazo duniya domin ya yi rayuwa irin ta mutane. Ammaza ka yi mamaki, ‘Ta yaya zai yiwu a haifi halittar ruhua mutum?’ Domin ya cim ma wannan, Jehobah ya yimu’ujiza. Ya �aurar da ran �an farinsa zuwa mahaifarBayahudiya budurwa Maryamu. Babu uba �an adam daya shiga tsakani. Saboda haka, Maryamu ta haifi kamil-taccen �a kuma ta kira shi Yesu.—Luka 1:30-35.

WANE IRIN MUTUM NE SHI YESU?15 Abin da Yesu ya ce kuma ya yi sa’ad da yake duniya

� Domin �arin tabbaci game da cewa �an farin ba daidai yake daAllah ba, ka dubi Rataye, shafuffuka na 201-204.

13. Menene Littafi Mai Tsarki yake nufi sa’ad da ya ce �an “surar Al-lah marar-ganuwa” ne?14. Ta yaya aka haifi �an maka�aici na Jehobah �an adam?15. Me ya za mu ce ta warin Yesu muka zo ga fahimtar Jehobah dakyau?

42 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

ya taimake mu mu fahimce shi �warai. Fiye da haka, taYesu mun zo ga fahimtar Jehobah da kyau. Me ya sa yakasance haka? Ka tuna cewa wannan �an cikakken su-rar Ubansa ne. Abin da ya sa ke nan Yesu ya fa�a wa �ayacikin almajiransa: “Wanda ya gan ni ya ga Uban.” (Yo-hanna 14:9) Littattafai hu�u na Littafi Mai Tsarki da akasani da Linjila, wato, Matta, Markus, Luka, da Yohanna,sun yi mana bayani �warai game da rayuwa, ayyuka, dakuma mutuntakar Yesu Kristi.

16 An fi sanin Yesu da “Malami.” (Yohanna 1:38; 13:13)Menene ya koyar? Ainihi, sa�onsa shi ne “bishara ta mul-kin” wato, Mulkin Allah, gwamnati ta samaniya da za tayi sarauta bisa dukan duniya kuma za ta kawo albarkamarar iyaka ga mutane masu biyayya. (Matta 4:23) Sa�onwaye ne wannan? Yesu da kansa ya ce: “Abin da ni ke ko-yarwa ba nawa ba ne, amma nasa ne wanda ya aiko ni,”wato Jehobah ke nan. (Yohanna 7:16) Yesu ya sani cewaUbansa yana so mutane su ji bisharar Mulkin. A Babina 8, za mu koyi game da Mulkin Allah da kuma abin dazai yi.

17 A ina Yesu ya koyar? A dukan wuraren da ya tarar damutane, a bayan gari, a cikin birni, a �auyuka, a kasu-wanni, da kuma gidajen mutane. Yesu bai jira mutane suzo gare shi ba. Shi ya je wurinsu. (Markus 6:56; Luka 19:5, 6) Me ya sa Yesu ya yi haka ya kuma ba da lokaci maiyawa wajen wa’azi da koyarwa? Domin yin haka shi nenufin Allah a gare shi. Yesu ko da yaushe yana yin nufinUbansa ne. (Yohanna 8:28, 29) Da kuma wani dalili da yasa ya yi wa’azi. Ya yi juyayin taron jama’a da ta zo wurinshi. (Matta 9:35, 36) Shugabannin addinai sun yi watsi dasu, wa�anda ya kamata su ri�a koyar da su gaskiya game

16. Menene ainihin sa�on Yesu, kuma daga ina ne koyarwarsa ta fito?17. A ina Yesu ya yi koyarwarsa, kuma me ya sa ya yi irin wannan �o-�ari domin ya koyar da wasu?

Wanene Yesu Kristi? 43

da Allah da kuma nufinsa. Yesu ya fahimci yadda sukebukatar su ji sa�on Mulki.

18 Yesu mutum ne mai �auna mai juyayi. Saboda hakamutane suka fahimci cewa suna iya zuwa wurinsa dominmai alheri ne. Har yara ma sukan sake sa’ad da suke tareda shi. (Markus 10:13-16) Yesu ba shi da son kai. Yesu ya�i lalaci da rashin adalci. (Matta 21:12, 13) A lokacin damata ba su da daraja da gata, ya bi da su da daraja. (Yo-hanna 4:9, 27) Yesu mai �as�antar da kai ne �warai. Yata�a ma wanke �afafun manzanninsa, abin da bara ne yasaba yi.

19 Yesu yana kula da bukatun mutane. Wannan ya bay-yana musamman sa’ad da ya yi amfani da ikon ruhu maitsarki na Allah ya warkar da wasu cikin mu’ujiza. (Mat-ta 14:14) Alal misali, wani kuturu ya zo wurin Yesu ya ce:

18. Wa�anne halaye ne na Yesu suka fi ba ka sha’awa?19. Wa�anne misalai ne suka nuna cewa Yesu ya damu da bukatunwasu?

Yesu ya yi wa’azi a dukan inda ya tarar da mutane

“Idan ka yarda, kana da iko ka tsarkake ni.” Yesu ya jiwahalar wannan mutumin. Tausayi ya kama shi, sai Yesuya mi�a hannunsa ya ta�a mutumin, ya ce: “Na yar-da; ka tsarkaka.” Sai kuturun ya warke. (Markus 1:40-42)Kana iya tunanin yadda wannan mutumin ya ji?

MAI AMINCI HAR �ARSHE20 Yesu ya ba da misali mafi kyau na yin biyayya cikin

aminci ga Allah. Ya kasance da aminci ga Ubansa na sa-maniya cikin dukan yanayi da hamayya da wahala. Yesuya yi nasara wajen tsayayya da jarabtar Shai�an. (Matta4:1-11) A wani lokaci ’yan’uwan Yesu kansu ba su ba dagaskiya a gare shi ba, har suka ce “ya ru�e.” (Markus 3:21)Amma Yesu bai �yale sun rinjaye shi ba; ya ci gaba da yinaikin Allah. Yesu ya kasance da kame kai, bai yi �o�arinya cuci masu hamayya da shi ba, duk da zagi da rashinmutunci da suka nuna masa.—1 Bitrus 2:21-23.

20, 21. Ta yaya Yesu ya kafa misalin biyayya ga Allah?

45

21 Yesu ya kasance da aminci har mutuwarsa, mutuwarwulakanci a hannun abokan gaba. (Filibbiyawa 2:8) Ka yila’akari da abin da ya jimre a ranarsa ta �arshe ta rayu-war �an adam. Aka kama shi, masu shaidan zur suka bada shaida aka tuhume shi, malalatan al�alai suka yankemasa hukunci, mutane suka yi masa dariya, kuma so-joji suka gana masa azaba. Aka buga shi da �usa a jikingungumen azaba, a fitar ransa ya yi kuka: “Ya �are.” (Yo-hanna 19:30) Duk da haka, kwanaki uku bayan mutuwarYesu, Ubansa na samaniya ya ta da shi zuwa rayuwa taruhu. (1 Bitrus 3:18) Bayan ’yan makonni, ya koma sa-maniya. A can ya “zauna ga hannun dama na Allah” yanajira ya kar�i mulki.—Ibraniyawa 10:12, 13.

22 Menene Yesu ya cim ma ta wajen kasancewa daaminci har mutuwarsa? Hakika mutuwar Yesu ta bu�emana hanyar samun rai na har abada a aljanna a du-niya, cikin jituwa da nufin Jehobah na tun d

¯a. Za a

tattauna yadda mutuwar Yesu ta sa haka ya yiwu a babina gaba.

22. Menene Yesu ya cim ma ta wajen kasance da aminci har mutu-warsa?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

ˇ Cikan annabce-annabce da kuma shaida taAllah suka tabbatar da cewa Yesu shi ne Alma-sihu, ko kuma Kristi.—Matta 16:16.

ˇ Yesu ya yi rayuwar halitta ta ruhu a sama dada�ewa kafin ya zo duniya.—Yohanna 3:13.

ˇ Yesu malami ne, mutum ne mai �auna dajuyayi, kuma misali ne mafi kyau na biyayyaga Allah.—Matta 9:35, 36.

46 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

WANE abu ne mafi girma aka ta�a ba ka kyauta? Badole ba ne abin da aka bayar ya kasance mai tsada ka-fin ya zama mai muhimmanci. Hakika, muhimmancinabin da aka ba da kyauta ba dole ba ne a kwatanta shi dafarashinsa. Maimakon haka, idan abin da aka ba ka kyau-ta ya sa ka farin ciki ko kuma ya biya wani muhimminbukata a rayuwarka, yana da muhimmanci matu�a a ga-reka.

2 A dukan kyauta da za ka yi begen a yi maka, da akwai�aya da ta fi fice. Kyauta ce da Allah ya yi wa ’yan adam.Jehobah ya ba mu abubuwa masu yawan gaske, ammakyauta mafi girma da ya yi mana ita ce hadayar fansata �ansa, Yesu Kristi. (Matta 20:28) Kamar yadda za mugani a wannan babin, fansar ita ce kyauta mafi tamani daza a ta�a yi maka, domin za ta ba ka farin ciki gaya kumata biya maka bukatarka mafi muhimmanci. Hakika, fan-sar ita ce nuna matu�ar �auna na Jehobah a gareka.

1, 2. (a) Yaushe ne kyauta take da muhimmanci �warai a gareka?(b) Me ya sa za a ce fansa ita ce kyauta mafi muhimmanci da za a ta�ayi maka?

BABI NA BIYAR

Fansa—KyautaMafi Girma Daga Allah

Mecece fansa?

Ta yaya aka ba da ita?

Menene amfaninta a gareka?

Ta yaya za ka nuna godiyarkadominta?

MECECE CE FANSA?3 A ta�aice, fansa hanyar da Jehobah zai ceci ’yan adam

daga zunubi da kuma mutuwa ce. (Afisawa 1:7) Dominka fahimci ma’anar wannan abin da Littafi Mai Tsarkiyake koyarwa, muna bukatar mu tuna abin da ya faru agonar Adnin. Sai mun fahimci abin da Adamu ya yi hasa-ra sa’ad da ya yi zunubi, kafin mu fahimci abin da ya safansar kyauta ce mai muhimmanci.

4 Sa’ad da ya halicci Adamu, Jehobah ya ba shi abinda yake da muhimmanci—kamiltaccen rai. Ka yi la’akarida amfani da Adamu ya samu daga wannan. An halicceshi da kamiltaccen jiki da tunani, ba zai yi ciwo ba, ko yatsufa, balle ya mutu. Sa’ad da yake kamiltaccen mutum,yana da dangantaka ta musamman da Jehobah. LittafiMai Tsarki ya ce Adamu “na Allah.” (Luka 3:38) Sabo-da haka, Adamu ya more dangantaka ta kusa da JehobahAllah, irin dangantakar da ke tsakanin �a da ubansa. Je-hobah ya yi magana da �ansa a duniya, ya ba shi aiki maikayatarwa kuma ya sanar da shi abin da ake bukata a gareshi.—Farawa 1:28-30; 2:16, 17.

5 An halicci Adamu cikin “surar Allah.” (Farawa 1:27)Wannan ba ya nufin cewa Adamu ya yi kama da Allah azahiri. Kamar yadda muka gani a Babi na 1 na wannanlittafin, Jehobah ruhu ne da ba ya ganuwa. (Yohanna4:24) Saboda haka Jehobah ba shi da jiki na tsoka dajini. Halittar Adamu cikin surar Allah tana nufin cewa anhalicce shi da halaye wa�anda Allah yake da irin su, �au-na, hikima, shari’a, da iko. Adamu yana da surar Ubansaa wata hanya kuma mai muhimmanci, domin yana da

3. Mecece ce fansa, kuma me muke bukata domin mu fahimci mu-himmancinta?4. Menene kamiltaccen rai yake nufi ga Adamu?5. Menene Littafi Mai Tsarki yake nufi sa’ad da ya ce an halicci Ada-mu cikin “surar Allah”?

48 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

’yanci ya za�i abin da yake so. Saboda haka, Adamu bakamar inji ba ne da yake yin abin da aka �era shi ya yikawai. Maimakon haka, zai iya yanke shawarar kansa, yaza�i tsakanin abin da ke mai kyau da abin da ke mugu.Da ya za�i ya yi wa Allah biyayya, da ya rayu har abada acikin Aljanna a duniya.

6 A bayyane yake cewa sa’ad da Adamu ya yi wa Al-lah rashin biyayya kuma aka yi masa hukuncin kisa,ya yi hasara mai girma. Zunubinsa ya sa ya yi hasararkamiltaccen rai da dukan albarkatai da ke tattare da shi.(Farawa 3:17-19) Abin ba�in ciki, Adamu ya yi rashin raimai tamani ga kansa da kuma ’ya’ya da zai haifa a nangaba. Kalmar Allah ta ce: “Zunubi ya shigo cikin duniyata wurin mutum �aya, mutuwa kuwa ta wurin zunubi;har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane, da shi ke dukasun yi zunubi.” (Romawa 5:12) Hakika, dukanmu mungaji zunubi daga Adamu. Saboda haka, Littafi Mai Tsarkiya ce ya ‘sayar’ da kansa da kuma ’ya’yansa ga zunubi damutuwa. (Romawa 7:14) Babu wani sauran sa rai ga Ada-mu da Hauwa’u domin da son ransu suka za�i su yi waAllah rashin biyayya. Amma mu kuma fa, da kuma sau-ran ’ya’yansu?

7 Jehobah ya ceci ’yan Adam ta wurin fansa. Mecece cefansa? Fansa ta �unshi abubuwa biyu ne. Na farko, ana bi-yan fansa domin a �yale abin da aka kama ko kuma a sakesayan wani abu. Ana iya kwatanta wannan da ku�i da akebiya domin a saki fursunonin ya�i. Na biyu, fansa diyyace da ake biya domin wani abu. Ta yi daidai da diyyar daake biya domin na�asa da aka yi wa wani. Alal misali, idanmutum ya haddasa ha�ari, dole ne ya biya diyyar da za tayi daidai da muhimmancin abin da aka lalata.

6. Sa’ad da Adamu ya yi rashin biyayya ga Allah, me ya yi hasara,kuma ta yaya wannan ya shafi ’ya’yansa?7, 8. Wa�anne abubuwa biyu ne fansa ta �unsa?

Fansa—Kyauta Mafi Girma Daga Allah 49

8 Zai yiwu kuwa a biya diyya ta babbar hasara da Ada-mu ya jawo mana kuma a kwato mu daga bautar zunubida mutuwa? Bari mu bincika fansa da Jehobah ya yi tana-dinta da kuma abin da wannan take nufi a gare mu.

YADDA JEHOBAH YA YI TANADIN FANSA9 Tun da kamiltaccen rai ne aka yi hasara, babu mutum

ajizi da zai iya biyan diyyar. (Zabura 49:7, 8) Abin da akebukata fansa ce da ta yi daidai da farashin abin da aka yihasara. Wannan ya jitu da mizanin kamiltacciyar shari’ada take Kalmar Allah, wadda ta ce: “Rai maimakon rai.”(Kubawar Shari’a 19:21) Saboda haka, menene zai biyadiyyar kamiltaccen rai da Adamu ya yi hasara? Ran wanikamiltacce mutum ne ake bukata don fansa da ta yi dai-dai.—1 Timothawus 2:6.

10 Ta yaya Jehobah ya ba da fansar? Ya aiko da �ayadaga cikin ’ya’yansa kamiltattu na ruhu zuwa duni-ya. Amma Jehobah bai aiko da kowace halittar ruhu ba.Ya aiko wadda ta fi tamani a gare shi, �ansa maka�ai-ci. (1 Yohanna 4:9, 10) Da son ransa, wannan �an yabar wurin zamansa a samaniya. (Filibbiyawa 2:7) Kamaryadda muka koya a babi da ya gabata na wannan littafi,Jehobah ya yi mu’ujiza wajen �aurar da ran wannan �anzuwa cikin Maryamu. Ta wajen ruhun Allah, aka haifiYesu kamiltaccen mutum kuma ba shi da hukuncin kisaa bisa kansa.—Luka 1:35.

11 Ta yaya mutum �aya zai kasance fansa ga mutaneda yawa, miliyoyin mutane kuwa? To, ta yaya ma muta-ne miliyoyin suka kasance masu zunubi da fari? Ka tunacewa domin zunubi, Adamu ya yi hasarar abu mai mu-himmanci da yake da shi, kamiltaccen rai. Saboda haka,

9. Wace irin fansa ce ake bukata?10. Ta yaya Jehobah ya yi tanadin fansa?11. Ta yaya mutum �aya zai fanshi miliyoyin mutane?

50 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

ba zai iya ba da shi ga ’ya’yansa ba. Maimakon haka,abin da ya ba su shi ne zunubi da mutuwa. Yesu, daLittafi Mai Tsarki ya kira “Adamu na �arshe,” ya ka-sance da kamiltaccen rai na mutum, kuma bai ta�ayin zunubi ba. (1 Korinthiyawa 15:45) Wato abin nufi,Yesu ya �auki matsayin Adamu ne domin ya cece mu.Ta wajen hadaya, wato ba da ransa, ransa kamiltacce wa-jen biyayya marar aibi ga Allah, Yesu ya biya diyyarzunubin da Adamu ya yi. Da haka, Yesu ya ba dabege ga ’ya’yan Adamu.—Romawa 5:19; 1 Korinthiyawa15:21, 22.

12 Littafi Mai Tsarki ya ba da cikakken kwatanci nawahalar da Yesu ya jimre kafin mutuwarsa. Ya sha mu-guwar bulala, ba�ar rataya, da kuma mutuwar akubaa kan gungumen azaba. (Yohanna 19:1, 16-18, 30; DubiRataye, shafi na 204-206) Me ya sa dole ne Yesu ya wa-hala haka? A wani babi a gaba a wannan littafin, zamu ga cewa Shai�an ya yi zargin cewa Jehobah ba shi dabawa da zai kasance da aminci sa’ad da yake fuskantargwaji. Ta wajen kasancewa da aminci cikin matsananci-yar wahala, Yesu ya ba da amsa ga �alubale na Shai�an.Yesu ya tabbatar da cewa kamiltaccen mutum da yake dadama ya za�i abin da yake so zai iya kasancewa da amin-ci ga Allah ko da menene Iblis ya yi. Hakika Jehobah ya yifarin ciki gaya domin amincin �ansa abin �auna!—Mi-salai 27:11.

13 Ta yaya aka ba da fansa? A ranar 14 ga watan Ni-san na Yahudawa, 33 A.Z., Allah ya �yale aka kashe�ansa kamili kuma marar zunubi. Ta haka Yesu ya bada hadayar ransa kamiltacce “sau �aya �ungum.” (Ibra-niyawa 10:10) A rana ta uku bayan mutuwarsa, Jehobahya tashe shi zuwa rayuwa ta ruhu. A samaniya, Yesu ya

12. Menene mutuwar Yesu ta tabbatar?13. Ta yaya aka biya fansar?

Fansa—Kyauta Mafi Girma Daga Allah 51

Jehobah ya bada �ansa maka�aici

domin fansa agaremu

mi�a wa Allah tamanin kamiltaccen ransa na mutum do-min fansar ’ya’yan Adamu. (Ibraniyawa 9:24) Jehobah yakar�i tamanin hadayar Yesu domin fansa da ake bukata aceci ’yan Adam daga bautar zunubi da mutuwa.—Roma-wa 3:23, 24.

AMFANIN FANSA A GARE KA14 Duk da yanayinmu na zunubi, za mu iya more albar-

katai masu yawa domin fansar. Bari mu bincika amfanina yanzu da kuma na gaba na wannan kyauta mafi girmadaga Allah.

15 Gafarta zunubai. Domin mun gaji ajizanci, munafama domin mu yi abin da ke nagari. Dukanmu munayin zunubi ko a furcinmu ko ta ayyukanmu. Amma tawajen hadayar fansa na Yesu, za mu sami “gafarar zunu-banmu.” (Kolossiyawa 1:13, 14) Amma domin mu samiwannan gafara muna bukatar mu tuba da gaske. Dole nekuma mu ro�i Jehobah cikin tawali’u, mu ro�e shi yagafarta mana domin bangaskiyarmu a hadayar fansa na�ansa.—1 Yohanna 1:8, 9.

16 Lamiri mai tsabta a gaban Allah. Lamiri da yakes¯uka zai iya kai wa ga rashin bege kuma ya sa mu ji ba

mu da amfani. Saboda gafarar da ta samu ta wajen fansa,Jehobah ya �yale mu mu bauta masa da lamiri mai tsab-ta duk da ajizancinmu. (Ibraniyawa 9:13, 14) Wannan yasa mun sami ’yancin magana da Jehobah. Saboda haka,za mu iya yin addu’a a gare shi a sake. (Ibraniyawa 4:14-16) Kasancewa da lamiri mai tsabta yana ba da kwanciyarhankali, yana sa mu daraja kanmu, kuma yana ba da fa-rin ciki.

14, 15. Domin mu sami “gafarar zunubanmu,” menene ne dolemu yi?16. Mecece ta sa muke bauta wa Allah da lamiri mai tsabta, kuma me-nene muhimmancin wannan lamiri?

Fansa—Kyauta Mafi Girma Daga Allah 53

17 Begen rai madawwami a aljanna a duniya. “Hakkinzunubi mutuwa ne,” in ji Romawa 6:23. Wannan ayarkuma ta da�a cewa: “Amma kyautar Allah rai na har aba-da ce cikin Kristi Yesu Ubangijinmu.” A Babi na 3 nawannan littafin, mun tattauna albarkatai na Aljanna taduniya. (Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4) Dukan wa�annan al-barkatai da za su zo a nan gaba, har da rai madawwami acikin �oshin lafiya, sun kasance masu yiwuwa ne dominYesu ya mutu dominmu. Domin mu sami wa�annanalbarkatai muna bukatar mu nuna cewa muna masu go-diya domin wannan kyautar ta fansa.

TA YAYA ZA KA NUNA GODIYARKA?18 Me ya sa za mu yi godiya �warai ga Jehobah domin

fansar? To, kyauta dai musamman tana da martaba idanta �unshi sadaukar da lokaci, �o�ari, da kuma wani abudaga wurin mai bayarwa. Tana motsa mu sa’ad da mukaga cewa kyautar nuna �auna ce da gaske daga mai ba-yarwa. Fansar ita ce kyauta mafi martaba domin Allah

17. Wa�anne albarkatai ne suka kasance masu samuwa domin Yesuya mutu dominmu?18. Me ya sa za mu yi wa Jehobah godiya domin tanadin da ya yimana na fansa?

Neman �arin saninJehobah wata

hanya ce ta nunacewa kana mai

godiya ga kyautarfansa da ya yi

maka

ya yi sadaukarwa mafi girma ta wajen yi mana ta-nadinta. ‘Saboda �aunar da Allah ya yi wa duniya ya bada maka�aicin �ansa,’ in ji Yohanna 3:16. Fansa ita cemuhimmiyar tabbaci na �aunar da Jehobah yake mana.Kuma tabbaci ne na �aunar da Yesu yake mana, dominya ba da ransa a gare mu da son ransa. (Yohanna 15:13)Kyautar nan ta fansa ya kamata ta tabbatar mana cewa Je-hobah da �ansa suna �aunarmu.—Galatiyawa 2:20.

19 To, ta yaya za ka nuna cewa kana godiya dominkyautar fansa ta Allah? Da farko, ya kamata ka san MaiBayarwa Mai Girma, Jehobah. (Yohanna 17:3) Yin na-zarin Littafi Mai Tsarki da taimakon wannan littafin zaitaimaka maka ka yi haka. Sa’ad da ka �ara sanin Jehobah,�aunarka gare shi za ta zurfafa. Sai kuma �aunar za ta saka so faranta masa rai.—1 Yohanna 5:3.

20 Ka ba da gaskiya ga hadayar fansa na Yesu. An furtawa�annan kalaman game da Yesu: “Wanda yana bada gas-kiya ga �an yana da rai na har abada.” (Yohanna 3:36) Tayaya za mu ba da gaskiya ga Yesu? Irinwannan bangaskiyaba a nuna ta da baki kawai. “Bangaskiya ba tare da ayyukamataciya ce,” in ji Ya�ub 2:26. Hakika, bangaskiya ta gas-kiya ana tabbatar da ita ta wajen “ayyuka” wato, abin damuke yi. Wata hanya �aya ta nuna bangaskiya ga Yesu itace ta wajen yin koyi da shi ba kawai ta wajen magana baamma kuma ta wajen abin da muke yi.—Yohanna 13:15.

21 Ka halarci bikin Jibin Ubangiji kowace shekara. Ayammancin ranar 14 ga watan Nisan, 33 A.Z., Yesu yagabatar da bikin tuni na musamman da Littafi Mai Tsar-ki ya kira “jibin Ubangiji.” (1 Korinthiyawa 11:20; Matta26:26-28) Wannan bikin ana kuma kiransa Bikin Tuna

19, 20. A wa�anne hanyoyi ne za ka nuna cewa kana mai godiya gakyautar fansa ta Allah?21, 22. (a) Me ya sa za mu halarci bikin Jibin Ubangiji kowace she-kara? (b) Menene za a yi bayani a kai a babi na 6 da 7?

Fansa—Kyauta Mafi Girma Daga Allah 55

Mutuwar Kristi. Yesu ya kafa wannan domin ya taima-ki manzanninsa da kuma dukan Kiristoci na gaskiya daza su kasance bayansu su tuna cewa ta wajen mutuwarsana kamilin mutum, ya ba da ransa domin fansa. Gameda wannan bikin Yesu ya ba da umurni: “Ku yi wannanabin tunawa da ni.” (Luka 22:19) Yin Bikin yana tunamana �auna mai girma da Jehobah da Yesu suka nunamana wajen fansa. Za mu iya nuna godiyarmu dominfansa ta wajen kasancewa a wajen Bikin Tuna MutuwarYesu.�

22 Tanadin da Jehobah ya yi na fansa hakika kyautace mai muhimmanci. (2 Korinthiyawa 9:14, 15) Wannankyautar mai muhimmanci za ta amfani har wa�andasuka mutu. Babi na 6 da 7 za su yi bayani game da yaddahakan zai faru.

� Domin �arin bayani game da ma’anar Jibin Ubangiji, dubi Rata-ye, shafi na 206-208.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

ˇ Fansa hanya ce ta Jehobah na ceton ’yanAdam daga zunubi da mutuwa.—Afisawa 1:7.

ˇ Jehobah ya yi tanadin fansa ta wajen aikowada �ansa maka�aici zuwa duniya ya mutudominmu.—1 Yohanna 4:9, 10.

ˇ Ta wajen fansa muka sami gafara ga zunu-banmu, lamiri mai tsabta, da kuma begen raimadawwami.—1 Yohanna 1:8, 9.

ˇ Muna nuna muna masu godiya domin fansata wajen samun �arin sanin Jehobah, ta wajenba da gaskiya ga hadayar fansa ta Yesu, dakuma ta wajen halartar Bikin Jibin Ubangiji.—Yohanna 3:16.

56 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

WA�ANNAN tambayoyi ne da mutane suka yi tunanin-su na shekaru dubbai. Tambayoyi ne masu muhimmanci�warai. Ko su wanene mu, kuma ko ina muke zaune, amso-shin sun shafi kowannenmu.

2 A babi na baya, mun tattauna yadda hadayar fansa taYesu Kristi ta bu�e hanyar rai madawwami. Mun kuma koyicewa Littafi Mai Tsarki ya yi maganar lokaci da “mutuwakuwa ba za ta �ara kasancewa ba.” (Ru’ya ta Yohanna 21:4)Amma a yanzu, dukanmu muna mutuwa. “Masu-rai sun sanza su mutu,” in ji Sarki Sulemanu mai hikima. (Mai-Wa’azi9:5) Muna so mu sami tsawon rai. Duk da haka, muna tuna-nin menene zai faru da mu sa’ad da muka mutu.

3 Sa’ad da wa�anda muke �auna suka mutu, sai mu yimakoki. Wata�ila kuma mu yi tambaya: ‘Menene yake fa-ruwa da su? Suna wahala ne? Suna k

¯are mu ne? Za mu

iya taimakonsu kuwa? Za mu sake ganinsu kuwa?’ Addinaina duniya sun ba da amsoshi dabam dabam ga wa�annantambayoyi. Wasu sun koyar da cewa idan ka yi rayuwa takirki, za ka tafi sama amma idan ka yi mummunar rayuwa,za a �ona ka a wutar jahannama. Wasu kuma sun koyar dacewa sa’ad da mutum ya mutu, sai ya je duniyar matattu

1-3. Wa�anne tambayoyi ne mutane suke yi game da matattu, kumawa�anne amsoshi ne addinai dabam dabam suka bayar?

BABI NA SHIDA

Ina Matattu Suke?

Me yake faruwa da mu sa’ad da muka mutu?

Me ya sa muke mutuwa?

Me ya sa sanin gaskiya game da mutuwayake ba da kwanciyar hankali?

ya sadu da kakanni. Har ila wasu addinai kuma sun koyarda cewa matattu suna zuwa wata duniya inda za a yi musushari’a sai kuma a sake haifansu da wani jiki dabam.

4 Dukan wa�annan koyarwa na addinai ra’ayin iri �ayane—cewa wani �angaren jikinmu yana tsira bayan mutu-war jiki na zahiri. Kusan dukan wani addini na d

¯a ko na

zamani, ya nuna cewa muna rayuwa har abada ba tare dagani, ko ji ko kuma tunani ba. Amma, ta yaya hakan zaikasance? Hankalinmu, tare da tunaninmu, suna da nasabada �wa�walwarmu. Sa’ad da muka mutu, �wa�walwarmutana daina aiki. Tunaninmu, da kuma hankalinmu ba sa cigaba da aiki ba tare da wani ala�a ba ta wata hanya da ke dawuyar ganewa. Ba sa tsira wa halakar �wa�walwarmu.

MENENE AINIHI YAKE FARUWA A MUTUWA?5 Abin da yake faruwa a mutuwa ba mai wuya ba ne ga

Jehobah, Mahaliccin �wa�walwa. Ya san gaskiya, kuma acikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki, ya yi bayani game dayanayin matattu. Koyarwarsa mai sau�in fahimta, ita ce:Sa’ad da mutum ya mutu, ya daina wanzuwa. Mutuwa ki-shiyar rai ce. Matattu ba sa gani, ba sa ji, ba sa tunani. Babuwani abin da yake tsira daga mutuwar jiki. Ba mu da kurwamarar mutuwa.�

6 Bayan Sulemanu ya lura cewa rayayyu sun san cewa zasu mutu, sai ya rubuta: ‘Matattu ba su san komi ba.’ Sai ya�ara bayani game da wannan gaskiya yana cewa matattu baza su iya �auna ko �iyayya ba kuma “babu wani aiki, kodabara, ko ilimi, ko hikima, cikin kabari inda za ka.” (Mai-Wa’azi 9:5, 6, 10) Hakazalika, Zabura 146:4 ta ce sa’ad damutum ya mutu, “shawarwarinsa su kan lalace.” Mu muta-

� Domin tattaunawa game da kalmar nan “kurwa” ko kuma “ruhu,”don Allah ka dubi Rataye, shafi na 208-211.

4. Wane ra’ayi iri �aya addinai da yawa suke da shi game da mutuwa?5, 6. Menene Littafi Mai Tsarki ya koyar game da yanayin matattu?

58 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

ne ne kuma ba ma tsira daga mutuwarjikinmu. Rai da muke da shi kamar wutarkyandir ne. Sa’ad da aka kashe wutar ba tatafiya ko’ina. Hakika ta daina wanzuwa.

ABIN DA YESU YA CE GAMEDA MUTUWA

7 Yesu Kristi ya yi magana game da yana-yin matattu. Ya yi hakan game da Li’azaru,mutum da ya sani sosai da ya mutu. Yesuya gaya wa almajiransa: “Abokinmu Li’aza-ru yana barci.” Almajiran suna tsammanincewa Yesu yana nufin Li’azaru yana barcinhutawa ne, domin yana samun sau�i dagarashin lafiyarsa. Amma ba haka yake nufiba. Yesu ya yi bayani: “Li’azaru ya mutu.”(Yohanna 11:11-14) Ka lura cewa Yesu yakwatanta mutuwa da hutu da kuma barci.Li’azaru bai je sama ba kuma ba a jefa shijahannama ba. Ba ya tare da mala’iku ko kuma da kakan-ni. Kuma ba a haifi Li’azaru ba ya zama wani mutumdabam. Yana hutawa ne cikin mutuwa, kamar dai yana bar-ci ne mai zurfi ba tare da mafarki ba. Wasu nassosi ma sunkwatanta mutuwa da barci. Alal misali, sa’ad da aka jejjefiIstafanus aka kashe shi, Littafi Mai Tsarki ya ce “ya yi barci.”(Ayukan Manzanni 7:60) Hakazalika, manzo Bulus ya rubu-ta game da wasu a zamaninsa da suka ‘yi barcin’ mutuwa.—1 Korinthiyawa 15:6.

8 Shin ainihin nufin Allah ne mutane su mutu? A’a! Je-hobah ya halicci mutum domin ya rayu har abada aduniya. Kamar yadda muka koya a baya a wannan littafin,Allah ya saka ma’aurata na fari a cikin aljanna mai ni’ima.Ya albarkace su da �oshin lafiya. Jehobah ya bukaci musu

7. Ta yaya Yesu ya yi bayanin yadda mutuwa take?8. Ta yaya muka sani cewa ba nufin Allah ba ne mutane su mutu?

Ina wutarta tafi?

Ina Matattu Suke?

abin da ke mai kyau. Da wani mahaifi da zai so ’ya’yan-sa su wahala daga azaba ta tsufa da kuma mutuwa? Hakika,babu! Jehobah yana �aunar ’ya’yansa kuma yana so sumore rayuwa cikin farin ciki a duniya. Game da mutane,Littafi Mai Tsarki ya ce: “[Jehobah] ya kuma sa madawa-man zamanai a cikin zuciyarsu.”’ (Mai-Wa’azi 3:11) Allahya halicce mu da muradin mu ci gaba da rayuwa har abada.Kuma ya bu�e hanyar biyan wannan muradi.

Jehobah ya halicci mutane surayu har abada a duniya

60 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

ABIN DA YA SAMUTANE SUKE MUTUWA

9 To, me ya sa mutane suke mutuwa? Domin mu samiamsar, dole ne mu bincika abin da ya faru sa’ad da mutanebiyu ne kawai mata da miji suke duniya. Littafi Mai Tsar-ki ya yi bayani: “Kowane itacen da ke mai-sha’awan gani,masu-kyau kuwa domin ci, Ubangiji Allah ya sa ya tsirodaga �asa.” (Farawa 2:9) Amma, da wani abin da ya hana.Jehobah ya gaya wa Adamu: “An yarda maka ka ci daga ko-wane itacen gona a s

¯ake: amma daga itace na sanin nagarta

da mugunta ba za ka �iba ba ka ci: cikin rana da ka ci, mu-tuwa za ka yi lallai.” (Farawa 2:16, 17) Wannan umurnin bashi da wuyar a bi shi. Da wasu itatuwa da yawa da Adamuda Hauwa’u za su ci. Sai suka sami zarafi su nuna godiyar-su ta musamman ga Wanda ya ba su dukan abin da sukeda shi, ha�e da kamiltaccen rai. Biyayyarsu za ta nuna cewasuna daraja ikon Ubansu na samaniya kuma suna son ja-gorarsa ta �auna.

10 Abin ba�in ciki, ma’aurata na farko suka za�i su yiwa Jehobah rashin biyayya. Da yake magana ta bakin ma-ciji, Shai�an ya tambayi Hauwa’u: “Ashe, ko Allah ya ce,ba za ku ci daga dukan itatuwa na gona ba?” Hauwa’u taamsa: “Daga ’ya’ya na itatuwan gona an yarda mamu muci: amma daga ’ya’yan itace wanda ke cikin tsakiyar gona,Allah ya ce, ba za ku ci ba, ba kuwa za ku ta�a ba, dominkada ku mutu.”—Farawa 3:1-3.

11 “Ba lallai ba za ku mutu ba,” in ji Shai�an. “Al-lah ya sani ran da kuka ci daga ciki, ran nan idanunkuza su bu�e, za ku zama kamar Allah, kuna sane da nagar-ta da mugunta.” (Farawa 3:4, 5) Shai�an yana so Hauwa’u

9. Wane hani Jehobah ya yi wa Adamu, kuma me ya sa wannan umur-nin ba mai wuyan biyayya ba ne?10, 11. (a) Ta yaya ma’aurata na fari suka yi wa Allah rashin biyay-ya? (b) Me ya sa rashin biyayya na Adamu da Hauwa’u abu ne maitsanani?

Ina Matattu Suke? 61

ta gaskata cewa ita za ta amfana idan ta ci ’ya’yan itaceda aka hana. In ji shi, za ta za�i wa kanta abin da ke na-garta da mugunta; za ta yi abin da take so. Shai�an kumaya ce Jehobah �arya yake yi game da sakamakon cin ’ya-’yan itacen. Hauwa’u ta gaskata Shai�an. Sai ta ci ’ya’yanitacen. Sai ta ba da wasu ga mijinta, shi ma ya ci. Ba ci-kin rashin sani ba ne suka yi hakan. Sun sani cewa sunayin abin da Allah ya gaya musu kada su yi. Ta wajen cin’ya’yan itacen, sun �i yin biyayya da gangan ga umurnimai sau�i. Sun nuna suna �yamar Ubansu na samaniya dakuma ikonsa. Irin wannan reni ga Mahaliccinsu mai �au-na ba abin gafartawa ba ne!

Adamu ya fito daga tur�aya,kuma ya koma tur�aya

62 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

12 Alal misali: Yaya za ka ji idan ka raini kuma ka �aunaciyaro ko yarinya wanda ya yi maka rashin biyayya a hanyarda ta nuna ba ya ganin mutuncinka ba ya �aunarka? Wan-nan zai �ata maka rai �warai. To, ka yi tunanin yaddaJehobah ya ji sa’ad da Adamu da Hauwa’u suka bi tafarkinhamayya da shi.

13 Jehobah ba shi da wani dalilin ci gaba da raya Adamuda Hauwa’u. Suka mutu, kamar yadda ya ce zai faru dasu. Adamu da Hauwa’u suka daina wanzuwa. Ba su �au-ra zuwa duniyar ruhu ba. Mun fahimci haka domin abinda Jehobah ya gaya wa Adamu bayan ya gaya masa laifin-sa. Allah ya ce: “[Za] ka koma �asa; gama daga cikinta akaciro ka, gama tur�aya ne kai, ga tur�aya za ka koma.” (Fa-rawa 3:19) Allah ya halicci Adamu daga tur�aya. (Farawa2:7) Kafin nan, Adamu bai wanzu ba. Saboda haka, sa’adda Jehobah ya ce Adamu zai koma tur�aya, yana nufi necewa Adamu zai koma yanayinsa na rashin wanzuwa.Adamu zai zama marar rai kamar tur�aya da aka yi sa daita.

14 Da Adamu da Hauwa’u suna da rai a yau, amma sunmutu domin sun za�i su yi wa Allah rashin biyayya kumasaboda haka suka yi zunubi. Abin da ya sa muke mutu-wa shi ne dukanmu zuriyarsa mun g

¯aji yanayin zunubi da

kuma mutuwa daga Adamu. (Romawa 5:12) Wannan zu-nubi kamar wata muguwar cuta ce da muka g

¯ada da babu

wanda zai tsira. Sakamakon ta mutuwa, la’ana ce. Mutuwaabokiyar gaba ce, ba abokiya ba. (1 Korinthiyawa 15:26) Yakamata mu zama masu godiya matu�a ga Jehobah wandaya yi tanadin fansa domin ya cece mu daga wannan aboki-yar gaba abar tsoro!

12. Menene zai taimake mu mu fahimci yadda Jehobah ya ji sa’ad daAdamu da Hauwa’u suka bi tafarkin hamayya da shi?13. Menene Jehobah ya ce zai sami Adamu idan ya mutu, kuma me-nene wannan yake nufi?14. Me ya sa muke mutuwa?

Ina Matattu Suke? 63

SANIN GASKIYA GAME DAMUTUWA YANA DA AMFANI

15 Abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar game da yanayinmatattu yana sanyaya zuciya. Kamar yadda muka gani ma-tattu ba sa shan azaba ko kuma akuba. Babu dalilin jintsoronsu, domin ba za su iya mana illa ba. Ba sa bukatar tai-mako daga gare mu, kuma ba za su iya taimakonmu ba. Baza mu iya magana da su ba, ba za su iya magana da mu ba.Shugaban addinai da yawa suna da’awar cewa za su iya tai-makon wa�anda suka mutu, kuma mutane da suka gaskatairin wa�annan shugabanni sai su ba su ku�i. Amma saningaskiya yana �are mu daga yaudarar wa�anda suke koyarda irin wannan �arya.

16 Shin addininka ya jitu da abin da Littafi Mai Tsarkiyake koyarwa game da matattu kuwa? Yawanci ba su jituba. Me ya sa? Domin Shai�an ya rinjayi koyarwarsu. Yanaamfani da addinan �arya domin ya sa mutane su gaskatacewa bayan jikinsu ya mutu, za su ci gaba da rayuwa a wataduniya ta ruhu. Wannan wata �arya ce da Shai�an yakeha�awa da wasu ya sa mutane su juya wa Jehobah Allahbaya. Ta yaya?

17 Kamar yadda muka gani a baya, wasu addinai sun ko-yar da cewa idan mutum ya yi mummunar rayuwa, bayanya mutu zai je wurin da ake azabtar da mutane ya dawwa-ma yana wahala. Irin wannan koyarwar ba ta daraja Allah.Jehobah, Allah ne mai �auna ba zai ta�a sa mutane su wa-hala a wannan hanyar ba. (1 Yohanna 4:8) Yaya za ka jigame da mutumin da ya hori yaronsa marar biyayya tawajen saka hannunsa cikin wuta? Za ka �auki wannan mu-tumin da mutunci? Za ka ma so ka san irin wannanmutumin? Ba za ka so ba! Wata�ila ka ce lalle mutumin az-zalumi ne. Duk da haka, Shai�an yana so mu gaskata cewa

15. Me ya sa sanin gaskiya game da mutuwa yana sanyaya zuciya?16. Waye ya rinjayi koyarwar addinai da yawa, kuma ta wace hanya?17. Me ya sa koyarwar azabtarwa cikin wuta ba ta daraja Jehobah?

64 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

Jehobah yana azabtar da mutane a cikin wuta har abada—na shekaru biliyoyi marasa iyaka!

18 Shai�an kuma yana amfani da wasu addinai ya koyarda cewa bayan mutane sun mutu suna zama ruhohi dadole ne rayayyu su daraja su. In ji irin wannan koyarwa,ruhun matattu suna zama aminai ko kuma abokan gaba.Mutane da yawa sun gaskata wannan �arya. Suna tsoronmatattu sukan daraja su kuma suna bauta musu. Akasarinhaka, Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa matattu suna barcikuma ya ce mu bauta wa Jehobah Allah shi ka�ai, Mahalic-cinmu kuma Mai yi mana tanadi.—Ru’ya ta Yohanna 4:11.

19 Sanin gaskiya game da matattu zai k¯are ka daga yauda-

ra ta addini. Zai kuma taimake ka ka fahimci wasu koyarwana Littafi Mai Tsarki. Alal misali, sa’ad da ka fahimci cewamutane ba sa zuwa duniyar matattu, alkawarin rai madaw-wami zai kasance da ma’ana a gare ka.

20 A d¯a can, mutum adali Ayuba ya yi wannan tambayar:

“Idan mutum ya mutu za ya sake rayuwa?” (Ayuba 14:14)Shin za a iya ta da mutumin da yake barcin mutuwa zuwarai kuma? Koyarwar Littafi Mai Tsarki game da wannanyana sanyaya zuciya, kamar yadda babi na gaba zai nuna.

18. Bautar matattu ta kasance ne bisa wace �arya ta addini?19. Sanin gaskiya game da mutuwa zai taimake mu mu fahimci wacekoyarwa ta Littafi Mai Tsarki?20. Wace tambaya za mu bincika a babi na gaba?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

ˇ Matattu ba sa gani ba sa ji ba sa tunani.—Mai-Wa’azi 9:5.

ˇ Matattu suna hutawa ne; ba sa wahala.—Yohanna 11:11.

ˇ Muna mutuwa domin mun gaji zunubi dagaAdamu.—Romawa 5:12.

Ina Matattu Suke? 65

KA YI tunanin kana tsere wa wani mugun abokin gaba. Yafi ka �arfi kuma ya fi ka gudu. Ka san cewa ba shi da tausayidomin ka ga yadda ya kashe wasu abokanka. Dukan �o�arida ka yi ka guje masa, sai kusa yake yi da kai. Kuma babuwani bege. Kwatsam, sai mai ceto ya �ullo daga gefenka. Yafi abokin gabanka �arfi sosai, kumayayi maka alkawarin zaitaimake ka. Wannan zai kwantar maka da hankali!

2 Awata hanya, irinwannan abokin gaba yana bin ka. Ha-kika, dukanmu. Kamar yadda muka koya a babi na baya,Littafi Mai Tsarki ya kira mutuwa abokiyar gaba. Babu wanicikinmu da zai iya guje mata. Da yawa cikinmu mun gawannan abokiyar gaba ta halaka mutane da muke �auna.Amma Jehobah ya fi mutuwa �arfi sosai. Shi ne mai Cetomai �auna wanda yake nuna mana yana shirye ya yi nasaraa kan wannan abokiyar gaba. Kuma ya yi alkawarin zai ha-laka wannan abokiyar gaba, mutuwa, har abada. Littafi MaiTsarki ya ce: “Ma�iyi na �arshe da za a kawar, mutuwa ne.”(1 Korinthiyawa 15:26) Wannan albishir ne babu shakka!

3 Bari mu �an bincika yadda wannan abokiyar gaba takeshafanmu sa’ad da ta �auki wani. Yin haka zai taimake mu

1-3. Wace abokiyar gaba ce take bin dukanmu, kuma me ya sa binci-ka abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar zai ba mu kwanciyar hankali?

BABI NA BAKWAI

Bege na Gaskiya ga�aunatattunka da Suka Mutu

Ta yaya muka sani cewa za a yi tashinmatattu da gaske?

Yaya Jehobah yake ji game da ta da matattu?

Waye za a ta da daga matattu?

mu fahimci wani abin da zai sa mu farin ciki. Jehobah ya yialkawarin cewa matattu za su sake rayuwa. (Ishaya 26:19) Zaa sake mai da su su rayu. Wannan shi ne bege na tashin ma-tattu.

SA’AD DA �AUNATACCE YA MUTU4 Wani wanda kake �auna ya ta�a rasuwa? Ba�in ciki, da

makoki, da ganin ba abin da za mu iya yi sai su cika mutum.A irin wa�annan lokatai, muna bukata mu je ga Kalmar Al-lah domin ta’aziyya. (2 Korinthiyawa 1:3, 4) Littafi MaiTsarki ya taimaka mana mu fahimci yadda Jehobah da Yesusuke ji game da mutuwa. Yesu, da ya ke kamanin Ubansa,ya san ba�in cikin rasuwar wani. (Yohanna 14:9) Sa’ad daYesu ya je Urushalima, Yesu yakan ziyarci Li’azaru da yay-yensa mata, Maryamu da Marta wa�anda suke gari na kusa,wato Betanya. Suka zama aminai. Littafi Mai Tsarki ya ce:“Yesu dai yana �aunar Martha, da ’yar’uwarta, da Li’azaru.”(Yohanna 11:5) Kamar yadda muka gani a babi na baya, saiLi’azaru ya mutu.

5 Yaya Yesu ya ji game da rashin abokinsa? Labarin ya ceYesu ya je wurin dangin Li’azaru da kuma abokanansa sa’adda suke makoki. Ganin su ya motsa Yesu �warai. “Ya ji hau-shi cikin ruhunsa, yana jin zafi a ransa.” Sai, labarin ya ce,“Yesu ya yi kuka.” (Yohanna 11:33, 35) Hawayen Yesu sunnuna cewaba shi dabegene?Koka�an.Hakika, Yesu ya sanicewa abin al’ajabi ya kusa faruwa. (Yohanna 11:3, 4) Duk dahaka, ya ji zafi da ba�in ciki da mutuwa take kawowa.

6 A wata hanya, nisawar Yesu tana �arfafa mu. Tana koyamana cewa Yesu daUbansa, Jehobah, ba sa �aunar mutuwa.

4. (a) Menene yadda Yesu ya ji game da mutuwar wanda yake �aunaya koya mana game da yadda Jehobah yake ji? (b) Yesu ya �ulla waceabokantaka ta musamman?5, 6. (a) Yaya Yesu ya yi sa’ad da yake tare da dangi da kuma abo-kanan Li’azaru da suke makoki? (b) Me ya sa nisawar Yesu take�arfafamu?

Bege na Gaskiya ga �aunatattunka da Suka Mutu 67

Amma Jehobah Allah yana da iyawar ya ya�i mutuwa kumaya yi nasara! Bari mu ga abin da Allah ya ba Yesu ikon yi.

“LI’AZARU, KA FITO!”7 An binne Li’azaru a cikin kogo, sai Yesu ya ce a cire du-

tsen da aka rufe bakin kogon da shi. Marta ta ce a’a dominbayan kwana hu�u, gawar Li’azaru ta fara ru�ewa. (Yohan-na 11:39) A matsayin mutane, babu wani abin da za a iya yikuma.

8 Aka �auke dutsen, sai Yesu ya yi kira da babbar murya:“Li’azaru, ka fito.” Menene ya faru? “Shi wanda ya mutu yafito.” (Yohanna 11:43, 44) Za ka iya tunanin irin farin ci-kinmutanen da sukewurin? Ko Li’azaru �an’uwansu ne, kodangi, ko aboki, koma�wabci, sun sani cewayamutu. Sai gashi mutumin da suka sani abin �auna yana tare da su kuma.Hakan kamar ba zai yiwu ba. Da yawa hakika sun rungumiLi’azaru don farin ciki. Hakika wannan nasara ce bisa mu-tuwa!

9 Yesu bai yi da’awar ya yi wannan mu’ujiza mai banal’ajabi da ikon kansa ba. A cikin addu’arsa kafin ya kiraLi’azaru, ya bayyana sarai cewa Jehobah ne Tushen ta damamacin. (Yohanna 11:41, 42) Wannan ba shi ba ne ka-wai lokacin da Jehobah ya yi amfani da ikonsa a wannanhanyar. Tashin Li’azaru yana �aya daga cikin mu’ujizoji tarairin wannan da suke rubuce cikin Kalmar Allah.� Karatuda kuma nazarin wa�annan labaran abin ban farin ciki ne.Sun koya mana cewa Allah ba ya nuna bambanci, domin

� Wasu labaran za a same su a 1 Sarakuna 17:17-24; 2 Sarakuna 4:32-37; 13:20, 21; Matta 28:5-7; Luka 7:11-17; 8:40-56; Ayukan Manzan-ni 9:36-42 da kuma 20:7-12.

7, 8. Me ya sa batun Li’azaru ya kasance kamar babu wani bege gawa�anda suke kallo, amma menene Yesu ya yi?9, 10. (a) Ta yaya Yesu ya nuna Tushen ikon da ya yi amfani da shiya tashi Li’azaru? (b) Menene amfanin karanta labaran Littafi MaiTsarki na tashin matattu?

68 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

Iliya ya ta da �an gwauruwa—1 Sarakuna 17:17-24

Manzo Bitrus ya tada mace Kirista Dokas—Ayukan Manzanni

9:36-42

Tashin Li’azaru dagamatattu ya kawo farin ciki

matu�a—Yohanna 11:38-44

tashin matattun ya ha�a da manya da yara, mata da maza,Isra’ilawa da wa�anda ba Isra’ilawa ba. Kuma wannan sunakwatanta farin ciki mai yawa! Alal misali, sa’ad da Yesu ya tada ’yar yarinyadagamutuwa, iyayenta “sukayimamaki nanda nan da mamaki mai-girma.” (Markus 5:42) Lalle, Jeho-bah ya ba su dalilin farin ciki da ba za su ta�a mantawa ba.

10 Hakika, wa�andaYesu ya ta da sudagamatattu sun sakemutuwa daga baya. Amma wannan ya nuna cewa da ma baa tashe su bane? A’a.Wa�annan labarai na LittafiMaiTsarkisun tabbatar da wata gaskiya mai muhimmanci kuma sunaba mu bege.

KOYO DAGA LABARAN TASHIN MATATTU11 Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa matattu “ba su san

kome ba.” Ba su da rai kuma ba sa rayuwa a wani waje. La-barin Li’azaru ya tabbatar da haka. Bayan ya sake rayuwa,Li’azaru yaburgemutaneneda kwatancinyadda sama take?Kokumaya tsorata sune da labaraimasuban tsoro nawutarjahannama? A’a. Littafi Mai Tsarki bai �unshi irin wa�an-nan labarai ba daga wurin Li’azaru. A cikin kwanakin nanhu�u da yake matacce, bai “san komi ba.” (Mai-Wa’azi 9:5)Li’azaru yana barci ne na mutuwa.—Yohanna 11:11.

12 Labarin Li’azaru kuma ya koya mana cewa tashin ma-tattu gaskiya ne, ba �age ba ne. Yesu ya tashi Li’azaru aidon jama’a ne. Har shugabannin addinai, da ba sa �aunarYesu, ba su musanci wannan mu’ujiza ba. Maimakon hakasuka ce: “Me muke yi? Gama mutumin nan [Yesu] yana yialamu dayawa?” (Yohanna 11:47) Mutane da yawa suna sosu ga Li’azaru da ya tashi daga matattu. Domin haka, dayawa suka ba da gaskiya ga Yesu. Li’azaru ya tabbatar musucewa Allah ne ya aiko Yesu. Wannan tabbacin yana da �arfi

11. Ta yaya labarin tashin Li’azaru daga matattu ya taimaka wajen tab-batar da gaskiyar da take rubuce a Mai-Wa’azi 9:5?12. Me ya sa za mu tabbata cewa tashin Li’azaru daga matattu ya faruda gaske?

70 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

�warai da wasu shugabannin addinin Yahudawa masu tau-rin zukata suka shirya su kashe Yesu da Li’azaru.—Yohanna11:53; 12:9-11.

13 Ba daidai ba ne a gaskata cewa tashin matattu gaskiyane? Daidai ne, domin Yesu ya koyar da cewa wata rana “du-kanwa�anda suna cikin kabarbaru” za a tashe su. (Yohanna5:28) Jehobah shi ne Mahaliccin dukan rai. Zai yi wuyane a gaskata cewa zai iya sake halittar rai? Hakika, yawancizai dangana ne a kan tunanin Jehobah. Zai iya tuna dukan�aunatattunmu da suka mutu kuwa? Taurari marasa iyakasun cika sararin samaniya, duk da haka, Allah ya ba kowa-ne suna! (Ishaya 40:26) Saboda haka, Jehobah Allah zai iyatuna dukan �aunatattunmu da suka mutu, kuma yana shir-ye ya sake ba su rai.

14 Amma, yaya Jehobahyake ji gameda ta damatattu? Lit-tafi Mai Tsarki ya nuna cewa yana �okin ya ta da matattu.Ayuba mutum mai aminci ya yi tambaya: “Idan mutum yamutu, za ya sake rayuwa?”Ayuba yana magana ne game dajira a kabari har sai lokaci ya yi da Allah zai tuna da shi. Yace game da Jehobah: “Za ka yi kira, ni ma in amsa maka:Za ka yi marmarin aikin hannuwanka.”—Ayuba 14:13-15.

15 Ka yi tunani! Jehobah yana murna ya maido da ma-tattu zuwa rai. Ba abin farin ciki ba ne mu fahimci cewaJehobah yana jin haka? Amma tashin matattu da ke zuwa anan gaba kuma fa? Wa za a ta da daga matattu, kuma a ina?

“DUK WA�ANDA KE KABURBURA”16 Labarin Littafi Mai Tsarki na tashin matattu ya koya

mana abubuwa da yawa game da tashin matattu. Muta-ne da aka maido zuwa rai a nan duniya sun sake saduwa

13. Wane dalili muke da shi na gaskata cewa Jehobah hakika zai iyata da matattu?14, 15. Kamar yadda abin da Ayuba ya ce ya kwatanta, yaya Jehobahyake ji game da ta da matattu zuwa rai?16. Za a tashi matattu a wane irin yanayi?

Bege na Gaskiya ga �aunatattunka da Suka Mutu 71

da wa�anda suke �auna. Tashin matattu na nan gaba zai yikama da wannan—amma zai fi kyau. Kamar yadda mukakoya daga Babi na 3, nufin Allah shi dukan duniya ta zamaaljanna. Saboda haka matattu ba za a tashe su a duniya datake cike da ya�e-ya�e, yin laifi, da kuma cututtuka ba. Za susami zarafin su rayu a wannan duniya a cikin yanayi na lu-mana da farin ciki.

17 Wa za a tasa? Yesu ya ce ‘dukan wa�anda suna cikinkabarbaru [da aka tuna da su] za su ji muryatasa [Yesu], sufito kuma.’ (Yohanna 5:28, 29) Hakazalika, Ru’ya ta Yohan-na 20:13 ta ce: “Teku kuma ya bada matattun da ke cikinsa;mutuwa da Hades kuma suka bada matattun da ke cikin-su.” “Hades” na nufin kabari na ’yan adam. (Dubi Rataye,shafuffuka 212-213.) Wa�annan kaburbura za su kasanceba kome cikinsu. Dukan biliyoyin mutane da suka huta acikinsu za su sake samun rai. Manzo Bulus ya ce: “Za a yi ta-shin matattu, na masu-adalci da na marasa-adalci.” (AyukanManzanni 24:15) Menene wannan yake nufi?

18 “Masu-adalci” sun ha�a da yawancin mutane da mukakaranta game da su a cikin Littafi Mai Tsarki wa�anda sukarayu kafin Yesu ya zo duniya. Za ka tuna da Nuhu, Ibrahim,Saratu, Musa, Rut, Esta, da wasu kuma masu yawa. Wasucikinwa�annanmaza damatamasu bangaskiya anyimaga-narsu a Ibraniyawa sura 11. Amma “masu-adalci” kuma sunha�a da bayin Jehobah na zamaninmu. Godiya t

¯a tabbata

ga begen tashin matattu, mun ’yantu daga tsoron mutuwa.—Ibraniyawa 2:15.

19 To mutanen da ba su bauta wa Jehobah ba kuma basu yi masa biyayya ba domin ba su san shi ba fa? Wa�an-nan biliyoyi na “marasa-adalci” ba za a manta da su ba. Su

17. Yaya yawan tashin matattun zai kasance?18. “Masu-adalci” da za a tashe su daga matattu sun ha�a da su waye,kuma ta yaya wannan begen zai shafe ka?19. Su waye ne “marasa-adalci,” kuma wane zarafi Jehobah ya ba sudon alherinsa?

72 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

ma za a ta da su kuma a ba su lokaci so koyi game da Al-lah na gaskiya kuma su bauta masa. A cikin shekara dubu,za a ta da matattu kuma a ba su zarafin su ha�u da mutanemasu aminci a duniya su bauta wa Jehobah. Zai kasance lo-kaci mai ban sha’awa. Wannan lokaci ne Littafi Mai Tsarkiyake kira Ranar Hukunci.�

20 Amma wannan yana nufi ne cewa dukan wani mutu-min da ya ta�a rayuwa za a tashe shi daga matattu? A’a.Littafi Mai Tsarki ya ce wasu matattu suna “Jahannama.”(Luka12:5) Jahannama ta samo sunanta nedaga juji da yakebayan Urushalima ta d

¯a. Gawaki da kuma datti ake �onawa

awurin. Yahudawa sun ga cewa gawawwaki da aka jefa a canba su cancanci a binne su kuma a tada su daga matattu ba.Saboda haka Jahannama alama ce da ta dace na madawwa-miyar halaka. Ko da yake Yesu zai saka hannu wajen yi warayayyu da matattu hukunci, Jehobah shi ne babban Al�ali.(Ayukan Manzanni 10:42) Ba zai ta da wa�anda ya ga miya-gu ne da ba su da niyyar canji.

TASHIN MATTATU ZUWA SAMA21 Littafi Mai Tsarki ya kwatanta wani irin tashin matattu

zuwa rayuwa ta ruhu a sama. Misali �aya ne kawai aka ru-buta a cikin Littafi Mai Tsarki na irin wannan tashi, na YesuKristi.

22 Bayan an kashe Yesu, Jehobah bai �yale �ansa maiaminci ya kasance a cikin kabari ba. (Zabura 16:10; Ayu-kan Manzanni 13:34, 35) Allah ya ta da Yesu daga matattu,amma bai tashe shi mutum ba. Manzo Bitrus ya yi bayanicewa “An matar da shi cikin jiki, amma an rayadda shi cikin

� Domin �arin bayani game da Ranar Hukunci da kuma dalilin hu-kunci, don Allah ka dubi Rataye, shafuffuka na 213-215.

20. Menene Jahannama, kuma waye suke zuwa can?21, 22. (a) Wane irin tashin matattu ne kuma ke akwai? (b) Wane-ne ne na farko da ya sami tashin matattu zuwa rayuwa ta ruhu?

Bege na Gaskiya ga �aunatattunka da Suka Mutu 73

ruhu.” (1 Bitrus 3:18) Wannan hakika babbar mu’ujiza ce.Yesu ya sake rayuwa, ruhu ne mai iko �warai! (1 Korinthiya-wa 15:3-6) Yesu shi ne na farko wajen samun irin wannantashinmatattu na �aukaka. (Yohanna 3:13) Ammaba shi nena �arshe ba.

23 Domin ya sani ba da da�ewa ba zai koma sama, Yesuya gaya wa mabiyansa masu aminci cewa zai ‘shirya musuwuri’ a can. (Yohanna 14:2) Yesu ya kira wa�anda za su tafisama “�aramin garke.” (Luka 12:32) Mutane nawa ne za sukasance a cikin wannan �aramin rukuni na Kiristoci masuaminci? In ji Ru’ya ta Yohanna 14:1, manzo Yohanna ya ce:“Na duba kuma, ga �an ragon [Yesu Kristi] yana tsaye bisadutsen Sihiyona, tare da shi kuma mutum zambar �ari dazambar arba’in da hu�u, suna da sunansa, da sunan Uban-sa, a rubuce bisa goshinsu.”

24 Wa�annan Kiristoci 144,000, sun ha�a da manzanninYesu masu aminci, da aka ta da zuwa rayuwa a sama. Yau-she ne tashinsu daga matattu ya kasance? Manzo Bulus yarubuta cewa zai faru a lokacin bayyanuwar Kristi. (1 Ko-rinthiyawa 15:23) Kamar yadda za ka fahimta a Babi na 9,yanzumunawannan lokacinne. Sabodahaka raguwar 144,-000 wa�anda suka mutu a zamaninmu ana ta da su a takezuwa rayuwa a sama. (1 Korinthiyawa 15:51-55) Amma ya-wancin ’yan adam suna da begen tashi daga matattu cikinAljanna a duniya.

25 Hakika, Jehobah zai yi nasara bisa abokiyar gabanmumutuwa, kuma za ta shu�e har abada! (Ishaya 25:8) Ammawata�ila kayimamaki, ‘Menenewa�anda aka tashe su zuwasama za su yi a can?’ Za su kasance a cikin gwamnati maiban sha’awana Mulkin sama. Zamu koyi abubuwa game dawannan gwamnatin a babi na gaba.

23, 24. Su waye suke cikin “�aramin garke” na Yesu, kuma adadinsunawa ne?25. Menene za a bincika a cikin babi na gaba?

74 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

ˇ Labarin tashin matattu na Littafi MaiTsarki ya ba mu tabbataccen bege.—Yohanna11:39-44.

ˇ Jehobah yana �okin ya ta da matattu zuwarai.—Ayuba 14:13-15.

ˇ Dukan wa�anda suke cikin kaburbura na ’yanadam za a tashe su.—Yohanna 5:28, 29.

A Aljanna, za a ta da matattu kumaza su sake saduwa da wa�anda suke �auna

Bege na Gaskiya ga �aunatattunka da Suka Mutu 75

MILIYOYIN mutane a dukan duniya suna sane da ad-du’ar da yawanci suke kira Ubanmu, ko kuma Addu’arUbangiji. Wa�annan furci biyu suna magana ne game dafitacciyar addu’ar da Yesu Kristi kansa ya yi na kwatanci.Addu’a ce mai ma’ana �warai, bincika abubuwa uku daya ro�a da fari za ta taimake mu mu koyi abin da ainihiLittafi Mai Tsarki yake koyarwa.

2 A farkon addu’ar kwatanci, Yesu ya umurci masu sau-raronsa: “Da hakanan fa za ku yi addu’a: Ubanmu wandake cikin sama, a tsarkake sunanka. Mulkinka shi zo, abinda ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsacikin Sama.” (Matta 6:9-13) Menene muhimmancin wa-�annan ro�o guda uku?

3 Mun riga mun fahimci abubuwa da yawa game dasunan Allah, Jehobah. Kuma mun tattauna game da nu-fin Allah—abin da ya yi da kuma wa�anda zai yi ga ’yanadam. Amma, me Yesu yake magana a kai sa’ad da yagaya mana mu yi addu’a: “Mulkinka shi zo”? Menene

1. Wace fitacciyar addu’a ce za a bincika a yanzu?2. Menene abubuwa uku daga cikin abin da Yesu ya koya wa almaji-ransa su ro�a a addu’a?3. Me muke bukata mu sani game da Mulkin Allah?

BABI NA TAKWAS

Menene Mulkin Allah?

Menene Littafi Mai Tsarki ya gaya managame da Mulkin Allah?

Menene Mulkin Allah zai yi?

Yaushe ne Mulkin zai sa a yi nufinAllah a duniya?

Mulkin Allah? Ta yaya zuwansa zai tsarkake sunan Allah?Kuma ta yaya zuwan Mulkin yake da nasaba da yin nufinAllah?

ABIN DA MULKIN ALLAH YAKE NUFI4 Mulkin Allah gwamnati ne da Jehobah Allah ya kafa

kuma ya za�a masa Sarki. Wanene Sarkin Mulkin Al-lah? Yesu Kristi. Sarki Yesu ya fi dukan sarakuna mutanesaboda haka aka kira shi “Sarkin sarakuna, Ubangijin iya-yengiji.” (1 Timothawus 6:15) Yana da ikon ya yi alherifiye da dukan wani sarki mutum, har ma mafi kirki a tsa-kaninsu.

5 Daga ina ne Mulkin Allah zai yi sarauta? To, a inaYesu yake? Ka tuna ka koyi cewa an kashe shi a kan gun-gumen azaba, sai kuma aka tashe shi daga matattu. Bada da�ewa ba bayan haka, ya koma sama. (Ayukan Man-zanni 2:33) Saboda haka, a nan ne Mulkin Allah yake—asama. Abin da ya sa ke nan Littafi Mai Tsarki ya kira shi‘Mulkin sama.’ (2 Timothawus 4:18) Ko da yake MulkinAllah yana sama, zai mallaki duniya.—Ru’ya ta Yohanna11:15.

6 Menene ya sa Yesu ya zama Sarki na musamman? Da-lili �aya shi ne, ba zai mutu ba. Sa’ad da Littafi Mai Tsarkiyake kwatanta Yesu da sarki �an adam, ya ce “shi ka�aiyana da rashin mutuwa, mazauni cikin haske wanda bashi kusantuwa.” (1 Timothawus 6:16) Wannan yana nu-fin cewa dukan alherin da Yesu zai yi zai dawwama. Kumazai yi manyan abubuwa nagari.

7 Ka yi la’akari da wannan annabci na Littafi Mai Tsar-ki game da Yesu: “Ruhun Ubangiji za ya zauna bisansa,ruhun ilimi da na ganewa, ruhun shawara da iko, ruhun

4. Menene Mulkin Allah, kuma waye ne Sarkin?5. Daga ina Mulkin Allah zai yi sarauta, kuma a kan waye?6, 7. Menene ya sa Yesu ya zama Sarki na musamman?

Menene Mulkin Allah? 77

sani da na tsoron Ubangiji: jin da�insa kuma za ya kasan-ce a cikin tsoron Ubangiji: ba za ya yi shari a bisa ga abinda ya bayyana ga idanunsa ba, ba kuwa za shi yanka ma-gana bisa ga abin da kunnensa ke ji ba: amma da adalciza ya yi ma talakawa shari’a, da daidaita kuma za ya yan-ka magana domin masu-tawali’u na duniya.” (Ishaya 11:2-4) Wa�annan kalmomin sun nuna cewa Yesu zai kasan-ce Sarki mai adalci mai juyayi bisa mutanen duniya. Za kaso ka sami sarki kamar haka?

8 Da wani abu kuma game da Mulkin Allah: Yesu bazai yi sarauta shi ka�ai ba. Zai kasance da abokan sa-rauta. Alal misali, manzo Bulus ya gaya wa Timothawus:“Idan mun jimre, za mu kuma yi mulki tare da shi.”(2 Timothawus 2:12) Hakika, Bulus, Timothawus, dawasu masu aminci da Allah ya za�a za su yi sarauta tareda Yesu a Mulkin sama. Mutane nawa ne za su sami wan-nan gatar?

9 Kamar yadda aka nuna a Babi na 7 na wannan lit-tafin, an bai wa manzo Yohanna wahayi da ya ga “�anragon [Yesu Kristi] yana tsaye bisa dutsen Sihiyona [ma-tsayinsa na sarauta a sama], tare da shi kuma mutumzambar �ari da zambar arba’in da hu�u, suna da sunan-sa, da sunan Ubansa, a rubuce bisa goshinsu.” Su waye newa�annan 144,000? Yohanna da kansa ya gaya mana: Sune kan bi �an Rago inda ya tafi duka. Aka fanshi wa�an-nan daga cikin mutane, su zama nunan fari ga Allah da�an Rago.” (Ru’ya ta Yohanna 14:1, 4) Hakika, mabiyanYesu Kristi ne masu aminci da aka za�a musamman su yisarauta tare da shi a sama. Bayan an ta da su daga matattuzuwa rayuwa ta sama, za su kuwa yi “mulki bisa duniya”tare da Yesu. (Ru’ya ta Yohanna 5:10) Tun daga zamanin

8. Waye zai yi mulki da Yesu?9. Mutane nawa ne za su yi sarauta tare da Yesu, kuma yaushe Allahya fara za�ansu?

78 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

manzanni, Allah ya yi ta za�an Kiristoci masu aminci do-min su cika wannan adadi na 144,000.

10 Shirin da aka yi domin Yesu da mutane 144,000 su yisarauta bisa ’yan adam �auna ce. Dalili guda shi ne, Yesuya san wahalar mutane. Bulus ya ce Yesu ba “wanda bashi ta�uwa da tarayyar kumamancinmu ba: amma wan-da an jarabce shi a kowace fuska kamarmu, sai dai bandazunubi.” (Ibraniyawa 4:15; 5:8) Abokanan sarautarsa masa’ad da suke mutane sun wahala kuma sun jure. �ari gahaka, sun yi fama da ajizanci kuma sun jimre wa dukanire-iren cututtuka. Hakika, za su fahimci matsaloli da mu-tane suke fuskanta!

MENENE MULKIN ALLAH ZAI YI?11 Sa’ad da Yesu ya ce wa almajiransa su yi addu’a Mul-

kin Allah ya zo, ya kuma ce su yi addu’a a yi nufin Allah“cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.” Al-lah a sama yake, kuma a kullum mala’iku masu amincisuna yin nufinsa. A Babi na 3 na wannan Littafin, munkoyi cewa wani mugun mala’ika ya daina yin nufin Al-lah kuma ya sa Adamu da Hauwa’u suka yi zunubi. A Babina 10, za mu sami �arin bayani game da abin da LittafiMai Tsarki yake koyarwa game da wannan mugun mala’i-ka, da muka sani da Shai�an Iblis. Shai�an da kuma wasumala’iku da suka za�i su bi shi—da ake kira aljannu—an�yale su su zauna a sama na �an lokaci. Saboda haka, baduka ba ne suke yin nufin Allah a sama a lokacin. Hakaba zai kasance ba sa’ad da Mulkin Allah ya fara sarau-ta. Sabon Sarki da aka na�a, Yesu Kristi, zai ya�i Shai�an.—Ru’ya ta Yohanna 12:7-9.

10. Me ya sa �auna ce shirin da aka yi Yesu da mutane 144,000 su yisarauta bisa ’yan adam?11. Me ya sa Yesu ya ce wa almajiransa su yi addu’a a yi nufin Allaha sama?

Menene Mulkin Allah? 79

12 Wa�annan kalmomi na annabci sun kwatanta abinda zai faru: “Na ji babbar murya kuma cikin sama,ta ce, Yanzu ceto, da iko, da mulkin Allahnmu ya zo,da sarautar Kristinsa kuma: gama an jefarda mai-saran’yan’uwanmu, shi wanda ya ke sararsu dare da rana a ga-ban Allahnmu.” (Ru’ya ta Yohanna 12:10) Ka lura daaukuwa biyu masu muhimmanci da aka kwatanta a wan-nan ayar Littafi Mai Tsarki? Na farko, Mulkin Allah ahannun Yesu Kristi ya fara sarauta. Na biyu, an jefo Shai-�an daga sama zuwa duniya.

13 Menene sakamakon wa�annan aukuwa biyu? Gameda abin da ya faru a sama, mun karanta: “Domin wan-nan fa, ku yi farinciki, ya sammai, da ku mazauna a ciki.”Hakika, mala’iku masu aminci a sama sun yi farin cikidomin Shai�an da aljannunsa ba sa sama kuma, kowa asama mai aminci ne ga Jehobah Allah. Sun sami cikakkensalama da jituwa. Ana yin nufin Allah a sama.

14 To, duniya kuma fa? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kaitonduniya da teku: domin Shai�an ya sauko wajenku, hasalamai-girma kuwa gareshi, domin ya sani sauran zarafinsaka�an ne.” (Ru’ya ta Yohanna 12:12) Shai�an yana fushidomin an jefo shi daga sama kuma lokacinsa ya �ure. Acikin fushinsa yana haddasa matsaloli, ko kuma ‘kaito,’ga duniya. Za mu sami �arin bayani game da “kaiton” ababi na gaba. Amma da tunanin wannan, za mu iya tam-baya, Ta yaya Mulkin zai sa a yi nufin Allah a duniya?

15 To, ka tuna nufin Allah ga duniya. Ka koyi game dawannan a Babi na 3. A Adnin, Allah ya nuna cewa nufin-sa ne duniya ta zama aljanna cike da mutane masu adalci

12. Wa�anne aukuwa biyu ne masu muhimmanci aka kwatanta aRu’ya ta Yohanna 12:10?13. Menene sakamakon jefo Shai�an daga sama?14. Menene ya faru domin an jefo Shai�an zuwa duniya?15. Menene nufin Allah ga duniya?

80 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

marasa mutuwa. Shai�an ya sa Adamu da Hauwa’u sukayi zunubi, wannan ya shafi cikan nufin Allah ga duni-ya amma bai canja shi ba. Har yanzu Jehobah ya nufacewa “masu-adalci za su gaji �asan, su zauna a cikintahar abada.” (Zabura 37:29) Kuma Mulkin Allah zai cimma wannan. A wace hanya?

16 Ka yi la’akari da annabci da ke Daniel 2:44. Anan mun karanta: “A cikin zamanin wa�annan sarakunakuwa, Allah mai-sama za ya kafa wani mulki, wanda ba zaa rushe shi ba da�ai, sarautarsa kuwa ba za a bar ma wataal’umma ba; amma za ya farfashe dukan wa�annan mul-koki ya cinye su, shi kuwa za ya tsaya har abada.” Menenewannan ya gaya mana game da Mulkin Allah?

17 Da fari, ya gaya mana cewa za a kafa Mulkin Allaha “cikin zamanin wa�annan sarakuna” ko kuma sa’ad dawasu mulkoki suke sarauta. Na biyu, ya gaya mana cewaMulkin za ya tsaya har abada. Kuma ba za a yi nasa-ra a kansa ba ko kuma a sake shi da wasu gwamnatoci.Na uku, mun ga cewa za a yi ya�i tsakanin Mulkin Allahda mulkokin duniya. Mulkin Allah zai yi nasara. A �arshezai zama shi ne ka�ai gwamnati a kan ’yan adam. Sa’annan mutane za su more sarauta mafi kyau.

18 Littafi Mai Tsarki yana da abubuwa da yawa da zaice game da wannan ya�i na �arshe tsakanin Mulkin Al-lah da gwamnatocin duniya. Alal misali, ya koyar dacewa sa’ad da �arshe ya yi kusa, miyagun ruhu za suya�a �arya domin su yaudari “sarakunan dukan duniya.”Domin menene? “Garin su tattara su zuwa ya�in bab-bar rana ta Allah Mai-iko duka.” Sarakunan duniya za atattara su a “wurin da a ke ce da shi da Ibrananci Har–Magedon.” (Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16) Domin abin

16, 17. Menene Daniel 2:44 ta gaya mana game da Mulkin Allah?18. Menene sunan ya�in �arshe tsakanin Mulkin Allah da gwamna-tocin duniya?

Menene Mulkin Allah? 81

da aka ce a wa�annan ayoyi biyu, ya�i na �arshe tsakaningwamnatocin mutane da Mulkin Allah ana kiransa ya�inHar–Magedon ko Armagedon.

19 Menene Mulkin Allah zai cim ma ta wajen Arma-gedon? Ka sake tunani game da nufin Allah ga duniya.Nufin Jehobah Allah shi ne duniya ta cika da mutanemasu adalci, kamilai da suke bauta masa a cikin Aljanna.Menene ya hana wannan daga faruwa a yanzu? Na far-ko, muna masu zunubi, kuma muna rashin lafiya munamutuwa. Mun koya a Babi na 5, cewa Yesu ya mutu do-minmu, saboda mu rayu har abada. Wata�ila, ka tuna dakalaman da ke rubuce a Linjilar Yohanna: “Gama Allah yayi �aunar duniya har ya bada �ansa, haifaffe shi ka�ai,domin dukan wanda yana bada gaskiya gareshi kada yalalace, amma ya sami rai na har abada.”—Yohanna 3:16.

20 Wani dalili kuma shi ne cewa mutane suna aikatamugunta. Suna �arya, suna cuta, kuma suna yin lalata.Ba sa so su yi nufin Allah. Mutane da suke yin miyagunabubuwa za a halaka su a lokacin ya�in Allah na Armage-don. (Zabura 37:10) Wani dalili kuma da ya sa ba a yinnufin Allah a duniya shi ne cewa gwamnatoci ba sa �ar-fafa mutane su yi shi. Wasu gwamnatoci suna da rauni,wasu kuma azzalumai ne, ko kuma malalata. Littafi MaiTsarki ya fa�a kai tsaye: “Mutum ya sami iko bisa wani,ikon kuwa ya ciwuce shi.”—Mai-Wa’azi 8:9.

21 Bayan Armagedon, ’yan adam za su kasance a �ar�a-shin gwamnati guda kawai, wato Mulkin Allah. WannanMulkin zai yi nufin Allah kuma zai kawo albarkatai masuban sha’awa. Alal misali, zai kawar da Shai�an da aljan-nunsa. (Ru’ya ta Yohanna 20:1-3) Za a yi amfani da ikonhadayar Yesu, saboda mutane masu aminci kada su �arayin ciwo ko kuma su mutu. Maimakon haka, a �ar�ashin

19, 20. Me yake hana yin nufin Allah a duniya a yanzu?21. Ta yaya Mulkin zai sa a yi nufin Allah a duniya?

82 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

Jefo Shai�an da aljannunsa dagasama ya jawo matsifu ga duniya.

Irin wa�annan matsifun za su�are ba da �a�ewa ba

sarautar Mulki za su rayu har abada. (Ru’ya ta Yohanna22:1-3) Za a mai da duniya ta zama aljanna. Ta haka Mul-kin zai sa a yi nufin Allah a duniya, kuma zai tsarkakesunan Allah. Menene wannan yake nufi? Wannan yananufin cewa a �arshe dukan wa�anda suke �ar�ashin Mul-kin Allah za su �aukaka sunan Jehobah.

YAUSHE MULKIN ALLAH ZAI SAA YI NUFINSA A DUNIYA?

22 Sa’ad da Yesu ya gaya wa mabiyansa su yi addu’a,“Mulkin ka shi zo,” a bayyane yake cewa Mulkin bai zo batukuna a lokacin. Ya zo ne sa’ad da Yesu ya koma sama?A’a, domin Bitrus da Bulus suka ce bayan tashin Yesudaga matattu, annabcin da ke Zabura 110:1 ta cika a kan-sa: “Ubangiji ya ce ma ubangijina, Ka zauna ga hannundamana, har in maida ma�iyanka matashin sawunka.”(Ayukan Manzanni 2:32-35; Ibraniyawa 10:12, 13) Daakwai lokacin jira.

23 Yaya tsawon lokacin jiran? A �arni na 19 da 20, �a-liban Littafi Mai Tsarki suka game cewa tsawon lokacinjiran, zai �are a shekara ta 1914. (Game da wannan kwa-nan wata, dubi Rataye, shafi na 215-218.) Abubuwa da

22. Ta yaya muka sani cewa Mulkin Allah bai zo ba sa’ad da Yesu yakeduniya ko kuma nan da nan bayan tashinsa daga matattu?23. (a) Yaushe Mulkin Allah ya fara sarauta? (b) Menene za a tattau-na a babi na gaba?

A �ar�ashin sarautar Mulkin, za a yi nufin Allaha duniya kamar yadda ake yi a sama

84 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

suke aukuwa a duniya tun daga shekara ta 1914 sun tab-batar da cewa famintar wa�annan �aliban Littafi MaiTsarki daidai ne. Cikan annabcin Littafi Mai Tsarki yanuna cewa a shekara ta 1914, Kristi ya zama Sarki kumaMulkin Allah na samaya fara sarauta. Saboda haka, munarayuwa ne a lokacin “ka�an” da ya rage wa Shai�an.(Ru’ya ta Yohanna 12:12; Zabura 110:2) Kuma za mu iyacewa da tabbaci ba da da�ewa ba, Mulkin Allah zai sa a yinufin Allah a duniya. Wannan ya kasance labari ne maiban mamaki a gare ka? Ka gaskata cewa gaskiya ne? Babina gaba zai taimake ka ka ga cewa da gaske Littafi Mai Tsa-ki ya koyar da wa�annan abubuwa.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWAˇ Mulkin Allah gwamnati ne na sama wanda

Yesu Kristi ne Sarkinsa, kuma a tsakanin mu-tane an za�i 144,000 su yi sarauta da shi.—Ru’ya ta Yohanna 14:1, 4.

ˇ Mulkin ya fara sarauta a shekara ta 1914,kuma an jefo da Shai�an daga sama zuwa du-niya.—Ru’ya ta Yohanna 12:9.

ˇ Mulkin Allah ba da da�ewa ba zai halakagwamnatocin mutane, kuma duniya za tazama aljanna.—Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16.

Menene Mulkin Allah? 85

KA TA�A kallon labarai a telibijin kuma ka yi mamaki,‘Shin menene duniyarmu take juyawa ta zama?’ Masifusuna fa�owa ba zato ba tsammani da babu mahalukin dazai iya fa�an abin da zai faru gobe. (Ya�ub 4:14) Amma,Jehobah ya san abin da zai faru a nan gaba. (Ishaya 46:10)Tun a d

¯a can Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki, ta fa�i miyagun

abubuwa da suke faruwa a zamaninmu da kuma abubu-wa masu ban sha’awa da za su faru a nan gaba ba dada�ewa ba.

2 Yesu Kristi ya yi magana game da Mulkin Allah, wan-da zai kawo �arshen dukan mugunta kuma ya mai daduniya ta zama aljanna. (Luka 4:43) Mutane suna so susan lokacin da Mulkin zai zo. Almajiran Yesu sun tamba-ye shi: “Me ne kuma alamar zuwanka da cikar zamani?”(Matta 24:3) Yesu ya amsa musu cewa Jehobah Allah neka�ai ya san daidai lokacin da �arshe zai zo. (Matta24:36) Amma Yesu ya fa�i abubuwa da za su faru a du-

1. A ina za mu iya sanin abin da ke zuwa a nan gaba?2, 3. Wace tambaya ce almajiran suka yi wa Yesu, kumayaya ya amsa?

BABI NA TARA

Muna Rayuwa ne a“Kwanaki na �arshe”?

Wa�anne abubuwa ne a zamaninmu akaannabta a Littafi Mai Tsarki?

Yaya Kalmar Allah ta ce mutane za su zama a“kwanaki na �arshe”?

Game da kwanaki na �arshe, wa�annekyawawan abubuwa ne Littafi Mai Tsarki ya

annabta game da zamaninmu?

niya kafin Mulkin ya kawo salama da kwanciyar hankalina �warai ga ’yan adam. Abin da ya fa�a yana faruwa ayanzu!

3 Kafin mu bincika tabbacin cewa muna rayuwa a “ci-kar zamani,” bari mu �an binciki ya�i da babu mutuminda ya gani. Ya�in ya faru ne a duniya marar ganuwa ta ru-hohi, kuma sakamakonsa ne yake shafanmu duka.

YA�I A SAMA4 Babi na baya na wannan littafin ya yi bayanin cewa

Yesu Kristi ya zama Sarki a samaniya a shekara ta 1914.(Daniel 7:13, 14) Ba da da�ewa ba bayan ya sami ikonMulki, Yesu ya �auki mataki. “Aka yi ya�i cikin sama,” inji Littafi Mai Tsarki. “Mika’ilu [wani suna na Yesu] da nasamala’iku suna fita su yi g

¯aba da dragon [Shai�an Iblis],

dragon kuma ya yi g¯aba da nasa mala’iku.”� Aka yi na-

sara a kan Shai�an da miyagun mala’ikunsa, wato aljanu,aka jefo su duniya daga sama. ’Ya’yan Allah na ruhu masuaminci suka yi farin ciki cewa Shai�an da aljanunsa sunbar sama. Amma mutane ba za su sami irin wannan farinciki ba. Maimakon haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kai-ton duniya . . . domin Shai�an ya sauko wajenku, hasalamai-girma kuwa gareshi, domin ya sani sauran zarafinsaka�an ne.”—Ru’ya ta Yohanna 12:7, 9, 12.

5 Don Allah ka lura da abin da ya faru a ya�in nan nasama. Cikin fushinsa, Shai�an zai haddasa kaito, kokuma masifa, ga wa�anda suke duniya. Kamar yadda zaku gani, a yanzu muna cikin lokaci ne na wannan kaito.Amma zai kasance marar tsawo sosai—‘zarafin ka�an

� Domin �arin bayani da ya nuna cewa Mika’ilu wani sunan YesuKristi ne, dubi Rataye, shafi na 218-219.

4, 5. (a) Menene ya faru a sama ba da da�ewa ba bayan an na�a YesuSarki? (b) In ji Ru’ya ta Yohanna 12:12, menene sakamakon ya�in nasama?

Muna Rayuwa ne a “Kwanaki na �arshe”? 87

ne.’ Shai�an kansa ya fahimci haka.Littafi Mai Tsarki yana kiran wannanlokaci “kwanaki na �arshe.” (2 Timo-thawus 3:1) Lalle ya kamata mu yifarin ciki cewa ba da da�ewa ba Al-lah zai kawar da rinjayar Iblis bisaduniya! Bari mu bincika abubuwa daaka fa�a a cikin Littafi Mai Tsarki dasuke faruwa a yanzu. Wa�annan suntabbatar da cewa muna kwanaki na�arshe kuma sun nuna cewa MulkinAllah ba da da�ewa ba zai kawomadawwamiyar albarka ga wa�andasuke �aunar Jehobah. Da farko, barimu bincika �angarori hu�u na ala-mun da Yesu ya ce za su kasance alokacin da muke rayuwa.

MUHIMMAN AUKUWA NAKWANAKI NA �ARSHE

6 “Al’umma za ta tasa ma al’um-ma, mulki kuma za ya tasa mamulki.” (Matta 24:7) An kashe miliyo-yin mutane a ya�e-ya�e na �arnin daya shige. Wani �an tarihin Britaniyaya rubuta: “An zubar da jini a �arnina 20 fiye da kowane a dukan rubu-taccen tarihi. . . . �arni da aka yi taya�i babu kama hannun yaro, sai daida ’yan gajerun lokatai da babu tsa-rarren ya�i awani wuri.” Rahoto dagaHukumar Sa wa Duniya Ido ya ce:

6, 7. Ta yaya kalmomin Yesu game da ya�i dayunwa suke cika a yau?

88

“Mutane da suka mutu a ya�i a �arni[na 20] sun yi ninki uku na muta-nen da suka mutu a dukan ya�e-ya�edaga �arni na fari A.Z., zuwa sheka-ra ta 1899.” Fiye da mutane miliyan100 suka mutu saboda ya�e-ya�e tundaga shekara ta 1914. Idan ma munsan ba�in cikin rashin wanda muke�auna a ya�i, sai dai mu ri�e bakiidan aka ninka wannan ba�in cikinsau miliyoyi.

7 “Za a yi yunwa.” (Matta 24:7) Bin-cike ya nuna cewa noman abinci ya�aru sosai a cikin shekaru 30 dasuke shige. Duk da haka, yunwa ta cigaba domin mutane da yawa ba suda isashen ku�in da za su sayi abin-ci ko kuma gonar da za su yi noma.A �asashe masu tasowa, fiye da mu-tane biliyan suna rayuwa ne bisadala guda ko kuma �asa da hakaa rana. Yawancin wa�annan sunawahala daga matsananciyar yunwa.Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya takimanta cewa yunwa ita ce kan gabawajen sanadin mutuwar yara fiye damiliyan biyar kowace shekara.

8 “Za a yi manyan rayerayen duni-ya.” (Luka 21:11) Bisa ga SashenBinciken �asa na Amirka, a kowa-ce shekara, ana sa ran cewa za a yi

8, 9. Menene ya nuna cewa annabcin Yesugame da raurawar �asa da annoba sun kasan-ce gaskiya?

89

matsakaicin girgizar �asa 19 a kowa-ce shekara. Suna da �arfin da za surushe gine-gine kuma su tsaga �asa.Kuma girgizar �asa da take da �ar-fin halaka gidaje gaba �aya tanafaruwa kowace shekara. Bayanan dake akwai sun nuna cewa girgizar�asa ta kashe miliyoyin mutane tundaga shekarar 1900. “Kuma mutu-war da ci gaba a fasaha ya rage, baitaka kara ya karya ba.”

9 “Za a yi . . . annoba.” (Luka 21:11)Duk da ci gaba a kimiyyar kiwon la-fiya, tsofaffin cututtuka da sababbisuna ci gaba da halaka mutane. Wanirahoto ya nuna cewa cututtuka 20—da suka ha�a da tarin fuka, zazza-bin cizon sauro, kwalara—sun �aru ashekarun baya bayan nan, kumawasu irin cututtuka suna da wuyarmagani. Kuma a�alla, sababbin cu-tuttuka talatin suka �ullo. Wa�ansunsu ba su da magani kuma suna kisa.

MUTANEN KWANAKI NA �ARSHE10 Ban da abubuwa da za su auku

a duniya, Littafi Mai Tsarki ya annab-ta cewa zamanin �arshe zai ga canjia zamanta kewa na mutane. ManzoBulus ya kwatanta yadda galibin mu-tane za su kasance. A 2 Timothawus3:1-5, mun karanta: “Cikin kwanaki

10. Wa�anne halaye da aka fa�a a 2 Timotihawus 3:1-5 kake gani a mutane a yau?

90

na �arshe miyagun zamanu za suzo.” Bulus ya ce mutane za su zama

ˇ masu sonkai

ˇ masu son ku�i

ˇ marasa bin iyayensu

ˇ marasa tsarki

ˇ marasa �auna

ˇ marasa kamewa

ˇ masu zafin hali

ˇ masu son annashuwa fiyeda son Allah

ˇ masu ri�e da surar ibada, ammasun musunci ikonta

11 Haka mutane suke a unguwar-ku? Hakika haka suke. Da mutane ako’ina da suke da mugayen hala-ye. Wannan ya nuna cewa ba dada�ewa ba Allah zai aikata, dominLittafi Mai Tsarki ya ce: “Lokacinda masu-mugunta suna tsiro kamarciyawa, sa’anda dukan masu-aikinmugunta suna yabanya: domin suhallaka ke nan har abada.”—Zabura92:7.

AUKUWA MASU KYAU!12 Hakika zamanin �arshe yana

11. Ta yaya Zabura 92:7 ta kwatanta abin dazai faru da miyagu?12, 13. Ta yaya “ilimi” ya �aru a “kwanakin�arshe”?

91

cike da kaito, kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya fa�a. Acikin wannan duniya da take cike da wahala, da akwaiabubuwa masu kyau da suka auku a tsakanin masu bautawa Jehobah.

13 “Ilimi kuma za ya �aru,” an annabta wannan a lit-tafin Daniel. A yaushe wannan zai faru? A “kwanakin�arshe.” (Daniel 12:4) Musamman tun shekara ta 1914,Jehobah ya taimaki wa�anda da gaske suke da muradinsu bauta masa suka �ara ilimin Littafi Mai Tsarki. Suka fa-himci gaskiya mai tamani game da sunan Allah da kumanufinsa, da kuma hadayar fansa ta Yesu Kristi, yanayinmatattu, da kuma tashin matattu. Bugu da �ari, bayin Je-hobah sun koyi yadda za su rayu a hanyar da za ta amfanesu kuma ta �aukaka Allah. Sun kuma fahimci matsa-yin Mulkin Allah da kuma yadda zai daidaita abubuwa aduniya. Menene suka yi da wannan ilimin? Wannan tam-bayar ta kawo mu ga wani annabci kuma da yake cika awannan zamanin �arshe.

14 “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azin-ta cikin iyakar duniya,” in ji Yesu Kristi a annabcinsa na“cikar zamani.” (Matta 24:3, 14) Miliyoyin Shaidun Je-hobah suna wa’azi na bisharar Mulki da �wazo a dukanduniya a fiye da �asashe 230 kuma a cikin fiye da harsu-na 400, suna sanar da Mulkin, abin da Mulkin zai yi, dakuma yadda za mu sami albarkarsa. Sun fito daga “Du-kan �abilai da al’ummai da harsuna.” (Ru’ya ta Yohanna7:9) Shaidun suna yin nazarin Littafi Mai Tsarki a gida damiliyoyin mutane wa�anda suke so su san abin da LittafiMai Tsarki ainihi yake koyarwa. Wannan cikar annabci cemai ban sha’awa, musamman ma tun da Yesu ya annab-ta cewa Kiristoci na gaskiya za su “zama abin �i”!—Luka21:17.

14. A ina ake yin wa’azin bisharar Mulki a yau, kuma su waye sukeyin wa’azin?

92 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

“Wannan bishara kuwata mulki za a yi wa’azintacikin iyakar duniya.”—Matta 24:14

MENENE ZA KA YI?15 Tun da annabce-annabce da yawa na Littafi Mai Tsar-

ki suna cika a yau, ba ka yarda ba cewa muna zamani na�arshe? Bayan an yi wa’azin bisharar yadda ya gamsar daJehobah, “matu�a” babu shakka za ta zo. (Matta 24:14)“Matu�a” tana nufin lokaci da Allah zai halaka miyagudaga duniya. Zai halaka dukan wa�anda suka yi hamayyada Shi da son rai, Jehobah zai yi amfani da Yesu da mala’i-ku. (2 Tassalunikawa 1:6-9) Shai�an da aljannunsa ba zasu sake yaudarar al’ummai ba. Bayan haka, Mulkin Allahzai zubo albarka ga dukan wa�anda suka mi�a kai ga sa-rautarsa ta adalci.—Ru’ya ta Yohanna 20:1-3; 21:3-5.

16 Tun da �arshen zamanin Shai�an ya yi kusa, munabukatar mu tambayi kanmu, ‘Menene ya kamata na cigaba da yi?’ Hikima ce mu ci gaba da koyo game da Je-hobah da kuma abin da yake bukata a gare mu. (Yohanna17:3) Ka kasance �alibin Littafi Mai Tsarki mai �wazo. Kasa yin hul�a a kai a kai da wa�anda suke yin nufin Jeho-bah ya zama maka jiki. (Ibraniyawa 10:24, 25) Ka nemiilimi da Jehobah Allah ya bayar ga mutane a dukan du-niya, kuma ka yi gyare-gyare da suka wajaba a rayuwarkasaboda ka more tagomashin Allah.—Ya�ub 4:8.

17 Yesu ya annabta cewa yawancin mutane za su yi wa-tsi da tabbacin cewa muna rayuwa a zamanin �arshe.Halakar miyagu za ta zo ba zato ba tsammani. Ka-mar �arawo cikin dare, za ta fa�a wa mutane ba zato.(1 Tassalunikawa 5:2) Yesu ya yi garga�i: “Kamar yaddakwanakin Nuhu su ke, hakanan kuma bayanuwar �anMutum za ta zama. Gama kamar yadda suna ci, suna

15. (a) Ka gaskata cewa muna rayuwa a zamanin �arshe, me ya sa?(b) Mecece “matu�a” take nufi ga wa�anda suka yi hamayya da Jeho-bah ga kuma wa�anda suka mi�a kai ga sarautar Mulkinsa?16. Menene zai kasance hikima a gare ka ka yi?17. Me ya sa halakar miyagu za ta fa�o wa yawancin mutane ba zato?

94 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

sha, suna aure, suna aurarwa a cikin kwanakin da ke ga-ban ruwan Rigyawa, har randa Nuhu ya shiga cikin jirgi,ba su sani ba har rigyawa ta zo ta kwashe su dukan; ha-kanan kuma bayanuwar �an mutum za ta zama.”—Matta 24:37-39.

18 Saboda haka, Yesu ya gaya wa wa�anda suke saura-ronsa: “Ku yi hankali da kanku, kada ya zama zukatankusu yi nauyi da zarin ci da maye da shagulgula na wan-nan rai, har ranan nan ta hume ku, ba labari, kamartarko: gama hakanan za ta humi dukan mazaunan fus-kar duniya duk. Amma a kowane loto sai ku yi tsaro, kunayin ro�o ku sami ikon da za ku tsere ma dukan wa�an-nan al’amuran da za su faru, ku tsaya [da yardar Allah]kuma a gaban �an mutum.” (Luka 21:34-36) Hikima ce a�auki maganar Yesu da muhimmanci. Me ya sa? Dominwa�anda suka sami yardar Jehobah Allah da kuma “�anmutum,” Yesu Kristi, suna da begen tsira daga �arshen za-manin Shai�an kuma su rayu har abada a cikin sabuwarduniya mai ban sha’awa da ta yi kusa sosai!—Yohanna3:16; 2 Bitrus 3:13.

18. Wane garga�i na Yesu ya kamata mu �auka da muhimmanci?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

ˇ Zamanin �arshe zai cika da ya�e-ya�e, dayunwa, da raurawar �asa, da kuma annoba.—Matta 24:7; Luka 21:11.

ˇ A zamanin �arshe, mutane da yawa za su sokansu, za su so ku�i, da kuma annashuwa,amma ba za su so Allah ba.—2 Timothawus 3:1-5.

ˇ A zamanin �arshe, za a yi wa’azin bishararMulki a dukan duniya.—Matta 24:14.

Muna Rayuwa ne a “Kwanaki na �arshe”? 95

SANIN mutum ya �unshi sanin wani abu game da iya-linsa. Hakazalika, sanin Jehobah Allah ya �unshi saniniyalinsa na mala’iku. Littafi Mai Tsarki ya kira mala’iku“’ya’yan Allah.” (Ayuba 38:7) To, menene matsayinsu anufin Allah? Suna da wani matsayi a tarihin mutanekuwa? Shin mala’iku suna shafan rayuwarka kuwa? Idanhaka ne, ta yaya?

2 Littafi Mai Tsarki ya yi maganar mala’iku sau �arurru-wa. Bari mu bincika ka�an daga cikin wa�annan dominmu �ara fahimtar mala’iku. Daga ina mala’iku suka fito?Kolossiyawa 1:16 ta ce: “A cikinsa [Yesu Kristi] aka halit-ta dukan abu, cikin sammai da bisa duniya kuma.” Sabodahaka, dukan halittu na ruhu da ake kira mala’iku, Jeho-bah Allah ne ya halicci kowannensu ta wajen �an farinsa.Mala’ikun su nawa ne? Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa anhalicci mala’iku miliyoyi barkatai, kuma dukansu suna daiko.—Zabura 103:20.�

� Game da mala’iku masu adalci, Ru’ya ta Yohanna 5:11 ta ce: “Ya-wansu fa zambar goma ajiye zambar goma ne, da kuma dubban dub-bai.” Saboda haka, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa an halicci miliyo-yin mala’iku.

1. Me ya sa za mu so mu koyi game da mala’iku?2. Daga ina mala’iku suka fito, kuma su nawa ne?

BABI NA GOMA

Halittun Ruhu—Yadda Suke Shafanmu

Shin mala’iku suna taimakon mutane ne?

Ta yaya miyagun ruhohi suka rinjayi mutane?

Muna bukatar mu ji tsoron miyagun ruhohi ne?

3 Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, ta gaya mana cewa,sa’ad da aka kafa duniya, “dukan ’ya’yan Allah kuwa sukayi sowa don farinciki.” (Ayuba 38:4-7) Saboda haka ma-la’iku sun wanzu da da�ewa kafin ma a halicci mutum,kai kafin ma a halicci duniya. Wannan sa�o na Littafi MaiTsarki ya nuna cewa mala’iku suna da motsin zuciya, do-min ya ce ‘suka yi sowa don farin ciki.’ Ka lura cewa ‘dukan’ya’yan Allahu’ suka yi murna tare. A wannan lokacin du-kanmala’iku suna cikin iyali guda mai ha�in kai mai bautawa Jehobah Allah.

TAIMAKO DA K¯ARIYA DAGA MALA’IKU

4 Tun da suka ga halittar mutane na fari, halittun ruhumasu aminci suna nuna �auna ga iyalin ’yan adam da take�aruwa da kuma cika nufin Allah. (Misalai 8:30, 31; 1 Bit-rus 1:11, 12) Amma, da shigewar lokaci, mala’iku sukalura cewa yawancin ’yan adam sun juya daga bautarMahaliccinsu mai �auna. Babu shakka cewa wannan yasa mala’ikun masu aminci ba�in ciki. Amma kuma, sa’adda mutum ya koma ga Jehobah, “akwai murna a wurinmala’ikun.” (Luka 15:10) Tun da mala’iku sun damu hakada mutane da suke bauta wa Allah, ba abin mamaki ba necewa Jehobah ya yi ta amfani da mala’ikun wajen �arfafabayinsa masu aminci a duniya da kuma kare su. (Ibraniya-wa 1:7, 14) Ga wasu misalai.

5 Mala’iku biyu suka taimaki mutumin nan mai aminciLutu da ’ya’yansa mata biyu su tsira daga halakar muga-yen biranan nan Saduma da Gwamrata ta wajen fitar da sudaga wannanwuri. (Farawa 19:15, 16) �arnuka bayan haka,aka jefa Daniel cikin kogon zakoki, amma ya ku�uta daga

3. Menene Ayuba 38:4-7 suka gaya mana game da mala’iku?4. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mala’iku masu aminci sunada marmari a ayyukan mutane?5. Wa�anne misalai muke da su a Littafi Mai Tsarki na taimako dagamala’iku?

Halittun Ruhu—Yadda Suke Shafanmu 97

bakinsu ya ce: “Allahna ya aiko mala’ikansa ya rufe bakinzakuna.” (Daniel 6:22) A �arni na farko A.Z., mala’ika yacece manzo Bitrus daga kurkuku. (Ayukan Manzanni 12:6-11) Bugu da �ari, mala’iku suka �arfafa Yesu a farkon hi-dimarsa a duniya. (Markus 1:13) Kuma sa’ad da Yesu yakedab da mutuwa, mala’ika ya bayyana masa kuma ya “�ar-fafa shi.” (Luka 22:43) Lalle wannan ya �arfafa Yesu awannan lokaci mai muhimmanci a rayuwarsa!

6 A yau, mala’iku ba sa bayyana wa mutanen Allah a du-niya. Ko da yake ba sa ganuwa ga idanunmutane, mala’ikunAllah har ila suna kare mutanensa, musamman ma dagadukan wani abin da yake da ha�ari a ruhaniya. Littafi MaiTsarki ya ce: “Mala’ikan Ubangiji yana kafa sansani a kewa-ye da masu-tsoronsa, yana tseradda su kuma.” (Zabura 34:7)Me ya sa wa�annan kalmomi ya kamata su zama abin �ar-fafa a gare mu? Dominda miyagunhalittun ruhu da suke sosu halaka mu! Su wanene su? Daga ina suka fito? Ta yayasuke so su yi mana lahani? Domin mu sami amsa, bari mubincika a ta�aice abin da ya faru a farkon tarihin mutane.

HALITTU NA RUHU DA ABOKAN GABANMU NE7 Kamar yadda muka koya daga Babi na 3 na wannan

littafin, �aya daga cikin mala’ikun ya yi muradin sarautabisa mutane saboda haka ya juya wa Allah baya. Daga bayaaka san wannan mala’ikan da suna Shai�an Iblis. (Ru’ya taYohanna 12:9) Bayan ya yaudari Hauwa’u, Shai�an ya yinasara wajen juya yawancin mutane daga Allah a �arni na16, ’yan ka�an kawai suka kasance da aminci, kamar su Ha-bila, Annuhu, da kuma Nuhu.—Ibraniyawa 11:4, 5, 7.

8 A zamanin Nuhu, wasu mala’iku suka yi wa Jehobah

6. (a) Ta yaya mala’iku suke ceton mutanen Allah a yau? (b) Wa�an-ne tambayoyi ne za mu bincika?7. Har yaya Shai�an ya yi nasara wajen juya mutane daga Allah?8. (a) Ta yaya wasu mala’iku suka zama aljanu? (b) Domin su tsiradaga ambaliya ta zamanin Nuhu, menene aljanun suka yi?

98 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

tawaye. Suka �yale matsayinsu daga iyalin Allah na sama-niya, suka sau�o duniya, suka �auki jiki irin na mutane.Me ya sa? Mun karanta a Farawa 6:2: “Sai ’ya’yan Allahsuka ga ’yan mata na mutane kyawawa ne; suka �aukowa kansu mata dukan wa�anda suka za�a.” Amma Jeho-bah Allah bai �yale irin wannan aiki na wa�annanmala’iku da kuma sakamakonsa na lalata mutane ya cigaba ba. Ya kawo ambaliya a duniya da ta share dukanmiyagun mutane kuma ya kare bayinsa masu aminci nekawai. (Farawa 7:17, 23) Saboda haka, mala’ikun da sukayi tawaye, ko kuma aljanu, aka tilasta musu barin jiki irinna mutane suka koma sama a halittar su ta ruhu. Sun

“Allahna ya aiko mala’ikansa,ya rufe bakin zakuna.”

—Daniel 6:22

Halittun Ruhu—Yadda Suke Shafanmu 99

goyi bayan Iblis, wanda ya zama “sarkin aljanu.”—Matta9:34.

9 Sa’ad da mala’iku marasa biyayya suka koma sama, anmai da su bare kamar sarkinsu, Shai�an. (2 Bitrus 2:4) Koda yake ba sa iya �aukan jikin mutane, har yanzu sunada mummunar rinjaya bisa mutane. Da taimakon wa�an-nan aljanu, Shai�an yana yaudarar “dukan duniya.” (Ru’yata Yohanna 12:9; 1 Yohanna 5:19) Ta yaya? Ainihi, aljanunsuna amfani da hanyoyin da suka tsara domin yaudararmutane. (2 Korinthiyawa 2:11) Bari mu bincika wasu cikinwa�annan hanyoyi.

YADDA ALJANU SUKE YAUDARA10 Domin su yaudari mutane, aljanu suna amfani da si-

hiri. Yin sihiri �ulla dangantaka ne da aljanu, ko kai tsayeko kuma ta hannun mutane. Littafi Mai Tsarki ya la’anci si-hiri kuma ya yi mana garga�i mu guji dukan wani abin dayake da ala�a da shi. (Galatiyawa 5:19-21) Sihiri yana yi waaljanu abin da �ugiya take yi wa masunci. Masunci yanaamfani da abubuwa da yawa a �ugiya domin ya kama ki-faye iri dabam dabam. Hakazalika, miyagun ruhohi sunaamfani da sihiri iri dabam dabam domin su rinjayi dukanire-iren mutane.

11 Wata irin �ugiya da aljanu suke amfani da ita ita ceduba. Mecece duba? �o�ari ne a san abin da zai faru a nangaba ko kuma wani abin sirri. Wasu ire-iren duba sun ha�ada hisabi, katin tarot, zuba wuri, duba da tafin hannu, kokuma neman alama cikin mafarki. Ko da yake mutane dayawa suna tsammanin duba ba wani abu ba ne mai lahani,Littafi Mai Tsarki ya nuna mana cewa duba da miyagun ru-hohi suna aiki tare. Alal misali, Ayukan Manzanni 16:16-18

9. (a) Menene ya faru da aljanun sa’ad da suka koma sama? (b) Me-nene za mu bincika game da aljanun?10. Menene sihiri?11. Menene duba, kuma me ya sa ya kamata mu guje shi?

100 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

sun ambaci “ruhu na duba” da ya sa yarinya take “duba.”Amma ta kasa duba sa’ad da aljanin ya fice daga gareta.

12 Wata hanya kuma da aljanu suke yaudarar muta-ne ita ce ta wajen �arfafa su su nemi taimakon matattu.Mutane da suke ba�in cikin rashin wanda suke �auna sauda yawa ana ru�in su da mugun ra’ayi game da wa�andasuka mutu. Boka zai ba da bayani na musamman ko kumaya yi magana da muryar da ta yi kama da ta mutuminda ya mutu. Saboda haka, mutane da yawa suka gaskatacewa matattu suna da rai da gaske, da cewa idan aka je garesu za su taimaki rayayyu su jimre ba�in cikinsu. Amma irinwannan “ta’aziyya” �arya ce kuma tana da ha�ari. Me yasa? Domin aljanu za su iya kwaikwayon muryar mamacinkuma su ba boka bayani game da mamacin. (1 Sama’ila 28:3-19) Bugu da �ari, kamar yadda muka gani a Babi na 6,matacce ba ya rayuwa kuma. (Zabura 115:17) Saboda hakadukan wanda ya yi “sha’ani da matattu” miyagun ruhohi

12. Me ya sa yake da ha�ari a yi �o�arin magana da matattu?

Aljanu suna amfani da hanyoyi da yawa su yaudari mutane

YADDA ZA ATSAYAYYA WA

MIYAGUN RUHOHI

ˇ Ka kawar da dukanabubuwan sihiri

ˇ Ka yi nazarin LittafiMai Tsarki

ˇ Ka yi addu’a gaAllah

sun ru�e shi kuma yana yin abin da ya sa�a wa nufin Al-lah. (Kubawar Shari’a 18:10, 11; Ishaya 8:19) Saboda haka,ka mai da hankali ka guji wannan mugun tarkon da aljanusuke amfani da shi.

13 Miyagun ruhohi suna tsorata mutane �ari ga yaudara.A yau, Shai�an da aljannunsa sun sani cewa ‘sauran zara-finsu ka�an ne’ kafin a halakar su, kuma yanzu fajircinsuya fi na da. (Ru’ya ta Yohanna 12:12, 17) Duk da haka,dubban mutane da a da suke rayuwa cikin tsoron irin wa-�annan miyagun ruhohi sun ’yantu. Ta yaya suka sami’yantuwa? Menene mutum zai iya yi idan ma yana sihiri?

YADDA ZA KA TSAYAYYA WA MIYAGUN RUHOHI14 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana yadda za mu tsayay-

ya wa miyagun ruhohi da kuma yadda za mu ’yantu dagagare su. Ka yi la’akari da misalin Kiristoci na �arni na far-ko a birnin Afisas. Wasunsu masu sihiri ne kafin su zamaKiristoci. Sa’ad da suka yanke shawarar cewa suna so su’yantu daga sihiri, menene suka yi? Littafi Mai Tsarki yace: “Wa�ansu kuwa ba ka�an ba daga masu-yin sihiri sukatattara littattafansu, suka �one su a gaban dukan mutane.”(Ayukan Manzanni 19:19) Ta wajen �ona littattafansu nasihiri, wa�annan sababbin Kiristoci sun kafa misali ga du-kan wa�anda suke so su yi tsayayya ga miyagun ruhohi ayau. Mutane da suke so su bauta wa Jehobah suna buka-tar su kawar da dukan wani abin da yake da ala�a da sihiri.Wa�annan za su ha�a da littattafai, mujallu, wasanni, kati,da kuma wa�o�i da suke �arfafa ayyukan sihiri kuma sukemasa ado. Sun ha�a har ila da layu da wasu abubuwa daake saka wa domin kariya daga aljannu.—1 Korinthiyawa10:21.

13. Menene mutane da yawa da d¯a suke tsoron aljanu suka yi?

14. Kamar Kiristoci na �arni na farko a Afisas, ta yaya za mu ’yantudaga miyagun ruhohi?

Halittun Ruhu—Yadda Suke Shafanmu 103

15 Bayan wasu shekaru da Kiristoci a Afisas suka halakalittattafansu na sihiri, manzo Bulus ya rubuta musu: ‘koku-warmu . . . da mugayen ruhohi ne.’ (Afisawa 6:12) Aljanunba su kasala ba. Sun yi �o�ari su yi nasara. To, menenewa�annan Kiristoci suke bukatar su yi? Bulus ya ce: “Mu-samman kuma, ku �auki garkuwa ta bangaskiya, waddaza ku iya �ice dukan jefejefe masu-wuta na Mugun [Shai-�an] da ita.” (Afisawa 6:16) Iyaka girman garkuwarmu naban gaskiya, haka iyaka tsayayyarmu ga miyagun ruhohizai kasance.—Matta 17:20.

16 Ta yaya za mu �arfafa bangaskiyarmu? Ta wajen yinnazarin Littafi Mai Tsarki. �arfin garu ya dangana ne a kanharsashinsa. Haka yake da bangaskiyarmu, �arfin bangas-kiyarmu ya dangana ne sosai a kan �arfin tushensa, watocikakken sani na Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki. Idanmuna karatu kuma muna nazarin Littafi Mai Tsarki kul-lum, bangaskiyarmu za ta yi �arfi. Kamar garu mai �arfi,haka wannan bangaskiyar za ta kare mu daga rinjayar mi-yagun ruhohi.—1 Yohanna 5:5.

17 Wa�anne matakai ne kuma wa�annan Kiristoci naAfisas suke bukatar su �auka? Suna bukatar �arin kari-ya domin suna zaune a birni da yake cike da shai�anci.Saboda haka Bulus ya gaya musu: “Kuna addu’a kowaneloto cikin Ruhu da kowace irin addua da ro�o.” (Afisawa6:18) Tun da mu ma muna rayuwa a duniya da ta cikada shai�anci, ro�on Jehobah domin taimako yana damuhimmanci �warai wajen tsayayya wa miyagun ruho-hi. Hakika, muna bukatar mu kira sunan Jehobah a cikinaddu’armu. (Misalai 18:10) Saboda haka, mu ci gaba daaddu’a ga Allah ya “cece mu daga Mugun,” Shai�an Iblis.

15. Domin mu tsayayya wa miyagun ruhohi, menene muke bukatarmu yi?16. Ta yaya za mu �arfafa bangaskiyarmu?17. Wane mataki yake da muhimmanci idan za mu tsayayya wa mi-yagun ruhohi?

104 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

(Matta 6:13) Jehobah zai amsa irin wannan addu’ar.—Za-bura 145:19.

18 Miyagun ruhohi suna da ha�ari, amma ba ma bukatarmu ji tsoronsu, idan muka tsayayya wa Iblis kuma mukakusaci Allah ta wajen yin nufinsa. (Ya�ub 4:7, 8) Ikon al-janun yana da iyaka. An yi musu horo a zamanin Nuhu,kuma za su fuskanci hukuncinsu na �arshe a nan gaba.(Yahuda 6) Ka tuna kuma cewa muna da kariyar mala’i-ku masu iko na Jehobah. (2 Sarakuna 6:15-17) Wa�annanmala’iku suna �aunar su ga mun yi nasara wajen tsayayyawa miyagun ruhohi. Kamar a ce mala’iku masu adalci sunayaba mana ne. Saboda haka mu kasance kusa da Jehobahda kuma iyalinsa na halittun ruhu masu aminci. Mu kumaguji dukan wani irin sihiri kuma a kullum mu bi garga�inKalmar Allah. (1 Bitrus 5:6, 7; 2 Bitrus 2:9) Sa’an nan za muyi nasara a kokawarmu da miyagun ruhohi.

19 Amma me ya sa Allah ya �yale miyagun ruhohi dakuma mugunta da ya jawo wa mutane wahala �warai? Za aamsa wannan tambayar a babi na gaba.

18, 19. (a) Me ya sa za mu tabbata cewa za mu yi nasara a kokawar-mu da miyagun ruhohi? (b) Wace tambaya ce za a amsa a babi nagaba?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

ˇ Mala’iku masu aminci suna taimakon wa-�anda suke bauta wa Jehobah.—Ibraniyawa 1:7, 14.

ˇ Shai�an da aljanunsa suna yaudarar mutanekuma su juya su daga Allah.—Ru’ya ta Yohan-na 12:9.

ˇ Idan ka yi nufin Allah kuma ka tsayayya waIblis, zai guje maka.—Ya�ub 4:7, 8.

Halittun Ruhu—Yadda Suke Shafanmu 105

BAYAN wani �azamin fa�a da aka yi a wata �asa da akeya�i, aka kashe dubban mutane farar hula, mata da yaraaka binne su a kabari guda aka saka alama. Alamar tana�auke da wannan rubutu: “Me ya sa?” Wani lokaci wan-nan ita ce tambaya mafi �una. Mutane suna yin ta daba�in ciki sa’ad da ya�i, annoba, cuta, ko kuma wani abumakamancin haka ya halakawani da suke �auna, koya ha-laka gidajensu, ko kuma ya jawo musu wahala a hanyoyidabam dabam. Suna so su san abin da ya sa irin wannanmasifa ta fa�a musu.

2 Me ya sa Allah ya �yale wahala? Idan Jehobah Allah yafi kowa iko, yana da �auna, yana da hikima, yana da adal-ci, me ya sa duniya take cike da �iyayya da rashin adalci?Ka ta�a yin irin wa�annan tambayoyin da kanka?

3 Ba daidai ba ne a tambayi abin da ya sa Allah ya �yalewahala? Wasu suna damuwa cewa yin irin wannan tam-bayar yana nufin cewa ba su da cikakkiyar bangaskiya ko

1, 2. Wace irin wahala mutane suke sha a yau, kuma wa�anne tam-bayoyi take sa mutane su yi?3, 4. (a) Me ya nuna cewa ba laifi ba ne a tambayi dalilin da ya saAllah ya �yale wahala? (b) Yaya Jehobah yake ji game da mugunta dakuma wahala?

BABI NA GOMA SHA �AYA

Me Ya Sa Allah Ya �yaleWahala?

Allah ne ya haddasa wahalar duniya?

Wane batu ne ya taso a gonar Adnin?

Ta yaya Allah zai magance wahalar’yan adam?

kuma sun rena Allah. Amma sa’ad da kake karatun LittafiMai Tsarki, za ka ga cewa mutane masu tsoron Allah masuaminci, sun yi irin wa�annan tambayoyin. Alal misali, an-nabi Habakkuk ya tambayi Jehobah: “Don me ka ke nunamini sa�o, ka sa ni in duba shiririta kuma? Gama �arnada mugunta suna gabana; akwai husuma, jayayya kuma tataso.”—Habakkuk 1:3.

4 Shin Jehobah ya tsawata wa annabi Habakuk maiaminci ne domin ya yi wa�annan tambayoyi? A’a. Maima-kon haka, Allah ya saka kalmomin Habakuk a cikin LittafiMai Tsarki. Allah ya taimake shi ya fahimci batun sosaikumaya kasance da bangaskiya mai �arfi. Jehobahyana sokai ma ka kasance haka. Ka tuna cewa Littafi Mai Tsarki yakoyar da cewa “yana kula da” kai. (1 Bitrus 5:7) Allah yana�in mugunta da kuma wahala fiye da dukanwani mutum.(Ishaya 55:8, 9) To, me ya sa akewahala haka da yawa a du-niya?

ME YA SA WAHALA TA YI YAWA?5 Mutanen addinai dabam dabam sun je ga

5. Wa�anne bayanai aka yi wa wasu game da dalilin wahala, ammamenene Littafi Mai Tsarki yake koyarwa?

Jehobah zai kawo �arshen dukan wahala

107

shugabannin addinansu da malamansu sun yi tambayame ya sa ake wahala haka da yawa. Sau da yawa, amsar daake bayarwa ita ce wahala nufin Allah ne, ya riga ya �ad-dara dukan abin da zai faru tun d

¯a har da masifu. An kuma

fa�awa mutane da yawa cewa al’amuran Allah ba a fahim-tarsu ko kuma shi yake haddasa mutuwar mutane—har data yara—saboda su kasance tare da shi a sama. Amma ka-mar yadda ka koya, Jehobah Allah ba ya yin mugun abu.Littafi Mai Tsarki ya ce: “Da�ai Allah shi yi mugunta! Mai-iko duka shi yi aikin sa�o!”—Ayuba 34:10.

6 Ka san abin da ya sa mutane suke yin kuskuren �orawa Allah alhakin dukan wahalar duniya? Yawanci, suna�ora wa Allah Mai Iko Duka laifi ne domin suna zaton shine ke mulkin wannan duniyar. Ba su san wata gaskiya maisau�i amma mai muhimmanci da Littafi Mai Tsarki yakekoyarwa ba. Ka koyi wannan gaskiyar a Babi na 3 na wan-nan littafi. Ainihin mai mulkin wannan duniyar Shai�anIblis ne.

7 Littafi Mai Tsarki ya fa�a a fili cewa: “Duniya dukakuwa tana kwance cikin Shai�an.” (1 Yohanna 5:19) Sa’adda ka yi tunani a kansa, wannan ba gaskiya ba ne? Wan-nan duniyar tana nuna irin hali ne na halittar ruhu mararganuwa “mai-ru�in dukan duniya.” (Ru’ya ta Yohanna12:9) Shai�an ma�iyi ne, mayaudari, ma�etacci. Shi ya saduniyar da take �ar�ashin ikonsa take cike da �iyayya, yau-dara, da �eta. Wannan dalili ne guda na abin da ya sa akewahala haka mai yawa.

8 Dalili na biyu game da abin da ya sa ake wahala shi nekamar yadda aka tattauna a Babi na 3, mutane ajizai ne

6. Me ya sa mutane suke yin kuskuren �ora wa Allah alhakin waha-lar duniya?7, 8. (a) Ta yaya duniya take nuna halin wanda yake sarautarta?(b) Ta yaya ajizancin mutane da kuma “sa’a, da tsautsayi” suka ba dagudummawa wajen jawo wahala?

108 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

kuma masu zunubi tun daga lokacin tawaye a gonar Ad-nin. Mutane masu zunubi suna kokawa domin iko, kumahaka yana jawo ya�e-ya�e, zalunci, da wahala. (Mai-Wa’azi4:1; 8:9) Dalilin wahala na uku shi ne cewa ‘sa’a, da tsau-tsayi, sukan sami kowannenmu.’ (Mai-Wa’azi 9:11 LittafiMai Tsarki) A duniya da ba Jehobah ba ne Sarkinta maik

¯are ta, mutane za su wahala domin sun kasance a wuri a

lokacin da bai dace ba.9 Abin farin ciki ne a gare mu mu fahimci cewa Allah ba

ya jawowahala. Ba shi ke da alhakin ya�e-ya�e, yin laifi, dakuma zalunci, har ma da annoba da suka haddasa waha-la ga mutane ba. Duk da haka, muna bukatar mu san, Meya sa Jehobah ya �yale wahala? Idan shi Mai Iko Duka ne,yana da ikon kawar da ita. To, me ya sa ya �yale ta? Allahmai �auna da muka zo ga fahimta dole ne ya kasance yanada kyakkyawan dalili.—1 Yohanna 4:8.

AN TA DA BATU MAI MUHIMMANCI10 Domin mu fahimci abin da ya sa Allah ya �yale waha-

la, muna bukatar mu tuna lokacin da wahala ta fara. Sa’adda Shai�an ya rinjayi Adamu da Hauwa’u su yi wa Jehobahrashin biyayya, wata tambaya mai muhimmanci ta taso.Shai�an bai �alubalanci ikon Jehobah ba. Shai�an kan-sa ya sani cewa ikon Jehobah ba shi da iyaka. Maimakonhaka, Shai�an ya �alubalanci dacewar sarautar Jehobah.Tawajen cewa Allah ma�aryaci ne wanda yake hana bayin-sa abin da ke mai kyau, Shai�an ya yi zargin cewa Jehobahmugun sarki ne. (Farawa 3:2-5) Shai�an yana cewa ne mu-tane za su fi jin da�i ba tare da Allah yana sarauta a kansuba. Wannan hari ne ga ikon mallaka na Jehobah, dacewarsarautarsa.

9. Me ya sa za mu tabbata cewa Jehobah yana da kyakkyawan dalilina �yale wahala ta ci gaba?10. Menene Shai�an ya �alubalanta, kuma ta yaya?

Me Ya Sa Allah Ya �yale Wahala? 109

11 Adamu da Hauwa’u sun yi wa Jehobah tawaye. Wato,cewa suka yi: ‘Ba ma son Jehobah ya yi Sarauta a kanmu.Za mu shawarta wa kanmu abin da ke nagarta da abin dake mugunta.’ Ta yaya Jehobah zai magance wannan batu?Ta yaya Jehobah zai koya wa dukan halittu masu tuna-ni cewa wa�annan ’yan tawaye sun yi kuskure, tafarkinsashi ne daidai? Wasu za su ce da Allah ya halaka wa�annan’yan tawaye kawai ya sake yinwasu. Amma Jehobahya rigaya fa�i nufinsa na cika duniya da ’ya’yan Adamu da Hau-wa’u, yana so su zauna a cikin aljanna a duniya. (Farawa1:28) Jehobah ko a yaushe yana cika nufinsa. (Ishaya 55:10, 11) Ban da haka ma, halaka ’yan tawayen a Adnin bazai warware batu da ta taso ba game da dacewar sarautarJehobah.

12 Bari mu dubi wani kwatanci. Alal misali, malamiyana koya wa �alibansa yadda za su magance wata matsa-la. Wani �alibi mai basira amma �an tawaye ya yi da’awar

11. Me ya sa Jehobah bai halaka ’yan tawayen ba kawai a Adnin?12, 13. Ka kwatanta abin da ya sa Jehobah ya �yale Shai�an ya zamamasaraucin wannan duniyar da kuma abin da ya sa Allah ya �yale mu-tane su mallaki kansu.

�alibin ya fi malamin �warewa ne?

cewa yadda malamin yake magance matsalar ba daidai bane. Wato, yana nufi ne cewa malamin bai �ware ba, wan-nan �an tawayen ya dage cewa ya san hanyar da ta fi kyauwajen magance matsalar. Wasu �alibai suka gaskata abinda ya ce, sai su ma suka yi tawaye. Menene malamin zaiyi? Idan ya kori ’yan tawayen daga aji, yaya hakan zai shafiwasu �alibai? Ba za su yi tunanin cewa �alibin da wa�andasuka ba shi goyon baya suna da gaskiya ba? Dukan sau-ran �alibai a ajin za su rena malamin, domin za su ce yanatsoron a fallasa shi. Amma idan malamin ya �yale �an ta-wayen ya nuna wa ajin yadda shi zai magance matsalar fa?

13 Jehobahya yi abin da ya kamanci abin da malamin yayi. Ka tuna cewa ’yan tawayen a Adnin ba su ka�ai ba ne.Wasu mala’iku miliyoyi suna kallo. (Ayuba 38:7; Daniel7:10) Yadda Jehobah ya magance wannan tawayen a �ar-she zai shafi dukan mala’iku da kuma halittu masu tunani.To, menene Jehobah ya yi? Ya �yale Shai�an ya nuna yad-da shi zai mallaki mutane. Allah kuma ya �yale mutane sumallaki kansu a �ar�ashin rinjayar Shai�an.

14 Malamin kwatancinmu ya sani cewa �an tawayen dakuma �aliban da suka ba shi goyon baya sun yi kuskure.Kuma ya sani cewa ba su lokaci su yi �o�ari su tabbatarda batunsu zai amfani dukan ajin. Sa’ad da ’yan tawayensuka gaza, dukan �aliban za su ga cewa malamin ne ka-�ai ya �ware ya koyar da ajin. Za su fahimci dalilin da yasa malamin ya kori duk wani �an tawaye daga ajin. Haka-zalika, Jehobah ya sani cewa dukan mutane masu zuciyarkirki da kuma mala’iku za su amfana da ganin cewa Shai-�an da ’yan tawaye masu goya masa baya sun gaza kumamutane ba za su iya mallakar kansu ba. Kamar yaddaIrmiya na zamanin d

¯a ya ce, za su fahimci wannan gaski-

yar: “Ya Ubangiji, na tabbata hanyar mutum ba cikin nasa

14. Wane amfani ne zai zo daga shawarar Jehobah ya �yale mutanesu mallaki kansu?

Me Ya Sa Allah Ya �yale Wahala? 111

hannu ta ke ba; mutum kuwa ba shi da iko shi shirya tafi-yarsa.”—Irmiya 10:23.

ME YA SA TA DA�E HAKA?15 Me ya sa Jehobah, ya �yale wahala ta da�e haka? Me

ya sa bai hana miyagun abubuwa daga faruwa ba? Ka yila’akari da abubuwa biyu da malami na kwantancinmu bazai yi ba. Da farko, ba zai hana �an tawayen ya ba da tab-bacinsa ba. Na biyu, malamin ba zai taimaki �an tawayenya gabatar da tabbacinsa ba. Hakazalika, ka yi la’akari daabubuwa biyu da Jehobah ya �uduri aniyar ba zai yi ba.Na farko, bai hana Shai�an da wa�anda suka ba shi goyonbaya daga �o�arin su tabbatar da cewa suna da gaskiya ba.Ba da lokaci ya wajaba. A shekaru dubbai na tarihin ’yanadam, ’yan adam sun ta�a salon sarauta dabam dabam, kokuma gwamnatin mutane. ’Yan adam sun sami ci gaba akimiyya da kuma wasu fannonin ilimi, amma rashin adal-ci, talauci, yin laifi, da kuma ya�i sun munanta. A yanzuan nuna cewa sarautar mutane ta gaza.

16 Na biyu, Jehobah bai taimaki Shai�an ya yi mulkinwannan duniyar ba. Alal misali, idan Allah ya hana muna-nan laifuffuka, hakan ba zai taimaka wa ’yan tawayen bane su tabbatar da batunsu? Ta haka Allah ba zai sa mutanesu yi tunanin cewa wata�ila ’yan adam za su iya mallakarkansu ba tare da sakamako mai ha�ari ba? Idan Jehobahya yi haka, zai kasance yana tarayya da ma�aryata. Amma“ba shi yiwuwa Allah ya yi �arya.”—Ibraniyawa 6:18.

17 To, yaya game da dukan lahanin da aka yi a wannandogon lokaci na tawaye ga Allah? Ya kamata mu tuna cewaJehobah shi ne Mai Iko Duka. Saboda haka, zai iya kumazai kawar da sakamakon wahalar ’yan adam. Kamar yad-

15, 16. (a) Me ya sa Jehobah ya �yale wahala ta da�e haka? (b) Meya sa Jehobah bai hana munanan laifuffuka faruwa ba?17, 18. Menene Jehobah zai yi game da dukan lahani da suka samudaga sarautar mutane da kuma rinjayar Shai�an?

112 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

da muka riga muka koya, za a gyara dukan wani lahanida aka yi wa duniyarmu sa’ad da aka mai da ita Aljanna.Za a kawar da sakamakon zunubi ta wajen ba da gaski-ya ga hadayar fansa ta Yesu, kuma sakamakon mutuwa tawajen tashin matattu. Ta haka Allah zai yi amfani da Yesu“halaka ayyukan Shai�an.” (1 Yohanna 3:8) Jehobah zaiyi dukan wa�annan a lokacin da ya dace. Ya kamata muyi godiya da bai yi wa�annan da wuri ba, domin ha�urin-sa ya ba mu zarafin mu fahimci gaskiya kuma mu bautamasa. (2 Bitrus 3:9, 10) A yanzu, Allah yana nemanwa�an-da suke so su bauta masa da gaske, kuma yana taimakonsusu jimre dukanwata wahala da za ta same su a wannan du-niya ta wahala.—Yohanna 4:23; 1 Korinthiyawa 10:13.

18 Wasu za su yi tunani, da ba a hana dukan wa�annanwahaloli faruwa ba, da Allah ya halicci Adamu da Hauwa’uyadda ba za su iya yin tawaye ba? Domin mu amsawannantambayar, kana bukatar ka tuna wata kyauta mai tamanida Allah ya ba ka.

YAYA ZA KA YI AMFANI DA KYAUTA DA ALLAH YA YI?19 Kamar yadda muka gani a Babi na 5, an halicci

’yan adam da ’yancin za�e. Ka fahimci muhim-mancinwannan kyautar? Allah ya yi dabbobimarasa iyaka, kuma wa�annan da ilhamisuke amfani. (Misalai 30:24) Mutane sun�era ’yar tsana da suka tsara ta bi dukanumurni. Da za mu yi farin ciki da Al-lah ya halicce mu haka? A’a, muna farin

19. Wace kyauta ce mai muhimmanci Jehobah ya bamu, kuma me ya sa za mu �au-ke shi da muhimmanci?

Allah zai taimakeka ka jimre wa wahala

Me Ya Sa Allah Ya �yale Wahala? 113

ciki da muke da ’yancin za�an irin mutane da muke so muzama, da kuma irin tafarkin rayuwa da za mu bi, irin abotada za mu �ulla, da dai sauransu. Muna �aunar mu kasan-ce da ’yanci, kuma abin da Allah yake so mu mora ke nan.

20 Jehobah ba ya son bauta da aka yi don dole. (2 Ko-rinthiyawa 9:7) Alal misali: Menene zai faranta wa iyayerai �warai—yaro ya ce “na gode” domin an gaya masa yafa�i haka, ko kuma wadda ya fa�a don kansa daga zuciyar-sa? To, tambayar ita ce, ta yaya za ka yi amfani da ’yancinza�in da Jehobah ya ba ka? Shai�an da kuma Adamu daHauwa’u sun yi mummunan amfani da shi. Suka �i Jeho-bah Allah. Menene za ka yi?

21 Ka nemi zarafi ka yi amfani da ’yancinka na za�e ahanyar da take da kyau. Za ka iya shiga tsakanin mutanemiliyoyi da suke goyon bayan Jehobah. Suna sa Allah ya yifarin ciki domin suna tabbatar da cewa Shai�an ma�arya-ci ne, wanda ya gaza wajen sarauta. (Misalai 27:11) Kai maza ka iya yin haka ta wajen za�an tafarki mai kyau na rayu-wa. Za a yi bayani game da wannan a babi na gaba.

20, 21. Ta yaya za mu yi amfani da kyautar ’yancin za�e a hanyar data dace, kuma me ya sa za mu so mu yi haka?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

ˇ Ba Allah ba ne yake haddasa mummunar ya-nayi na duniya.—Ayuba 34:10.

ˇ Ta wajen kiran Allah ma�aryaci da kumayana hana abin da ya dace ga wa�anda ke �ar-�ashinsa, Shai�an ya �alubalanci dacewarsarautar Jehobah.—Farawa 3:2-5.

ˇ Jehobah zai yi amfani da �ansa, Sarki Alma-sihu, ya kawo �arshen wahala kuma ya gyaralahanin da ta yi.—1 Yohanna 3:8.

114 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

WANE irin mutum za ka za�a ya zama abokinka? Wata�i-la za ka za�i mutumin da yake da irin ra’ayinka, yana sonirin abin da kake so, wanda yake da irin halinka. Kuma za kakusaci mutumin da yake da halayen kirki irinsu aminci daalheri.

2 A tarihi, Allah ya za�i wasu mutane su zama abokansa.Alal misali, Jehobah ya kira Ibrahim abokinsa. (Ishaya 41:8;Ya�ub 2:23) Allah ya kira Dauda “mutum gwalgwadon zu-ciyata” domin mutum ne da Jehobah yake �auna. (AyukanManzanni 13:22) Kuma Jehobah ya ce game da annabiDaniel “kai �aunatace ne �warai.”—Daniel 9:23.

3 Me ya sa Jehobah ya za�i Ibrahim, Dauda, da kumaDaniyel su zama abokanansa? Ya gaya wa Ibrahim: “Ka yibiyayya da maganata.” (Farawa 22:18) Saboda haka Jeho-bah yana kusantar wa�anda suka yi abin da ya gaya musucikin tawali’u. Ya gaya wa Isra’ilawa: “Ku kasa kunne gamuryata; ni kuma in zama Allahnku.” (Irmiya 7:23) Idan kayi wa Jehobah biyayya kai ma za ka zama abokinsa!

1, 2. Ka ba da misalin mutane da Jehobah ya za�a su zama aboka-nansa.3. Me ya sa Jehobah ya za�i wasu mutane su zama abokanansa?

BABI NA GOMA SHA BIYU

Rayuwa a Hanyar da TakeFaranta wa Allah Rai

Ta yaya za ka zama abokin Allah?

A wace hanya ce �alubalan Shai�an ya shafe ka?

Wa�anne irin halaye ne suke �ata wa Jehobah rai?

Ta yaya za ka rayu a hanyar da take farantawa Allah rai?

JEHOBAH YANA �ARFAFA ABOKANANSA4 Ka yi tunani game da abin da abota da Allah take nufi.

Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah yana neman zarafi don yanuna “bayyana kansa mai �arfi sabili da wa�anda zuciyarsuta kamalta gareshi.” (2 Labarbaru 16:9) Ta yaya Jehobah zainuna ikonsa a gare ka? An fito da hanya �aya a Zabura 32:8, a nan mun karanta: “[Ni Jehobah] ni koya maka cikin ta-farkin da za ka bi: da idona a kanka zan ba ka shawara.”

5 Hakika furci ne na �auna daga Jehobah! Zai yi maka ja-gora da kake bukata kuma ya kula da kai sa’ad da kakeamfani da su. Allah yana so ya taimake ka ka jimre gwa-ji kuma ka yi nasara. (Zabura 55:22) Saboda haka idan kabauta wa Jehobah da zuciya �aya, za ka kasance da tabbacikamar mai Zabura wanda ya ce: “Na sa Ubangiji a gabanatuttur: Da shi ke yana ga hannun damana ba zan jijjigu ba.”(Zabura 16:8; 63:8) Hakika, Jehobah zai taimake ka ka rayua hanyar da za ta faranta masa rai. Amma, kamar yadda kasani, Allah yana da abokin gaba da ba zai so ka yi haka ba.

�ALUBALAN DA SHAI�AN YA YI6 Babi na 11 na wannan littafin ya yi bayani game da

yadda Shai�an Iblis ya �alubalanci ikon mallaka na Allah.Shai�an ya zargi Allah da yin �arya kuma ya nuna cewa Je-hobah bai yi adalci ba da bai �yale Adamu da Hauwa’u suza�i wa kansu abin da ke nagarta da abin da ke muguntaba. Bayan da Adamu da Hauwa’u suka yi zunubi kuma du-niya ta fara cika da ’ya’yansu, Shai�anya �alubalanci dukan’yan adam. “Mutane ba sa bauta wa Allah domin suna �au-narsa,” in ji Shai�an. “Ka ba ni zarafi ka gani, zan sa kowaya juya maka baya.” Tarihin mutumin da aka kira Ayuba yanuna cewa abin da Shai�an ya gaskata ke nan. Wanene Ayu-ba, kuma ta yaya �alubalan da Shai�an ya yi ya shafe shi?

4, 5. Ta yaya Jehobah yake nuna ikonsa ga mutanensa?6. Wane zargi Shai�an ya yi wa ’yan adam?

116 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

7 Ayubaya rayu shekaru 3,600da suka shige. Mutumin kir-ki ne, domin Jehobah ya ce: “Babu mai-kama da shi cikinduniya, kamili ne,mutummai-adalci,mai tsoronAllah, yana�in mugunta.” (Ayuba 1:8) Ayuba ya faranta wa Allah rai.

8 Shai�anya zargi dalilin da ya sa Ayuba yake bautawa Al-lah. Iblis ya gaya wa Jehobah: “Ba ka kewaye shi da shingeba, da shi da gidansa, da dukan abin da ya ke da shi, a kowa-ne sassa? Ka albarkaci aikin hannuwansa, dabbobinsa sun�aru a �asa. Mi�a hannunka ka�ai yanzu, ka ta�a dukanabin da ya ke da shi, za ya la’anta ka a fuskarka!”—Ayuba 1:10, 11.

9 Saboda haka Shai�an ya ce Ayuba yana bauta wa Allahne saboda abin da yake samu. Iblis ya ce idan aka gwadaAyuba zai juyawa Allah baya. Yaya Jehobah ya amsa �aluba-lan da Shai�an ya yi? Tun da batun ya shafi dalilin bautarAyuba, Jehobah ya �yale Shai�an ya gwada Ayuba. Ta wan-nan hanyar, za a tabbatar da ko Ayuba yana �aunar Allah koba ya �aunarsa.

AN GWADA AYUBA10 Ba da da�ewa ba Shai�an ya gwada Ayuba ta hanyo-

yi da yawa. Na farko, aka sace wasu daga cikin dabbobinAyuba, aka kuma kashe wasu. Kuma an kashe yawancin ba-yinsa. Wannan ya karya masa arziki. Masifa ta sake fa�a waAyuba sa’ad da guguwa ta kashe ’ya’yansa goma. Duk dawa�annan masifu da suka faru, “Ayuba ba ya yi zunubi ba,ba ya kuwa sa�i Allah ba.”—Ayuba 1:22.

11 Shai�an bai gaji ba. Wata�ila ya yi tunanin cewa ko da

7, 8. (a) Me ya sa Ayuba ya yi fice a tsakanin mutane na zamaninsa?(b) Ta yaya Shai�an ya zargi dalilin da ya sa Ayuba yake bauta?9. Yaya Jehobah ya amsa �alubalan Shai�an, kuma me ya sa?10. Wa�anne gwaji ne suka fa�o wa Ayuba, kuma me ya yi?11. (a) Wane zargi na biyu Shai�an ya yi game da Ayuba, kuma tayaya Jehobah ya amsa? (b) Yaya Ayuba ya yi da cutarsa mai matsanan-ciyar zafi?

Rayuwa a Hanyar da Take Faranta wa Allah Rai 117

An ba wa Ayuba ladadomin tafarkinsa na aminci

yake Ayuba ya jimre wa hasarar dukiyarsa, rashin bayinsada ’ya’yansa, zai juya wa Allah baya idan ya yi ciwo. Jeho-bah ya �yale Shai�an ya harbi Ayuba da muguwar cuta maimatsananciyar zafi. Wannan ba zai sa Ayuba ya yi rashinbangaskiya ga Allah ba. Maimakon haka, ya ce da tabbaci:“Har in mutu ba ni rabuwa da gaskiyata.”—Ayuba 27:5.

12 Ayuba bai san cewa Shai�an ne dalilin masifarsa ba.Da yake ba shi da cikakken bayani game da �alubalan daIblis ya yi game da ikon mallaka na Jehobah, Ayuba yanazaton ko Allah ne ya sa masa masifa. (Ayuba 6:4; 16:11-14)Duk da haka, ya kasance da amincinsa ga Jehobah. Kumata wajen amincin Ayuba aka tabbatar da da’awar da Shai-�an ya yi wai Ayuba yana bauta wa Allah ne saboda sonkai, �arya ce!

13 Amincin Ayuba ya ba wa Jehobah dalilin ba da kyak-kyawar amsa ga �alubalantar ikon mallaka na Jehobah daShai�an ya yi. Babu shakka, Ayuba abokin Jehobah ne nagaskiya, kuma Allah ya ba shi lada domin tafarkinsa naaminci.—Ayuba 42:12-17.

YADDA YA SHAFE KA14 Wannan al’amari game da aminci ga Allah da Shai�an

ya yi zargi ba ga Ayuba ba ne kawai. Ya shafe ka. Wannanya bayana a fili a Misalai 27:11, inda Kalmar Jehobah ta ce:“�ana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata: domin in ma-yarda magana ga wanda ya zarge ni.” Wa�annan kalmomida aka rubuta shekaru da yawa bayan mutuwar Ayuba, sunnuna cewa Shai�an har yanzu yana s

¯ukan Allah kuma yana

zargin bayinsa. Idan muka yi rayuwa da take faranta wa Je-hobah rai, muna taimakawa ne wajen amsa zargin Shai�an,kuma a wannan hanyar muna faranta wa Allah rai. Yaya kaji game da wannan? Ba zai kasance da ban sha’awa ba idan

12. Ta yaya Ayuba ya mai da martani ga �alubalan Iblis?13. Menene ya faru domin Ayuba ya kasance da aminci ga Allah?14, 15. Me ya sa za mu ce �alubalan Shai�an ya shafi dukan mutane?

Rayuwa a Hanyar da Take Faranta wa Allah Rai 119

ka saka hannu wajen amsa da’awar Iblis, idan maya zaman-to kana bukatar ka yi wasu canji a rayuwarka?

15 Ka lura cewa Shai�an ya ce: ‘Dukan abin da mutum yake da shi, ya bayar a bakin ransa.’ (Ayuba 2:4) Da ya ce “mu-tum” Shai�an ya bayyana a fili cewa zarginsa ba ga Ayubaba ne kawai amma ga dukan mutane ne. Wannan al’amarine mai muhimmanci. Shai�an ya zargi amincinka ga Al-lah. Iblis zai so ya ga ka yi wa Allah rashin biyayya kuma kayi watsi da tafarkin adalci sa’ad da wahala ta samu. Ta yayaShai�an zai so ya yi haka?

16 Kamar yadda aka tattauna a Babi na 10, Shai�an yanaamfani da hanyoyi dabam dabam ya sa mutane su juyawa Allah baya. A wata hanyar yana fa�

¯a wa ne “kamar

zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya cin-ye.” (1 Bitrus 5:8) Ta haka, kana iya ganin rinjayar Shai�ansa’ad da abokane, ’yan’uwa, ko kuma wasu suka yi ha-mayya da �o�arinka ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki kumaka yi abin da ka koya.� (Yohanna 15:19, 20) A wani ge-fen kuma, Shai�an “ya kan mayarda kansa kamar mala’ikana haske.” (2 Korinthiyawa 11:14) Iblis yana iya yin amfanida dabara ya yaudare ka daga tafarkin rayuwa mai farantawa Allah rai. Zai iya kuma yin amfani da karaya, wata�ila yasa ka ji kai ba ka cancanta ka faranta wa Allah rai ba. (Mi-salai 24:10) Ko Shai�an ya kasance kamar “zaki mai-ruri”ko “kamar shi mala’ika na haske” ne, �alubalensa ya kasan-ce �aya ne: Ya ce sa’ad da ka fuskanci gwaji, ko jarabta, zaka bar bauta wa Allah. Ta yaya za ka amsa wannan �alubale

� Wannan ba ya nufin cewa wa�anda suka yi hamayya da kai Shai-�an ne yake rinjayarsu kai tsaye ba. Amma Shai�an shi ne allahn wan-nan zamanin, kuma dukan duniya tana cikin ikonsa. (2 Korinthiya-wa 4:4; 1 Yohanna 5:19) Saboda haka, rayuwa irin ta ibada ba za takasance abin da mutane suke so ba, kuma saboda haka wasu za su yihamayya da kai.

16. (a) Ta wa�anne hanyoyi ne Shai�an yake so ya juya mutane dagaAllah? (b) Ta yaya Iblis zai yi amfani da wa�annan salo a gareka?

120 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

kuma ka tabbatar da amincinka ga Allah, kamar yadda Ayu-ba ya yi?

YIN BIYAYYA GA UMURNIN JEHOBAH17 Za ka iya amsa �alubalen Shai�an ta wajen rayuwa da

take faranta wa Allah rai. Menene wannan ya �unsa? LittafiMai Tsarki ya amsa: “Kuma za ka �aunaci Ubangiji Allah-nkada dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan �arfinka.”(Kubawar Shari’a 6:5) Sa’ad da �aunarka ga Allah ta �aru, zaka cika da muradin ka yi abin da ya bukace ka da yi. “�aunarAllah ke nan, mu kiyaye dokokinsa,” in ji manzo Yohanna.Idan ka yi �aunar Jehobah da dukan zuciyarka, za ka ga cewa“dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba.”—1 Yohanna 5:3.

18 Meneneumurnin Jehobah?Wasu sunha�a dahalaye dadole ne mu guje wa. Alal misali, ka lura da akwatin da ke sha-fina 122, mai jigo “KaGujewaAbinda Jehobahya�i.”A nanza ka ga jerin halaye da Littafi Mai Tsarki ya haramta. A ga-nin farko, wasu halaye da aka jera ba za su kasance da wanilaifi ba. Amma idan ka yi bimbini a kan nassosi da aka rubu-ta, wata�ila ka ga hikimar dokar Jehobah. Yin canji a halinkazai kasance �alubale mafi girma da ka ta�a fuskanta. Duk dahaka, rayuwa a hanyar da take faranta wa Allah rai tana kawogamsuwa da kuma farin ciki. (Ishaya 48:17,18) Kuma abin daza ka iya yi ne. Ta yaya muka san haka?

19 Jehobah ba ya bukatar abin da ba za mu iya yi ba a garemu. (Kubawar Shari’a 30:11-14) Ya san abin da za mu iya daabin da ba za mu iya ba fiye da yadda muka sani. (Zabura103:14) Bugu da �ari, Jehobah zai iya ba mu �arfin da za muyi masa biyayya. Manzo Bulus ya rubuta: “Allah mai-amincine, da ba za ya bari a yi muku jarabawadda ta fi �arfinku ba;amma tare da jaraba za ya yi muku hanyar tsira, da za ku iya

17. Menene ainihin dalilin yin biyayya da dokokin Jehobah?18, 19. (a) Fa�i wasu cikin umurnin Jehobah. (Dubi akwati a shafina 122.) (b) Ta yaya muka sani cewa Allah ba ya bukatar abin da ya fi�arfinmu?

Rayuwa a Hanyar da Take Faranta wa Allah Rai 121

jimrewa.” (1 Korinthiyawa 10:13) Domin ya taimake ka kajimre, Jehobah zai iya ba ka “mafificin girman iko.” (2 Ko-rantiyawa 4:7) Bayan da ya jimre wa gwaji da yawa, Bulus yace: “Na iya yin abu duka a cikinwannan da ya ke �arfafata.”—Filibbiyawa 4:13.

KOYON HALAYE DA ALLAH YAKE SO20 Hakika, faranta wa Jehobah rai ya �unshi fiye da fa-

20. Wa�anne halaye ne da Allah yake so ya kamata ka koya, kuma meya sa wannan yake da muhimmanci?

KA GUJE WA ABIN DA JEHOBAH YA �I

Kisan Kai.—Fitowa 20:13; 21:22, 23.

Lalata.—Leviticus 20:10, 13,15, 16; Romawa 1:24, 26, 27, 32;1 Korinthiyawa 6:9, 10.

Sihiri.—Kubawar Shari’a 18:9-13; 1 Korinthiyawa 10:21, 22; Ga-latiyawa 5:20, 21.

Bautar Gumaka.—1 Korinthi-yawa 10:14.

Maye.—1 Korinthiyawa 5:11.

Sata.—Leviticus 6:2, 4; Afisawa4:28.

�arya.—Misalai 6:16, 19; Kolos-siyawa 3:9; Ru’ya ta Yohanna22:15.

Kwa�ayi.—1 Korinthiyawa 5:11.

Nuna �arfi.—Zabura 11:5; Mi-salai 22:24, 25; Malachi 2:16;Galatiyawa 5:20, 21.

�anyen Magana.—Leviticus 19:16; Afisawa 5:4;Kolossiyawa 3:8.

Amfani da Jini.—Farawa 9:4;Ayukan Manzanni 15:20, 28, 29.

�in Yi wa Iyali Tanadi.—1 Timothawus 5:8.

Saka hannu cikin ya�e-ya�eda hargitsin siyasa na wan-nan duniyar.—Ishaya 2:4;Yohanna 6:15; 17:16.

Shan taba ko kuma �wa-yoyi.—Markus 15:23; 2 Korinthi-yawa 7:1.

122 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

ranta masa rai kawai ta wajen guje wa abubuwa da ya�i. Kana bukatar kuma ka �aunaci abin da yake �auna.(Romawa 12:9) Kana kusantar wa�anda suke da irin ra’a-yinka, abin da kake so da kuma halayenka? Haka Jehobahma yake. Saboda haka ka koyi ka yi �aunar abin da Jeho-bah yake �auna. An kwatanta wasu cikin wa�annan aZabura 15:1-5, a nan mun karanta game da wa�anda Allahya �auke su abokanansa. Abokanan Jehobah suna nunaabin da Littafi Mai Tsarki ya kira “�iyan ruhu.” Wa�andasuka ha�a da “�auna, farinciki, salama, tsawon jimrewa,

Rayuwa a Hanyar da Take Faranta wa Allah Rai 123

nasiha, nagarta, aminci, tawali’u, kamewa.”—Galatiyawa5:22, 23.

21 Karatu da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki a kullum zaitaimake ka ka koyi halaye da Allah yake so. Koyon abin daAllah yake bukata zai taimake ka ka sa tunaninka ya jitu dana Allah. (Ishaya 30:20, 21) Da zarar ka �arfafa �aunarka gaJehobah, haka nan muradinka zai kasance na son ka faran-ta wa Allah rai.

22 Ana bukatar �o�ari domin a rayu a hanyar da take fa-ranta wa Jehobah rai. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta canzarayuwarka da yin watsi da hali na d

¯a da �aukan sabon hali.

(Kolossiyawa 3:9, 10) Amma game da umurnin Jehobah,mai zabura ya rubuta: “Cikin kiyaye su da lada mai-girma.”(Zabura 19:11) Kai ma za ka sami ladan rayuwa a hanyarda take faranta wa Allah rai. Ta wajen yin haka, za ka ba daamsa ga �alubalan da Shai�an ya yi kuma ka faranta wa Je-hobah rai!

21. Menene zai taimake ka ka koyi halaye da Allah yake so?22. Menene za ka cim ma idan ka rayu a hanyar da take faranta waAllah rai?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

ˇ Za ka zama abokin Allah ta wajen yi masa bi-yayya.—Ya�ub 2:23.

ˇ Shai�an ya �alubalanci amincin dukan muta-ne.—Ayuba 1:8, 10, 11; 2:4; Misalai 27:11.

ˇ Dole ne mu guje wa abubuwa da Allah ba yaso.—1 Korinthiyawa 6:9, 10.

ˇ Za mu faranta wa Jehobah rai ta wajen �inabin da ya �i da kuma �aunar abin da yake�auna.—Romawa 12:9.

124 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

“UBANGIJI shi ne Allah mai-gaskiya,” in ji annabi Ir-miya. “Allah mai-rai ne.” (Irmiya 10:10) Bugu da �ari,Jehobah Allah shi ne Mahaliccin dukan wani abu mairai. Mala’iku suka ce masa: “Kai ka halicci dukan abu,saboda nufinka kuma suka kasance, saboda nufinka akahalicce su.” (Ru’ya ta Yohanna 4:11) A cikin wa�ar yaboga Allah, Sarki Dauda ya ce: “A wurinka ma�ul�ular rai take.” (Zabura 36:9) Saboda haka, rai kyauta ne daga Allah.

2 Jehobah ne yake raya mu. (Ayukan Manzanni 17:28)Shi yake ba mu abincin da muke ci, da ruwan da mukesha, da kuma iskar da muke she�a, da kuma �asar damuke zama a kanta. (Ayukan Manzanni 14:15-17) Jeho-bah ya yi wannan a hanyar da ta sa rayuwa ta kasancemai armashi. Amma saboda mu more rayuwa da kyau,muna bukatar mu koyi dokokin Allah kuma mu yi musubiyayya.—Ishaya 48:17, 18.

KA DARAJA RAI3 Allah yana so mu daraja rai—ranmu da kuma rayukan

wasu. Alal misali, a zamanin Adamu da Hauwa’u, �ansuKayinu ya yi fushi matu�a da �aninsa Habila. Jehobah ya

1. Wanene ya halicci dukan abubuwa masu rai?2. Menene Jehobah ya yi domin ya raya mu?3. Yaya Allah ya �auki kashe Habila?

BABI NA GOMA SHA UKU

Ra’ayin Allah Game da Rai

Menene Ra’ayin Allah Game da rai?

Menene Ra’ayin Allah Game da zubar da ciki?

Ta yaya za mu nuna muna daraja rai?

MUNA DARAJA RAI

ˇ ta wajen �in kashe yaron

da ba a haifa ba tukuna

ˇ ta wajen daina�in mutane azuciyarmu

ˇ ta wajen dainamunanan halaye

yi wa Kayinu garga�i cewa fushinsa zai sa ya yi zunubimai tsanani. Kayinu ya yi banza da garga�in. Ya “tasa maHabila �anensa, ya kashe shi.” (Farawa 4:3-8) Jehobah yayi wa Kayinu horo domin ya kashe �an’uwansa.—Farawa4:9-11.

4 Bayan shekaru dubbai, Jehobah ya bai wa ’ya’yan Is-ra’ila dokoki domin su taimaka musu su bauta masayadda zai amince. Domin wa�annan dokoki an ba da suta hannun annabi Musa, wani lokaci ana kiransu DokarMusa. Dokar Musa �in ta ce: “Ba za ka yi kisankai ba.”(Kubawar Shari’a 5:17) Wannan ya nuna wa Isra’ilawacewa Allah yana daraja ran mutane kuma dole ne muta-ne su daraja rayukan wasu.

5 To, ran wanda ba a haifa ba fa? In ji Dokar Musa,haddasa mutuwar jariri a cikin uwarsa ba daidai bane. Hakika, har irin wannan ran yana da muhimmanciga Jehobah. (Fitowa 21:22, 23; Zabura 127:3) Wannan yanuna cewa zubar da ciki ba shi da kyau.

6 Daraja rai ya �unshi �aukan mutane yadda ya ka-mata. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Dukan wanda ya �i�an’uwansa mai-kisankai ne: kun sani babu mai-kisankaiwanda shi ke da rai na har abada cikinsa zaune.” (1 Yo-hanna 3:15) Idan muna son rai madawwami, munabukatar mu cire dukan wata �iyayyar wani da ke cikinzuciyarmu, domin �iyayya ita ce tushen yawancin mu-gunta. (1 Yohanna 3:11, 12) Yana da muhimmanci mukoyi mu yi �aunar juna.

7 To, yaya batun daraja namu ran? Galibi, mutane basa so su mutu, amma wasu suna �aukar kasada dominnisha�i. Alal misali, mutane da yawa suna shan taba, ko

4. A Dokar Musa, ta yaya Allah ya nanata yadda ya kamata a �auki rai?5. Yaya ya kamata mu �auki zubar da ciki?6. Me ya sa bai kamata mu �i wani ba?7. Wa�anne irin halaye ne ba sa daraja rai?

Ra’ayin Allah Game da Rai 127

su tauna ta, ko kuma su sha miyagun �wayoyi dominannashuwa. Irin wannan abubuwa suna iya yi wa jikilahani kuma sau da yawa suna kashe masu shansu. Mu-tumin da yake jarabar shan irin wa�annan abubuwa bai�auki rai da tsarki ba. Wa�annan halaye ba su da tsabtaa gaban Allah. (Romawa 6:19; 12:1; 2 Korinthiyawa 7:1)Domin mu bauta wa Allah yadda zai amince, dole nemu bar irin wa�annan halaye. Ko da yake yin haka zaiyi wuya, Jehobah zai yi mana taimako da muke bukata.Kuma yana yabon �o�arin da muke yi mu daraja ranmudomin kyauta ne mai muhimmanci daga wurinsa.

8 Idan muna daraja rai, za mu ri�a tuna cewa ya kama-ta mu mai da hankali. Ba za mu ri�a rayuwa ta ko ohoba kuma ba za mu �auki kasada ba domin nisha�i koannashuwa. Za mu guji mugun tu�i da kuma miya-gun wasanni. (Zabura 11:5) Dokar Allah ga Isra’ila tad

¯a ta ce: “Sa’anda ka gina sabon gida, sai ka ja dangar-

ma bisa beni, domin kada ka ja ma gidanka alhakin jini,idan wani ya fa�o daga can.” (Kubawar Shari’a 22:8) Ci-kin jituwa da mizanin da aka bayar a wannan dokar,ka tabbata cewa matakala na gidanka na sama suna gya-re domin kada santsi ya kwashi wani ya fa�i ya ji rauni.Idan kana da mota, ka tabbata cewa tu�a ta ba shi da ha-�ari. Kada ka �yale gidanka ko kuma motarka ta kasanceha�ari ga kanka da kuma wasu.

9 To, ran dabba fa? Wannan ma yana da daraja a wajenMahaliccinsa. Allah ya �yale kashe dabbobi domin abin-ci da kuma tufafi ko kuma domin a k

¯are mutane daga

ha�ari. (Farawa 3:21; 9:3; Fitowa 21:28) Amma, yi wadabbobi mugunta ko kuma kashe su kawai domin wasaba daidai ba ne kuma yana nuna matu�ar rashindaraja tsarkakar rai.—Misalai 12:10.

8. Me ya sa za mu ri�a tuna cewa ya kamata mu mai da hankali?9. Idan muna daraja rai, yaya za mu yi da dabbobi?

128 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

KA DARAJA JINI10 Bayan Kayinu ya kashe �an’uwansa Habila, Jehobah

ya gaya masa: “Muryar jinin �aninka ta yi �ara a wuri-na daga �asa.” (Farawa 4:10) Sa’ad da Allah ya yi maganagame da jinin Habila, yana magana ne game da ran Habi-la. Kayinu ya �auki ran Habila, yanzu za a hori Kayinu.Jinin Habila, ko kuma ransa yana kuka ne ga Jehobah yayi hukunci. An sake nuna nasaba da take tsakanin jinida rai bayan Ambaliya ta zamanin Nuhu. �afin Ambali-yar, mutane suna cin ’ya’yan itatuwa, da ganyaye. BayanAmbaliyar, Jehobah ya gaya wa Nuhu da kuma ’ya’yansa:“Kowane abu mai-motsi wanda ya ke da rai, za ya zamaabincinku; kamar ganye duk na ba ku su.” Amma, Allahya yi wannan hanin: “Sai dai nama tare da ransa, wataujininsa ke nan, wannan ba za ku ci ba.” (Farawa 1:29; 9:3, 4) A bayyane yake, Jehobah ya nuna nasaba da ke tsa-kanin rai da jinin halitta.

11 Muna daraja jini ta wajen �in cinsa. A cikin Dokar daJehobah ya ba wa Isra’ilawa, ya ba da wannan umurni:“Kuma kowane mutum . . . wanda yana farauta ya kamakowane nama, ko tsuntsu, halal ga ci; sai shi zubarda ji-ninsa, shi rufe da �ura. . . . Domin wannan na ce ma’ya’yan Isra’ila, Ba za ku ci jini na kowane irin nama”ba. (Leviticus 17:13, 14) Allah ya ba Nuhu umurnin kadaa ci jini, shekaru 800 da farko, har yanzu ya kamata mubi umurnin. Yadda Jehobah ya �auki wannan a bayyaneyake sarai: Bayinsa za su iya cin naman dabba amma bajininsa ba. Za su zub da jinin a �asa—wato, suna mai daran halittar ga Allah.

12 Umurni makamancin wannan yana kan Kiristoci.

10. Ta yaya Allah ya nuna cewa da nasaba tsakanin rai da jini?11. Menene Jehobah ya hana a yi da jini tun daga zamanin Nuhu?12. Wace doka game da jini ruhu mai tsarki ya bayar a �arni na far-ko kuma yake ci gaba har zuwa yau?

Ra’ayin Allah Game da Rai 129

Manzanni da kuma dattawa da suke ja-gora a tsakaninmabiyan Yesu a �arni na farko suka taru suka yanke sha-warar doka da dukan ikilisiyar Kirista za ta bi. Ga abinda suka ce: “Ya yi kyau ga Ruhu Mai-tsarki, da mu kuma,kada mu nawaita muku wani abu gaba da wa�annan wa-jibai; ku hanu daga abin aka mi�a ma gumaka, da jinikuma, da abin da aka ma�are [barin jini cikin nama],da fasikanci.” (Ayukan Manzanni 15:28, 29) Saboda hakadole ne mu guji ‘jini.’ A idanun Allah, yin haka mu-himmancinsa �aya ne da guje wa bautar gunki da kumalalata.

13 Shin umurnin mu guji jini ya ha�a ne da kar�ar �a-rin jini? E. Alal misali, a ce Likita ya hana ka shan giya.Wannan yana nufin kada ka sha amma kana iya saka taa jikinka ta jijiyoyinka ne? A’a! Hakazalika, guje wa jiniyana nufin kada mu saka shi a jikinmu sam. Saboda hakaumurnin mu guje wa jini yana nufin cewa kada mu �ya-le kowa ya saka mana jini ta cikin jijiyoyinmu.

14 Idan Kirista ya ji mugun rauni ko kuma yana bukatarfi�a fa? A ce likitoci sun ce dole ne a �ara masa jini idanba haka ba zai mutu. Hakika, Kirista ba zai so ya mutuba. Domin �o�arinsa ya k

¯are kyauta mai muhimmanci ta

rai daga Allah, zai yarda da wasu fannonin magani da basu �unshi jini ba. Saboda haka, zai iya neman irin wan-nan magani idan wannan yana samuwa kuma zai yardada wasu hanyoyin magani da ba su �unshi jini ba.

15 Ya kamata ne Kirista ya taka dokar Allah domin ya�an �ara tsawon rayuwarsa a wannan zamanin? Yesu yace: “Dukan wanda ya ke nufi shi ceci ransa, �adda ran-sa shi ya ke yi: kuma dukan wanda ya ke �adda ransa

13. Ka ba da misalin abin da ya sa guje wa jini ya ha�a da guje wa �a-rin jini.14, 15. Idan likitoci suka ce za su �ara wa Kirista jini, me ya kamataya yi kuma me ya sa?

130 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

sabili da ni, samunsa ya ke yi.” (Mat-ta 16:25) Ba ma so mu mutu. Ammaidan muna so mu yi tattalin ran-mu ta wajen taka dokar Allah, zamu shiga ha�arin rasa rai madawwa-mi. Muna masu hikima, mu dogaraga adalcin dokar Allah, da cikakkentabbacin cewa idan muka mutu do-min wani abu, Wanda Ya Ba Mu Raizai tuna da mu a lokacin tashin ma-tattu kuma ya sake ba mu kyauta maitamani na rai.—Yohanna 5:28, 29; Ib-raniyawa 11:6.

16 A yau, bayin Allah masu amincisuna da niyyar bin umurninsa gameda jini. Ba za su ci jini ba ta kowa-ce hanya. Kuma ba za su kar�i jini badomin magani.� Sun tabbata cewaMahaliccin jini ya san abin da ya fikyau a gare su. Ka gaskata haka?

HANYAR DA TA DACE KAWAINA AMFANI DA JINI

17 Dokar Musa ta nanata hanyar data dace na amfani da Jini. Game da bauta da ake buka-ta daga Isra’ilawa na d

¯a Jehobah ya ba da umurni: “Ran

nama yana cikin jini: na kuwa ba ku shi bisa bagadi do-min a yi kafarar rayukanku: gama jini ne ke yin kafara

� Domin �arin bayani game da wasu hanyoyin magani maimakon�arin jini, ka dubi shafuffuka 13-17 na mujallar nan How Can BloodSave Your Life? (Ta Yaya Jini Zai Ceci Ranka?) da Shaidun Jehobah sukawallafa.

16. Menene bayin Allah suke da niyyar yi game da jini?17. A Isra’ila ta d

¯a, wace hanyar amfani da jini Jehobah Allah ya amin-

ce da ita?

Idan likitan ka yace kada ka sha giya,

za ka yarda a sakane a jikin ka ta

jijiyoyinka?

Ra’ayin Allah Game Da Rai

saboda rai.” (Leviticus 17:11) Sa’ad da Isra’ilawa suka yizunubi, za su sami gafara ta wajen mi�a dabba kuma azuba ka�an cikin jininsa a kan bagade a mazauni kokuma daga baya a haikalin Allah. Hanyar da ta dace naamfani da jini ita ce irin wa�annan hadayun.

18 Kiristoci na gaskiya ba sa �ar�ashin Dokar Musakuma saboda haka ba sa ba da hadaya ta dabbobi su zubajinin dabba a kan bagadi. (Ibraniyawa 10:1) Amma, am-fani da jini a kan bagadi a zamanin Isra’ila ta d

¯a yana

nuni da hadaya na �arshe mafi tamani—na �an Allah,Yesu Kristi. Kamar yadda muka koya a Babi na 5 na wan-nan littafi, Yesu ya ba da ransa na mutum ya �yale azubar da jininsa wajen hadaya. Sa’ad da ya haura zuwa

18. Wane amfani da albarka za mu iya samu daga jinin Yesu da akazubar?

Ta yaya za ka daraja rai da kuma jini?

132 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

sama kuma sau �aya tak ba �ari ya mi�a tamanin jininsada aka zubar ga Allah. (Ibraniyawa 9:11, 12) Wannan yaba da dalilin gafarta zunubai kuma ya bu�e mana han-yar samun rai madawwami. (Matta 20:28; Yohanna 3:16)Wannan amfani da jini ya kasance mai matu�ar muhim-manci! (1 Bitrus 1:18, 19) Sai ta wajen bangaskiya gajinin Yesu da ya zubar za mu sami tsira.

19 Ya kamata mu yi wa Jehobah Allah godiya dominya yi mana tanadin rai cikin �auna! Kuma hakan bai ka-mata ba ne ya motsa mu mu gaya wa mutane gameda zarafin samun rai madawwami daga bangaskiya gahadaya ta Yesu? Damuwa ta ibada na rayukan ’yan’uwamutane za ta motsa mu mu yi haka da �wazo da kumahimma. (Ezekiel 3:17-21) Idan muka sau�e wannan hak-kin yadda ya dace, za mu iya cewa kamar yadda manzoBulus ya ce: “Ni ku�utace ne daga jinin dukan mutane.Gama ban ji nauyin bayyana muku dukan shawarar Al-lah.” (Ayukan Manzanni 20:26, 27) Gaya wa mutanegame da Allah da kuma nufinsa ita ce hanya mafi kyauda ya nuna cewa muna daraja rai da jini �warai da gaske.

19. Dole ne mu yi menene domin mu ‘ku�uta daga jinin dukan mu-tane’?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

ˇ Rai kyauta ne daga Allah.—Zabura 36:9;Ru’ya ta Yohanna 4:11.

ˇ Zubar da ciki ba daidai ba ne, tun da ran �anda ba a haifa ba yana da muhimmanci a idonAllah.—Fitowa 21:22, 23; Zabura 127:3.

ˇ Muna daraja rai ta wajen guje wa �aukar ka-sada da kuma cin jini.—Kubawar Shari’a 5:17;Ayukan Manzanni 15:28, 29.

Ra’ayin Allah Game da Rai 133

JEHOBAH ALLAH yana so rayuwar iyalinka ta kasance maifarin ciki. Kalmarsa Littafi MaiTsarki ta ba da sharu�a ga ko-wane mutum cikin iyali, ta kwatanta hakkin da Allah yakeso kowa ya cika. Sa’ad da kowa ya sau�e hakkinsa cikin ji-tuwa da umurnan Allah, sakamakon suna gamsarwa. Yesuya ce: “Gwamma dai wa�annan da suna jin maganar Allah,suna kiyaye ta kuma.”—Luka 11:28.

2 Farin cikin iyali ya dangana bisa fahimtar Jehobah netushen iyali, shi ne kuma Yesu ya kira “Ubanmu.” (Matta6:9) Dukan wata iyali a duniya ta kasance ne domin Uban-mu na sama—kuma hakika ya san abin da yake sa iyali farinciki. (Afisawa 3:14, 15) To, menene Littafi Mai Tsarki yakekoyarwa game da hakkin kowa cikin iyali?

ALLAH NE YA TSARA IYALI3 Jehobah ya halicci mutane na farko, Adamu da Hau-

1. Menene zai sa rayuwar iyali ta zama mai farin cikin?2. Farin ciki na iyali ya dangana ne bisa fahimtar menene?3. Yaya Littafi Mai Tsarki ya kwatanta farkon iyali, kuma ta yaya mukasani cewa hakan gaskiya ne?

BABI NA GOMA SHA HU�U

Yadda Za Ka Sa RayuwarIyalinka ta Zama Mai Farin Ciki

Menene ake bukata domin mutum yazama mijin kirki?

Ta yaya mace za ta yi nasara wajen cikaaikinta na matar aure?

Menene kasancewa iyayen kirki ya �unsa?

Ta yaya yara za su taimaka wajen sa rayuwariyali ta zama mai farin ciki?

wa’u, ya ha�a su suka zama mata da miji. Ya saka su a ci-kin aljanna a duniya—gonar Adnin—kuma ya gaya musu suhaifi ’ya’ya. “Ku yalwata da ’ya’ya, ku ri�u, ku mamaye du-niya,” in ji Jehobah. (Farawa 1:26-28; 2:18, 21-24) Wannanba labari ba ne ko kuma �age, domin Yesu ya nuna cewaabin da Farawa ta ce game da farkon iyali gaskiya ne. (Mat-ta 19:4, 5) Ko da yake muna fuskantar matsaloli masu yawaa rayuwa, ba haka Allah ya nufa ba, bari mu ga yadda farinciki zai iya kasancewa a cikin iyali.

4 Kowa cikin iyali zai iya sa rayuwar iyalin ta kasancemai farin ciki ta wajen yin koyi da Allah wajen nuna �au-na. (Afisawa 5:1, 2) Amma, ta yaya za mu yi koyi da Allah,tun da ba ma iya ganin shi? Za mu iya koyo game da yad-da Jehobah yake abubuwa domin ya aiko da �ansa na faridaga sama zuwa duniya. (Yohanna 1:14, 18) Sa’ad da yakeduniya, wannan �a, Yesu Kristi, ya yi koyi da Ubansa nasamaniya sosai da ganinsa da saurarensa tamkar kasancewada Jehobah ne da kuma saurarensa. (Yohanna 14:9) Sabodahaka, koyo game da �auna da Yesu ya nuna da kuma yinkoyi da misalinsa, kowannenmu zai iya taimaka wa wajensa rayuwar iyali ta zama mai farin ciki.

MISALI GA MAZA5 Littafi Mai Tsarki ya ce ya kamata namiji ya bi da ma-

tarsa kamar yadda Yesu ya bi da almajiransa. Ka yi la’akarida wannan umurni na Littafi Mai Tsarki: ‘Ku mazaje, ku�aunaci matanku, kamar yadda Kristi kuma ya �aunaci ikili-siya, ya bada kansa dominta; . . . Hakanan ya kamata mazajekuma su yi �aunar matayensu kamar jikunansu. Wanda yake �aunar matatasa kansa ya ke �auna: gama babu mutum

4. (a) Ta yaya kowa cikin iyali zai iya taimaka wajen sa iyali farin ciki?(b) Me ya sa yin nazarin rayuwar Yesu yana da muhimmanci wajen saiyali farin ciki?5, 6. (a) Ta yaya yadda Yesu ya bi da ikilisiya ya kafa misali ga maza?(b) Menene dole ne a yi domin a sami gafara daga zunubi?

Yadda Za Ka Sa Rayuwar Iyalinka ta Zama Mai Farin Ciki 135

wanda ya ta�a �in jiki nasa; amma ya kan ciyadda shi yakan kiyaye shi, kamar yadda Kristi kuma ya kan yi da ikilisi-ya.’—Afisawa 5:23, 25-29.

6 �aunar Yesu ga ikilisiyar mabiyansa ya kafa misali maikyau ga maza. Yesu “ya �aunace su har matu�a,” ya sa-daukar da ransa dominsu, ko da yake ba kamiltattu bane. (Yohanna 13:1; 15:13) Haka nan, aka aririci maza: ‘Kuyi �aunar matayenku, kada kuwa ku yi fushi da su.’ (Ko-lossiyawa 3:19) Menene zai taimaki namiji ya bi wannangarga�i, musamman ma a lokacin da matarsa ta yi kuskure?Ya kamata ya tuna da na shi kuskure da kuma abin da dolene ya yi dominya sami gafara daga Allah. Menene wannan?Dole ne ya gafarta wa wa�anda suka yi masa laifi kumawannan ya ha�a da matarsa. Hakika, ita ma ya kamata ta yihaka nan. (Matta 6:12, 14, 15) Ka ga abin da ya sa wasu sukace aure mai nasara, auren mutane ne biyu masu yin gafara?

7 Ya kamata kuma maza su lura cewa a kullum Yesu yananuna sanin ya kamata ga almajiransa. Yana yin la’akari dagazawarsu da kuma bukatunsu na zahiri. Alal misali, sa’adda suka gaji, ya ce: “Ku zo da kanku waje �aya inda ba kowa,ku huta ka�an.” (Markus 6:30-32) Mata ma suna bukatara nuna musu sanin ya kamata. Littafi Mai Tsarki ya kwa-tanta su a matsayin wa�anda suka fi “rashin �arfi” kuma yaumurci maza su ri�a ba su “girma.” Me ya sa? Domin mazada mata “masu-tarayyan gado na alherin rai” ne. (1 Bitrus3:7) Maza ya kamata su tuna cewa aminci, ba jinsi ba, kesa mutum ya kasance da martaba a gaban Allah.—Zabura101:6.

8 Littafi Mai Tsarki ya ce mijin da “ya ke �aunar matata-sa kansa ya ke �auna.” Wannan haka yake domin mutumda matarsa ‘su ba biyu ba ne, amma nama �aya ne,’ ka-

7. Menene Yesu ya yi la’akari da shi, kuma wane misali ne ya kafa gamaza?8. (a) Ta yaya ne namijin da ya �aunaci matarsa, “kansa ya ke �au-na”? (b) Menene kasancewa “nama �aya” yake nufi ga mata da miji?

136 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

mar yadda Yesu ya nuna. (Matta 19:6) Saboda haka dole nesu tsaya wa juna a batun jima’i. (Misalai 5:15-21; Ibraniya-wa 13:4) Za su iya yin haka idan suka nuna damuwa mararson kai ga bukatar juna. (1 Korinthiyawa 7:3-5) Abin lurane wannan tunasarwa: ‘Babu mutum wanda ya ta�a �injiki nasa; amma ya kan ciyadda shi ya kan kiyaye shi.’ Mazasuna bukatar su �aunaci matansu kamar yadda suke �aunarkansu, suna kuma tuna cewa za su ba da lissafi ga nasu, shu-gaba, Yesu Kristi.—Afisawa 5:29; 1 Korantiyawa 11:3.

9 Manzo Bulus ya yi maganar “�aunar da Almasihu Yesuke yi.” (Filibbiyawa 1:8 Littafi Mai Tsarki) �aunar Yesu haline mai da�a�awa, wadda mata da suka zama almajiransasuke so. (Yohanna 20:1, 11-13, 16) Dukan mata suna buka-tar �aunar mazansu.

MISALI GA MATA10 Iyali �ungiya ce, kuma domin ta yi tafiya daidai,

tana bukatar shugaba. Yesu ma yana da Shugaban da yakemi�a wa kai. “Kan Kristi kuma Allah ne,” yadda “kan macekuma namiji ne.” (1 Korinthiyawa 11:3) Yadda Yesu yakemi�a wa Shugabancin Allah kai misali ne mai kyau, tun dadukanmu muna da shugaban da muke mi�a wa kai.

11 Mutane ajizai suna yin kuskure kuma sau da yawa sunagaza kasance shugabannin iyali da suka dace. Saboda haka,menene mace ya kamata ta yi? Kada ta raina abin da mijintaya yi, ko kuma ta yi �o�arin �wace shugabancinsa. Ya kama-ta mace ta tuna cewa a idanun Allah, tawali’u da natsuwa,wa�annan abubuwa ne masu martaba a gun Allah. (1 Bit-rus 3:4) Ta wajen nuna irin wannan hali, zai kasance dasau�i a gare ta ta mi�a kai irin na ibada, har a lokaci masu

9. Wane hali ne na Yesu aka ambata a Filibbiyawa 1:8, kuma me yasa ya kamata maza su nuna wannan hali ga matansu?10. Ta yaya Yesu ya ba da misali ga mata?11. Wane irin hali ya kama mata ta nuna wa mijinta, kuma menenezai kasance sakamakon halinta?

Yadda Za Ka Sa Rayuwar Iyalinka ta Zama Mai Farin Ciki 137

wuya. Bugu da �ari, Littafi MaiTsarki ya ce: “Matan kuma taga kwarjinin mijinta.” (Afisawa 5:33) Amma idan bai kar�iYesu a zaman Shugabansa ba fa? Littafi Mai Tsarki ya ariricimata: ‘Ku yi zaman biyayya ga mazaje naku; domin ko daakwai wa�ansu da ba su yin biyayya da magana, su rinjayubanda magana saboda halayen matansu; suna lura da hala-yenku masu-tsabta tare da tsoro.’—1 Bitrus 3:1, 2.

12 Ko mijin mai bi ne ko a’a, ba raini ba ne mace ta fa�ira’ayinta da ya bambanta da na shi cikin ladabi. Ra’ayintazai iya kasance daidai, kuma dukan iyalin za su amfana idanya saurare ta. Ko da yake Ibrahim bai yarda da ra’ayin ma-tarsa Saratu ba sa’ad da ta ba da shawarar abin da za a yi amagance wata matsala na iyali, Allah ya gaya masa: “Ka jimaganarta.” (Farawa 21:9-12) Hakika, sa’ad da mijin ya yan-ke shawarar da ba ta sa�a wa dokar Allah ba, matarsa za tanuna mi�a kanta tawajen taimaka masa.—Ayukan Manzan-ni 5:29; Afisawa 5:24.

13 A wajen cika aikin ta, mace tana iya yin abubuwada yawa domin ta kula da iyalinta. Alal misali, Littafi MaiTsarki ya nuna cewa matan aure su “yi �aunar mazajensu,su yi �aunar ’ya’yansu, su zama masu-hankali, masu-tsab-tan rai, masu-aiki a gidajensu, masu-nasiha, masu-biyayyaga mazajensu.” (Titus 2:4, 5) Matar da ta yi irinwannan za a�aunace ta kuma za a daraja ta a iyalinta. (Misalai 31:10, 28)Tun da aure gamin mutane ne biyu ajizai, yanayi mai wuya�warai zai iya kai wa ga rabuwa ko kuma kashe aure. Lit-tafi Mai Tsarki ya yarda a rabu domin wani yanayi. Duk dahaka, kada a �auki rabuwa da wasa, domin Littafi Mai Tsar-ki ya yi garga�i: “Kada matan ta rabu da mijinta . . . , mijinkuma kada shi rabu da matatasa.” (1 Korinthiyawa 7:10, 11)Zina ne kawai daga �aya cikin ma’auratan, zai iya ba da da-mar kashe aure bisa ga Nassosi.—Matta 19:9.

12. Me ya sa ba laifi ba ne mace ta fa�i ra’ayinta cikin ladabi?13. (a) Menene Titus 2:4, 5 suka aririci matan aure su yi? (b) Mene-ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da rabuwa da kuma kisan aure?

138 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

MISALI MAI KYAU GA IYAYE14 Yesu ya kafa misali mai kyau ga iyaye a hanyar da ya bi

da yara. Sa’ad da wasu suke so su hana wa�annan yara �a-nana zuwa wurin Yesu, ya ce: “Ku bar yara �an�anana su zogareni; kada ku hana su.” Littafi MaiTsarki ya ce sai “ya run-gume su, ya sa musu albarka, ya �ibiya musu hannuwa.”(Markus 10:13-16) Tun da Yesu ya ba da lokaci ga yara �a-nana, bai kamata mu ma mu yi haka ba ga yaranmu mazada mata? Suna bukatar, ba �an lokaci ba, amma lokaci maiyawa. Kuna bukatar ku �auki lokaci domin ku koyar da su,domin wannan shi ne abin da Jehobah ya umurci iyaye suyi.—Kubawar Shari’a 6:4-9.

15 Sa’ad da wannan duniyar ta ci gaba da zama muguwa,yara suna bukatar iyaye da za su k

¯are su daga mutanen da

za su nemi su yi musu lahani, irinsu masu lalata da yara.Ka yi la’akari da yadda Yesu ya k

¯are almajiransa, wa�anda

ya kira cikin �auna “’ya’ya �an�anana.” Sa’ad da aka kamashi kuma za a kashe shi ba da da�ewa ba, Yesu ya yi musu

14. Yaya Yesu ya bi da yara, kuma menene yara suke bukata daga iya-yensu?15. Menene iyaye za su yi domin su k

¯are ’ya’yansu?

Wane misali ce mai kyau Saratu ta kafa wa matan aure?

hanyar tsira. (Yohanna 13:33; 18:7-9) Iyaye, kuna bukatarku kasance a fa�ake domin �o�arin Iblis ya yi wa ’ya’yanku�an�anana lahani. Kuna bukatar ku yi musu garga�i a kanlokaci.� (1 Bitrus 5:8) Yanzu sun fi fuskantar ha�ari ta zahi-ri, ta ruhaniya, da kuma ta �abi’a.

16 A daren da Yesu zai mutu, almajiransa sun yi garda-ma game da wanda ya fi girma a tsakaninsu. Maimakon ya

� Za a sami taimako game da yadda za a k¯are yara a babi na 32 na

littafin nan Ka Koya Daga Wurin Babban Malami, Shaidun Jehobahne suka wallafa.

16. Menene iyaye za su iya koya daga hanyar da Yesu ya bi da ajizan-cin almajiransa?

Menene iyaye za su iya koya dagayadda Yesu ya bi da yara?

140 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

yi fushi da su, Yesu ya ci gaba da koyar da su da kalmo-mi da kuma misali. (Luka 22:24-27; Yohanna 13:3-8) Idankana da ’ya’ya, ka ga yadda za ka iya bin misalin Yesu awannan hanyar wajen koyar da yaranka? Hakika, suna bu-katar horo, amma ya kamata a yi shi ‘da adalci’ bacikin fushi ba. Ba za ka so ka yi maganganun rashin tuna-ni “kamar sussukan takobi.” (Irmiya 30:11; Misalai 12:18)Horo ya kamata a yi shi a hanyar da yaro daga baya zai fa-himci cewa hakan daidai ne.—Afisawa 6:4; Ibraniyawa 12:9-11.

MISALI GA YARA17 Akwai abin da yara za su koya kuwa daga Yesu? Hakika

kuwa! Ta wajen misalinsa, Yesu ya nuna yadda ya kamatayara su yi wa iyayensu biyayya. “Ina fa�in wa�annan ma-gana yadda Uba ya koya mini,” in ji shi. Ya da�a cewa:“Kullum ina aika abin da ya gamshe shi.” (Yohanna 8:28, 29) Yesu yana biyayya ga Ubansa na samaniya, kumaLittafi Mai Tsarki ya gaya wa yara su yi biyayya ga iyayensu.(Afisawa 6:1-3) Ko da yake Yesu yaro ne kamili, ya yi wa iya-yensa, Yusufu da Maryamu, da suke ajizai biyayya. Wannanhakika, ya sa kowa a cikin iyalin Yesu ya yi farin ciki!—Luka2:4, 5, 51, 52.

18 A wa�anne hanyoyi ne yara za su iya zama kamar Yesukuma su sa iyayensu su yi farin ciki? Hakika, a wasu lokataizai yi wa yara wuya su yi wa iyayensu biyayya, amma Allahyana so yara su yi wa iyayensu biyayya. (Misalai 1:8; 6:20)Koyaushe Yesu yana yi wa Ubansa na samaniya biyayya, harma a lokaci mai wuya. Akwai lokacin da nufin Allah ne Yesuya yi wani abin da yake da wuya sosai, Yesu ya ce: “Ka ka-war mini da wannan �o�on [wani abin da ake bukata a gare

17. A wace hanya ce Yesu ya kafa misali mai kyau ga yara?18. Me ya sa ko da yaushe Yesu yana yi wa Ubansa na samaniya bi-yayya, kuma waye yake yin farin ciki sa’ad da yara suka yi wa iyayensubiyayya?

Yadda Za Ka Sa Rayuwar Iyalinka ta Zama Mai Farin Ciki 141

shi].” Duk da haka, Yesu ya yi abin da Allah ya ce masa, do-min ya fahimci cewa Ubansa ya san abin da ke mai kyau.(Luka 22:42) Idan suka koyi su yi biyayya, yara za su sa iya-yensu da kuma Ubansu na samaniya su yi farin ciki �warai.�—Misalai 23:22-25.

19 Shai�an ya jarrabi Yesu, kuma za mu iya tabbata cewazai jarrabi yara su yi abin da ba shi da kyau. (Matta 4:1-10)Shai�an Iblis yana amfani da matsi na tsara, wanda yakeda wuya a tsayayya wa. Yana da muhimmanci �warai kadayara su yi abota da masu yin abin da ba shi da kyau! (1 Ko-rinthiyawa 15:33) ’Yar Yakubu Dinatu ta yi abota da mutaneda ba sa bauta wa Jehobah, kuma haka ya saka ta cikinmasifa. (Farawa 34:1, 2) Ka yi tunanin yadda zai shafi iya-linka idan wani cikin iyalin ya fa�a cikin lalata!—Misalai 17:21, 25.

ABIN DA ZAI SA IYALI FARIN CIKI20 Za a iya magance matsala a iyali idan aka yi amfani

da garga�in Littafi Mai Tsarki. Hakika, amfani da wannan

� Idan iyayen suka ce wa yaroya �eta dokar Allah, a nan kawaiyaro zai iya yin rashin biyayya.—Ayukan Manzanni 5:29.

19. (a) Ta yaya Shai�an yake ja-rabtar yara? (b) Yaya lalata nayara zai shafi iyayensu?20. Domin a more rayuwar iya-li, menene dole wa�anda sukecikin iyali za su yi?

Menene ya kamatayara su tuna sa’adda aka jarrabe su?

142 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

garga�i zai sa iyali farin ciki. Saboda haka, maza, ku �au-naci matanku, kuma ku bi da su kamar yadda Yesu yake bida ikilisiyarsa. Mata, ku mi�a kai ga shugabancin mazanku,kuma ku bi misalin macen kirki da aka kwatanta a Mi-salai 31:10-31. Iyaye, ku koyar da ’ya’yanku. (Misalai 22:6)Ubanni, ku sarrafa iyalanku da kyau. (1 Timothawus 3:4, 5;5:8; Kolossiyawa 3:20) Kuma yara, ku yi biyayya ga iyayen-ku. Babu wanda yake cikin iyali da yake kamili, domin bawanda ba ya kuskure. Saboda haka, ku kasance da tawali’u,kuna neman gafarar juna.

21 Hakika, Littafi Mai Tsarki ya �unshi garga�i da umur-ni masu muhimmanci domin rayuwar iyali. Bugu da �ari,ya koya mana game da sabuwar duniya ta Allah da kumaaljanna ta duniya wadda za ta cika da mutane masufarin ciki wa�anda suke bauta wa Jehobah. (Ru’ya ta Yo-hanna 21:3, 4) Wannan bege ne mai ban sha’awa! Hara yanzu, za mu iya more farin ciki na iyali ta wajen am-fani da umurnin Allah da suke cikin Kalmarsa, Littafi MaiTsarki.

21. Wane bege ne mai ban sha’awa muke jira, kuma ta yaya za mumore farin ciki na rayuwar iyali a yanzu?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

ˇ Maza su �aunaci matansu kamar jikinsu.—Afisawa 5:25-29.

ˇ Ya kamata mata su �aunaci iyalinsu su kumadaraja mazansu.—Titus 2:4, 5.

ˇ Iyaye suna bukatar su yi �auna, su koyarkuma su kare ’ya’yansu.—Kubawar Shari’a 6:4-9.

ˇ Yara suna bukatar su yi wa iyayensu biyayya.—Afisawa 6:1-3.

Yadda Za Ka Sa Rayuwar Iyalinka ta Zama Mai Farin Ciki 143

JEHOBAH ALLAH yana �aunarmu �warai kuma yana somu amfana daga ja-gorarsa ta �auna. Idan muka bau-ta masa a hanyar da ta dace, za mu zama masu farin cikikuma za mu guje wa matsalolin rayuwa. Za mu kuwa samialbarka daga wurinsa da kuma taimako. (Ishaya 48:17)Amma, da �arurruwan addinai da suke da’awar suna koyarda gaskiya game da Allah. Duk da haka, koyarwarsu gameda Allah da kuma abin da yake bukata a gare mu sun bam-banta �warai.

2 Ta yaya za ka san hanyar da ta dace ta bauta wa Jeho-bah? Ba ka bukatar ka nazarci koyarwa na dukan addinaikuma ka gwada su. Abin da kake bukata shi ne ka koyiabin da Littafi Mai Tsarki ainihi yake koyarwa game dabauta ta gaskiya. Alal misali: A �asashe da yawa ana famada matsalar jabun ku�i. Idan aka ba ka aikin gano jabunku�i, me za ka fara yi? Za ka je ne ka nazarci dukan jabunku�i? A’a. Zai fi maka alheri idan ka nazarci ku�i na gas-kiya. Bayan ka fahimci yadda ku�i na gaskiya suke, za kaiya ka gane jabu. Hakazalika, idan muka san yadda za mugane addini na gaskiya, za mu iya gane wa�anda suke na�arya.

1. Ta yaya za mu amfana idan muka bauta wa Allah a hanyar da tadace?2. Ta yaya za mu koyi hanyar da ta dace na bauta wa Jehobah, kumawane misali ne ya taimake mu mu fahimci haka?

BABI NA GOMA SHA BIYAR

Bauta da Allah Ya Amince da Ita

Dukan addinai ne suke faranta wa Allah rai?

Ta yaya za mu gane addini na gaskiya?

Su waye suke bauta wa Allah da gaske a yau?

3 Yana da muhimmanci mu bauta wa Jehobah a hanyarda ya amince da ita. Mutane da yawa suna tsammanin Al-lah ya amince da dukan addinai, amma Littafi Mai tsarki baikoyar da haka ba. Muna bukatar fiye da yin da’awar cewamu Kiristoci ne. Yesu ya ce: “Ba dukan mai-ce mini, Uban-giji, Ubangiji, zaya shiga cikinmulkin samaba; saiwanda keaika nufin Ubana wanda ke cikin sama.” Saboda haka, do-min mu sami yardar Allah, dole ne mu koyi abin da Allahyake bukata a gare mu kuma mu yi shi. Yesu ya kira wa-�anda ba sa yi abin da Allah yake so “masu-aika mugunta.”(Matta 7:21-23) Kamar jabun ku�i, addinin �arya ba shi damuhimmanci. Fiye ma da haka, irin wannan addinin yanada lahani.

4 Jehobah ya ba kowa da ke duniya zarafin samun rai ma-dawwami. Domin mu sami rai madawwami a Aljanna, to,dole ne mu bauta wa Allah yadda ya dace kuma mu yi rayu-wadaya aminceda ita. Abinba�in ciki, mutanedayawa sun�i yinhaka. Abin da ya sa ke nanYesu ya ce: “Ku shiga tawu-rin �un�untar �ofa: gama �ofa da f

¯a�i ta ke, hanya kuwa da

f¯a�i, wadda ta nufa wajen hallaka, mutane dayawa fa sunashiga ta wurinta. Gama �ofa �un�unta ce, hanya kuwa ma-tsatsiya, wadda ta nufa wajen rai, masu samunta fa ka�anne.” (Matta 7:13, 14) Addinin gaskiya yana sa a sami rai ma-dawwami. Addinin �arya yana kai wa ga halaka. Jehobah baya so mutane su halaka, abin da ya sa ke nan ya ba mutanea ko’ina zarafi su san shi. (2 Bitrus 3:9) Saboda haka, yaddamuke bauta wa Allah zai kai mu ga rai ko kuwa mutuwa.

YADDA ZA A GANE ADDINI NA GASKIYA5 Ta yaya za a sami ‘hanyar rai?’ Yesu ya nuna cewa addini

3. Idan muna so mu sami yardar Allah, dole ne mu yi menene in jiYesu?4. Mecece ma’anar kalmomin Yesu game da hanyoyi biyu, kuma inane kowace take kai mutane?5. Ta yaya za mu gane wa�anda suke bin addini na gaskiya?

Bauta da Allah Ya Amince da Ita 145

na gaskiya zai bayyana a rayuwar mutane da suke binsa.“Bisa ga ’ya’yansu za ku sansance su,” ya ce. “kowane itacenkirki ya kan fitarda ’ya’yan kirki.” (Matta 7:16, 17) Wato, wa-�anda suke bin addini na gaskiya za a gane su ta wajen abinda suka gaskata da kuma�abi’arsu. Ko da yake ba kamiltattuba ne kuma suna yin kuskure, rukunin masu bauta ta gas-kiya suna �o�ari su yi abin da Allah yake so. Bari mu bincikaabubuwa shida da suka nuna wa�anda suke bin addini nagaskiya.

6 Koyarwar bayin Allah tana da tushe daga cikin LittafiMai Tsarki. Littafi Mai Tsarki kansa ya ce: “Kowane nas-si hurarre daga wurin Allah mai-amfani ne ga koyarwa, gatsautawa, ga kwa�ewa, ga horo kuma da ke cikin adalci: do-min mutumin Allah shi zama kamili, shiryayye sarai dominkowane managarcin aiki.” (2 Timothawus 3:16, 17) Ga ’yan-’uwansa Kiristoci, manzo Bulus ya rubuta: “Sa’anda kukakar�imaganar jawabi daga garemu, watau maganar Allah kenan, kuka kar�e ta, ba kamar maganar mutane ba, amma,yadda ta ke hakika, maganar Allah.” (1 Tassalunikawa 2:13)Saboda haka, abin da aka gaskata da kuma abin da ake yi aaddini na gaskiya ba ta samo asali daga ra’ayin mutane bako kuma al’adarsu. Sun samo asali ne daga hurarriyar Ma-ganar Allah, Littafi Mai Tsarki.

7 Yesu Kristi ya kafa misali da ya dace wajen koyar da abinda ke cikin Kalmar Allah. A addu’arsa ga Ubansa na samani-ya, ya ce: “Maganarka ita ce gaskiya.” (Yohanna 17:17) Yesuya gaskata Kalmar Allah, kuma dukan abin da ya koyar yajitu da Nassosi. Sau da yawa Yesu yana cewa: “An kuma ru-buta.” (Matta 4:4, 7, 10) Sa’an nan Yesu ya yi �aulin nassi.Haka nan, mutanen Allah a yau ba sa koyar da nasu ra’ayi.Sun gaskata cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ce, kumasun koyar da abin da ya ce.

6, 7. Yaya bayin Allah suka �auki Littafi Mai Tsarki, kuma yaya Yesuya kafa misali a wannan?

146 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

WA�ANDA SUKE BAUTA WA ALLAH NA GASKIYA

ˇ koyarwarsu tana da asali cikin Littafi Mai Tsarki

ˇ suna bauta wa Jehobah ne kawai kuma suna sanar dasunansa

ˇ suna �aunar juna

ˇ sun gaskata cewa Yesu shi ne hanyar ceto na Allah

ˇ su ba na duniya ba ne

ˇ suna wa’azin Mulkin Allah cewa shi ne kawai zai ma-gance matsalolin ’yan adam

8 Wa�anda suke bauta ta gaskiya Jehobah kawai suke bau-ta wa kuma suna sanarda sunansa.Yesu ya ce: “Kayi sujjadaga Ubangiji Allahnka, shi ka�ai ma za ka bauta masa.” (Mat-ta 4:10) Saboda haka, bayin Allah ba sa bauta wa wani banda Jehobah. Wannan bautar ta ha�a da sanar da mutanesunan Allah da kuma yadda yake. Zabura 83:18 ta ce: “Kai,wanda sunanka Jehovah ne, kai ka�ai ne Ma�aukaki bisadukan duniya.” Yesu ya kafa misalin taimakon mutane susan Allah, kamar yadda ya ce a cikin addu’arsa: “Na bayanasunanka ga mutane wa�anda ka ba ni daga cikin duniya.”(Yohanna 17:6) Haka nan, masu bauta ta gaskiya a yau sunakoyar da mutane sunan Allah, nufe-nufensa, da kuma hala-yensa.

9 Mutanen Allah suna �aunar junansu da �auna mararson kai. Yesu ya ce: “Bisa ga wannan mutane duka za sufahimta ku ne almajiraina, idan kuma da �auna ga junan-ku.” (Yohanna 13:35) Kiristoci na farko suna da irinwannan�aunar ga juna. Irin wannan �auna ta Allah, ta fi gaban �a-bilanci, da wariya kuma tana jawo mutane ga juna cikin’yan’uwantaka ta gaskiya. (Kolossiyawa 3:14) Wa�anda sukecikin addinin �arya ba su da irin wannan ’yan’uwantaka.Ta yaya muka san wannan? Suna kashe juna domin rashinjituwa ta �asa ko kuma ta �abila. Kiristoci na gaskiya ba sa�aukan makamai su kashe ’yan’uwansu Kiristoci da wasumutane. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Inda ’ya’yan Allah sunbayyanu ke nan, da ’ya’yan Shai�an: dukan wanda ba shiaika adalci ba, ba na Allah ba ne, da wannan kuma wandaba ya yi �aunar �an’uwansa ba . . . Mu yi �aunar junanmu:ba kamar Kayinu wanda shi ke na Shai�an, ya kashe �an’u-wansa.”—1 Yohanna 3:10-12; 4:20, 21.

10 Hakika, �auna ta gaskiya tawuce �in kashe wasu kawai.Kiristoci na gaskiya suna amfani da lokacinsu, da �arfin-

8. Menene bauta wa Jehobah ta �unsa?9, 10. A wa�anne hanyoyi ne Kiristoci na gaskiya suke �aunar juna?

148 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

su, da dukiyarsu domin su taimaki juna kuma su �arfafajuna. (Ibraniyawa 10:24, 25) Suna taimakon juna a lokatanwahala, kuma suna fa�in gaskiya ga wasu. Hakika, suna bingarga�in Littafi Mai Tsarki su “aika nagarta zuwa ga dukanmutane.”—Galatiyawa 6:10.

11 Kiristoci na gaskiya sun gaskata cewa Allah zai ceci mu-tane ta hannun Yesu Kristi ne. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Babuceto ga waninsa: gama babu wani suna �ar�ashin sama, daaka bayar wurin mutane, inda ya isa mu tsira.” (AyukanManzanni 4:12) Kamar yadda muka gani a Babi na 5, Yesuya ba da ransa domin fansar mutane masu biyayya. (Matta20:28) Bugu da �ari, Yesu Sarki ne da Allah ya na�a a Mul-kin sama da zai mallaki dukan duniya. Kuma Allah yanabukatar muyiwaYesubiyayya kumamubi koyarwarsa idanmuna son rai madawwami. Abin da ya sa ke nan Littafi MaiTsarki ya ce: “Wanda yana bada gaskiya ga �an yana da raina har abada; amma wanda ba ya yi biyayya ga �an ba, baza shi ganin rai ba.”—Yohanna 3:36.

12 Masu bauta na gaskiya ba na duniya ba ne. Sa’ad daake yi masa hukunci a gaban Bilatus masarauci na Romawa,Yesu ya ce: “Mulkina ba na wannan duniya ba ne.” (Yo-hanna 18:36) Ko a wace �asa suke da zama, mabiyan Yesutalakawa ne na Mulkin sama kuma saboda haka ba sa sakahannu a sha’anin siyasa na duniya. Ba sa saka hannu kumaa cikin ya�e-ya�enta. Amma kuma, babu ruwan masu bau-ta wa Jehobah idan mutum ya za�i ya shiga siyasa, ya tsayatakara, ko kuma ya yi za�e. Ko da yake, masu bauta wa Al-lah da gaske babu ruwansu da siyasa, masu kiyaye doka ne.Me ya sa? Domin Kalmar Allah ta umurce su su yi “biyayya”ga gwamnatoci “masu mulki.” (Romawa 13:1) Amma idanakwai sa�ani tsakanin abin da Allah yake bukata da abin da

11. Me ya sa yake da muhimmanci a gaskata cewa Allah zai ceci mu-tane ta Yesu Kristi ne?12. Menene kasancewa ba na duniya ba ya �unsa?

Bauta da Allah Ya Amince da Ita 149

tsarin siyasa yake bukata, masu bauta ta gaskiya suna binmisalin manzani, wa�anda suka ce: “Dole sai mu fi biyay-ya ga Allah da mutane.”—Ayukan Manzanni 5:29; Markus12:17.

13 Mabiyan Yesu na gaskiya suna wa’azi cewa MulkinAllah shi ne kawai zai magance matsalolin mutane. Yesu ya

13. Yaya mabiyan Yesu na gaskiya suke �aukan Mulkin Allah, kumawane mataki suka �auka?

Ta wajen bauta wa Jehobah tare da mutanensa zaka sami albarka fiye da wa�anda za ka yi rashi

150 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

annabta cewa: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’a-zinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai;sa’annanmatu�a za ta zo.” (Matta 24:14)MabiyanYesu Kris-ti na gaskiya suna shelar Mulkin Allah cewa shi ne kawai zaimagance matsalolin mutane maimakon su �arfafa mutanesu dogara ga shugabanni su magance matsalolinsu. (Zabura146:3) Yesu ya koya mana mu yi addu’a game da wan-nan gwamnatin sa’ad da ya ce: “Mulkinka shi zo. Abin daka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda ake yinsa cikinsama.” (Matta 6:10) Kalmar Allah ta annabta cewa Mulkinsama “za ya farfashe dukan wa�annan mulkoki ya cinye su,shi kuwa za ya tsaya har abada.”—Daniel 2:44.

14 Bisa ga abin da muka tattauna, ka tambayi kanka:‘Wane addini ya samo dukan abin dayake koyarwa daga Lit-tafi Mai Tsarki kuma yake sanar da sunan Jehobah? Wanerukuni ne yake nuna �auna irin ta Allah, yake ba da gaskiyaa Yesu, kuma ba na duniya ba, kuma yake sanar da MulkinAllah cewa shi ne kawai zai magance matsalolin mutane? Acikin dukan addinai na duniya, wannene ne ya cika dukanwa�annan bukatu?’ Dukanwa�annan sun nuna cewa Shai-dun Jehobah ne.—Ishaya 43:10-12.

MENENE ZA KA YI?15 Ba gaskata wa da Allah ba ne kawai ake bukata domin

a faranta masa rai. Ban da haka ma, Littafi Mai Tsarki ya cealjanu ma sun gaskata Allah yana wanzuwa. (Ya�ub 2:19) Abayyane yake cewa ba sa yin abin da Allah yake so kuma baiamince musu ba. Domin mu sami amincewarsa dole ne mugaskata yana wanzuwa kuma dole ne mu yi abin da yake so.Dole ne kuma mu raba gari da addinin �arya mu rungumibauta ta gaskiya.

14. Wane rukunin addini ne ka gaskata cewa ya cika dukan bukatudomin bauta ta gaskiya?15. Menene kuma Allah yake bukata �ari ga gaskata cewa yana wan-zuwa?

Bauta da Allah Ya Amince da Ita 151

16 Manzo Bulus ya nuna cewa dole ne mu guji saka han-nu cikin addinin �arya. Ya rubuta: “Ku fito daga cikinsu,ku ware, in ji Ubangiji, Kada ku ta�a kowane abu mara-tsar-ki; Ni ma in kar�e ku.” (2 Korinthiyawa 6:17; Ishaya 52:11)Saboda haka Kiristoci na gaskiya suke guje wa dukan waniabin da zai ha�a su da bauta ta �arya.

17 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa dukan addinai na �ar-ya �angaren “Babila Babba” ne.� (Ru’ya ta Yohanna 17:5)Wannan sunan yana tuna mana birnin Babila na d

¯a,

inda addinin �arya ya samo asali bayan Ambaliyar zama-nin Nuhu. Abubuwa da yawa da ake koyarwa kuma ake yia addinin �arya sun samo asali ne tun d

¯a daga Babila. Alal

misali, Babilawa suna bauta wa allah uku cikin �aya. A yau,cibiyar koyarwa ta yawancin addinai allah uku cikin �ayane. Amma Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa Allah �aya ne,Jehobah, kuma Yesu Kristi �ansa ne. (Yohanna 17:3) Babi-lawa kuma sun gaskata cewa mutane suna da kurwa da takerayuwa bayan mutum ya mutu kuma za ta wahala a wajengana azaba. A yau, ana koyar da cewa kurwa za ta wahala acikin wuta a yawancin addinai.

18 Tun da bauta ta Babilawa na d¯a ta ya�u a duniya, Babi-

la Babba ta zamani za a iya ce da ita daular addinan �arya taduniya. Kuma Allah ya ce wannan daular ta addinan �aryaza ta halaka farat �aya ba zato ba tsammani. (Ru’ya ta Yo-hanna 18:8) Ka ga abin da ya sa yake da muhimmanci kaware kanka daga Babila Babba? Jehobah Allah yana so ka“fito daga cikinta” da wuri tun da sauran lokaci.—Ru’ya taYohanna 18:4.

� Domin �arin bayani game da abin da ya sa Babila Babba take wa-kiltan daular addinin �arya ta duniya, dubi Rataye, shafuffuka na 219-220.

16. Menene ya kamata a yi game da saka hannu a addini na �arya?17, 18. Mecece “Babila Babba,” kuma me ya sa yake da gaggawa a “fitodaga cikinta”?

152 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

19 Domin ka yanke shawarar ka daina yin addinin �ar-ya, wasu mutane za su za�i su daina hur�a da kai. Ammata wajen bauta wa Jehobah tare da mutanensa, za ka samialbarka fiye da yadda za ka yi rashi. Kamar almajiran Yesuna farko wa�anda suka �yale abubuwa domin su bi shi, zaka sami ’yan’uwa maza da mata na ruhaniya da yawa. Za kashiga cikin iyali mai girma na miliyoyin Kiristoci na gaski-ya na dukan duniya wa�anda suke nuna �auna ta gaskiya.Kuma za ka sami bege mai ban sha’awa ta rai madawwamia zamani mai zuwa. (Markus 10:28-30) Wata�ila daga baya,wa�anda suka �i ka domin abin da ka gaskata za su bincikaabin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa su zama masu bau-ta wa Jehobah.

20 Littafi Mai Tsarki yana koyar da cewa ba da da�ewa baAllah zai kawo �arshen wannan mugun zamani zai sake shida sabuwar duniya mai adalci a �ar�ashin sarautarsa. (2 Bit-rus 3:9, 13) Wannan duniya ce mai ban sha’awa! Kuma awannan sabon zamani, addini �aya ne kawai zai kasance,da kuma hanyar bauta guda �aya kawai. Ba hikima ba ce agare ka ka �auki matakai da ake bukata domin ka yi hul�ada masu bauta ta gaskiya a yanzu?

19. Menene za ka samu domin bauta wa Jehobah?20. Menene yake zuwa a nan gaba ga wa�anda suke bin addini na gas-kiya?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

ˇ Addini �aya ne kawai na gaskiya.—Matta 7:13, 14.

ˇ Ana gane addini na gaskiya ta wajen koyar-warsa da kuma ayyukansa.—Matta 7:16, 17.

ˇ Shaidun Jehobah suna yin bauta da Allah yaamince da ita.—Ishaya 43:10.

Bauta da Allah Ya Amince da Ita 153

A CE ka fahimci cewa dukan unguwarku ta gur�ata. Waniyana ta zuba guba a �oye, kuma yanayin wurin ya kasanceyana da ha�ari ga rayuwa. Me za ka yi? Hakika, za ka �auraidan ka sami dama. Amma bayan ka �aura ma, za ka tam-bayi kanka, ‘Gubar ta shafe ni ne?’

2 Yanayi mai kama da haka ta samu game da addini na�arya. Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa irin wannanbauta ta gur�ata da koyarwa marasa gaskiya da ayyukamarasa tsabta. (2 Korinthiyawa 6:17) Abin da ya sa ke nanyake da muhimmanci a gare ka ka fito daga “Babila Bab-ba,” daular addinan �arya na duniya. (Ru’ya ta Yohanna18:2, 4) Ka yi hakan kuwa? Idan ka yi haka, to, barkanka.Amma kana bukatar fiye da yin murabus daga addinin�arya. Bayan haka, dole ka tambayi kanka, ‘Shin da wani�igon bauta ta �arya da ta rage a gare ni?’ Ga wasu misa-lai.

1, 2. Wace tambaya kake bukatar ka tambayi kanka bayan ka baraddinin �arya, kuma me ya sa kake tsammanin wannan yana da mu-himmanci?

BABI NA GOMA SHA SHIDA

Ka Dage Domin Bautata Gaskiya

Menene Littafi Mai Tsarki ya koyar gameda amfani da sifofi wajen bauta?

Yaya Kiristoci suke �aukan ranakumasu tsarki na addinai?

Ta yaya za ka yi bayani game da abin da kagaskata ba tare da sa wasu sun fusata ba?

SIFFOFI DA BAUTAR KAKANNI3 Wasu suna da siffofi ko kuma wuraren bauta a gida-

jensu na shekaru da yawa. Kai ma kana da su? Idan hakane, to, kana iya jin cewa ba�on abu ne ko kuma ba dai-dai ba ne a yi wa Allah addu’a ba tare da wa�annanabubuwa da ake gani ba. Wata�ila ka ga cewa kana �au-nar wa�annan abubuwa. Amma Allah ne mai fa�inyadda yake so a bauta masa, kuma Littafi Mai Tsarki yakoya mana cewa ba ya so mu yi amfani da siffofi. (Fito-wa 20:4, 5; Zabura 115:4-8; Ishaya 42:8; 1 Yohanna 5:21)Saboda haka kana iya dagewa domin bauta ta gaskiyata wajen halaka dukan wani abin da ka mallaka da yakeda ala�a da bauta ta �arya. Ka �auke su kamar yadda Je-hobah yake �aukansu—abin “�yama.”—Kubawar Shari’a27:15.

3. (a) Menene Littafi Mai Tsarki ya ce game da amfani da siffofi,kuma me ya sa zai yi wa wasu wuya su amince da yadda Allah yake�aukansu? (b) Me ya kamata ka yi da dukan wani abin da ka mallakada yake da ala�a da bauta ta �arya?

155

4 Yawancin addinan �arya suna bauta wa kakanni. Kafinsu koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki, wasu sun gaskata cewamatattu suna raye a wani lardi marar-ganuwa, kuma za suiya taimaka wa ko yi wa rayayyu lahani. Wata�ila kana �o-�ari matu�a domin ka faranta wa kakanni da suka muturai. Amma kamar yadda ka fahimta daga Babi na 6 nawan-nan littafin, matattu ba sa rayuwa a ko’ina. Saboda haka,babu wani amfani a yi �o�arin magana da su. Dukan wanisa�o daga wa�anda muke �auna da suka mutu ya fito nedaga aljanu. Saboda haka, Jehobah ya hana Isra’ilawa �o-�arin magana da matattu ko kuma su yi kowane irin sihiri.—Kubawar Shari’a 18:10-12.

5 Idan kana amfani da siffofi ko kuma kana bauta wa ka-kanni d

¯a, me za ka yi? Ka karanta kuma ka yi bimbini bisa

Nassosi da suka nuna yadda Allah yake �aukan wa�annanabubuwa. Ka yi wa Jehobah addu’a kullum game da mura-din ka ka dage domin bauta ta gaskiya, kuma ka ro�e shiya taimake ka ka ri�a tunani kamar yadda yake yi.—Ishaya55:9

KIRISTOCI NA FARKO BA SU YI BIKIN KIRSIMATI BA6 Bauta ta �arya za ta iya gur�ata bautar mutum tawajen

bukukuwa. Alal misali, ka yi la’akari da Kirsimati. Kirsi-mati wai bikin tuna haihuwar Yesu Kristi ne, kuma kusandukan wani rukunin addini da ya ce shi Kirista ne yana bi-kin. Duk da haka, babu wani tabbaci cewa almajiran Yesuna �arni na farko sun yi wannan bikin. Littafin nan Sac-

4. (a) Ta yaya muka sani cewa bauta wa kakanni a banza ne? (b) Meya sa Jehobah ya hana mutanensa su saka hannu cikin kowane irin si-hiri?5. Me za ka yi idan kana amfani da siffofi ko kuma bauta wa kakan-ni d

¯a?

6, 7. (a) Kirsimati wai bikin menene ne, amma shin mabiyan Yesuna �arni farko sun yi wannan bikin kuwa? (b) Su waye suke bikin ra-nar haihuwa a lokacin almajiran Yesu na farko?

156 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

red Origins of Profound Things ya ce: “�arnuka biyu bayanhaihuwar Kristi, babu wanda ya san ainihin lokacin da akahaife shi, mutane �alilan ne suka damu da ainihin lokacinda aka haife shi.”

7 Ko da almajiran Yesu sun san ainihin ranar da aka hai-fe shi, ba za su yi biki ba. Me ya sa? Domin kamar yaddaThe World Book Encyclopedia ya ce, Kiristoci na farko sun�auki “bikin ranar haihuwar mutum al’adar arna ne.” Bi-kin ranar haihuwa da aka fa�a a cikin Littafi Mai Tsarkina sarakuna ne biyu da ba sa bauta wa Jehobah. (Farawa40:20; Markus 6:21) Ana kuma yin bikin haihuwa ga al-lolin arna domin a �aukaka su. Alal misali, a ranar 24 gaMayu, Romawa suna bikin haihuwar Daina allahiya. Wa-shegari, sai su yi bikin ranar haihuwar rana, allahnsuApollo. Saboda haka, bikin ranar haihuwa na arna ne bana Kiristoci ba.

8 Da kumawani dalili da ya sa Kiristoci na �arni na farkoba za su yi bikin haihuwar Yesu ba. Wata�ila almajiran-sa sun sani cewa bikin ranar haihuwa yana cike da camfi.Alal misali, Helenawa da Romawa da yawa na zamanind

¯a sun gaskata cewa ruhu yana zuwa wurin haihuwar ko-

wane mutum kuma ya k¯are wannan a dukan rayuwarsa.

“Wannan ruhun yana da dangantaka da allahn da a ranarhaihuwarsa aka haifi mutumin,” in ji littafin nanThe Loreof Birthdays. Hakika, Jehobah ba zai ji da�in dukan wanibiki ba da zai ha�a Yesu da camfi. (Ishaya 65:11, 12) To tayaya mutane da yawa suka zo ga yin bikin Kirsimati?

ASALIN KIRSIMATI9 Shekaru �arurruwa sun shige bayan Yesu ya rayu a

8. Ka yi bayani game da dangantaka da take tsakanin bikin ranar hai-huwa da camfi.9. Ta yaya aka zo ga kafa ranar 25 ga Disamba a zaman ranar bikinhaihuwar Yesu?

Ka Dage Domin Bauta ta Gaskiya 157

duniya kafin mutane suka fara bikin haihuwarsa a ranar25 ga Disamba. Amma wannan ma ba ranar haihuwarYesu ba ce, domin an haife shi a watan Oktoba.� To, meya sa aka za�i ranar 25 ga Disamba? Wasu da suke da’awarcewa su Kiristoci ne wata�ila “suna so ne ranar ta yi dai-dai da ranar bikin haihuwar rana da ba a nasara a kanta taRomawa.’” (The New Encyclopædia Britannica) A lokacinsanyi, sa’ad da rana ba ta da zafi sosai, arna suna bukuku-wa domin rana ta komo daga tafiya mai nisa da ta yi. Sunyi tunanin cewa ranar 25 ga Disamba ce ranar da rana takejuyowa. Domin su sa arna su tuba, shugabannin addinisuka kar�i wannan bikin kuma suka mai da shi ya kasan-ce na “Kiristoci.”�

10 Da da�ewa aka fahimci asalin Kirsimati. Domin tu-shensa aka hana Kirsimati a Ingila da kuma wasuyankunan Amirka a �arni na 17. Dukwanda ya zauna a gida ranar Kirsima-ti zai biya diyya. Ba da da�ewa ba,tsohuwar al’adar ta komo, kuma akada�a wasu sababbi. Kirsimati ya �arazama ranar babban biki, kuma har ayanzu haka yake a �asashe da yawa.Amma, domin nasabar Kirsimati dabauta ta �arya, wa�anda suke so sufaranta wa Allah rai ba sa yin bikin

� Ka dubi Rataye, shafuffuka na 221-222.

� Satunaliya wani bikin Romawa ma yashafi za�an ranar 25 ga Disamba. Ana wan-nan bikin domin a �aukaka allahn Romawana noma a ranakun 17-24 ga Disamba. Anaci, ana sha, ana yin kyauta ga mutane a wan-nan ranaku na Satunaliya.

10. A d¯a, me ya sa wasu mutane ba su yi bi-

kin Kirsimati ba?

Za ka sha mintida aka �auko a

cikin kwata?

158 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

Kirsimati ko kuma wani biki da ya samo asali daga bautararna.�

SHIN ASALIN BIKI YANA DA MUHIMMANCI KUWA?11 Wasu sun yarda cewa irin wannan bukukuwa kamar

su Kirsimati sun samo asali ne daga arna amma duk dahaka suna jin cewa ba laifi ba ne a yi bikin. Ban da hakama, mutane da yawa ba sa tunanin bauta ta �arya sa’adda suke yin biki. Wannan lokaci kuma yana ba wa iyalaizarafin su matso kusa da juna. Haka kake ji? Idan haka ne,to wata�ila �aunar iyali ce, ba �aunar addinin �arya ba,yake sa dagewa ga bauta ta gaskiya yake da wuya. Kakasance da tabbacin cewa Jehobah da ya kafa tushin iyali,yana son ka more dangantaka mai kyau da ’yan’uwanka.(Afisawa 3:14, 15) Kana iya �arfafa wannan dangantakara hanyar da Allah ya amince da ita. Game da abin da yakamata mu damu da shi, manzo Bulus ya rubuta: “Kunagwada abin da ke na yarda ga Ubangiji.”—Afisawa 5:10.

12 Wata�ila kana jin cewa asalin bukukuwa ba su dawani dangantaka da yadda ake yin su a yau. Shin asalinsayana da wani muhimmanci ne? Hakika! Alal misali: A ceka ga minti a cikin kwata. Za ka �auki mintin ne ka sha?Ba daidai ba ne! Wannan mintin ba shi da tsabta. Kamarwannan mintin, bukukuwa suna da da�i, amma an �aukosu ne daga wuri marar tsabta. Domin mu dage ga bauta tagaskiya, muna bukatar mu kasance da ra’ayi irin na anna-bi Ishaya, wanda ya gaya wa masu bauta ta gaskiya: “Kadaku ta�a wani abu mai-�azamta.”—Ishaya 52:11.

� Domin �arin bayani game da yadda Kiristoci na gaskiya suke �au-kan wasu ranakun biki, dubi Rataye, shafuffuka 222-223.

11. Me ya sa wasu mutane suke bukukuwa, amma me ya kamata mudamu da shi?12. Ka ba da misalin abin da ya sa ya kamata mu guje wa al’adu dakuma bukukuwa da suke da mummunan asali.

Ka Dage Domin Bauta ta Gaskiya 159

NUNA FAHIMI WAJEN SHA’ANI DA MUTANE13 Za ka fuskanci �alubale sa’ad da ka za�i ka daina yin

bukukuwa. Alal misali, abokan aiki za su yi mamakin abinda ya sa ka daina saka hannu cikin wasu ayyukan bukuku-wa a wurin aiki. To, idan aka ba ka kyauta ta Kirsimati fa?Ba daidai ba ne ka kar�a? Idan matarka ko mijinki bai gas-kata abin da ka ko kika gaskata ba fa? Ta yaya za ka tabbatacewa yaranka ba sa jin cewa an cuce su domin ba ka yinbukukuwa?

14 Ana bukatar fahimi domin a magance kowane yanayi.Idan mutum ya yi maka barka domin bikin da ake yi, kanaiya gode wa mutumin mai yi maka fatan alheri. Amma ace kana tare ne da mutumin da kake gani ko kuma kakeaiki da shi kullum. A irin wannan yanayi kana iya yi masabayani. A dukan yanayi, ka yi magana cikin basira. Litta-fi Mai Tsarki ya ba da shawara: “Bari zancenku kullum yakasance tare da alheri, gyartace da gishiri, domin ku saniyadda za ku amsa tambayar kowa.” (Kolossiyawa 4:6) Kamai da hankali domin kada ka raina mutane. Maimakonhaka, ka yi musu bayanin matsayinka cikin basira. Ka ba-yana musu cewa ba ka �in kyauta kuma ba ka �in gaisuwaamma ka fi son haka a wani lokaci dabam.

15 Idan wani yana so ya yi maka kyauta fa? Ya danganabisa yanayin. Mai bayarwa yana iya cewa: “Na sani ba kayin wannan bikin. Duk da haka, ina so in ba ka wannan.”Kana iya shawartawa cewa kar�an wannan kyauta a wan-nan yanayi ba �aya ba ne da yin bikin. Hakika, idan maibayarwa bai san abin da ka gaskata ba, kana iya gaya masacewa kai ba ka yin wannan biki. Wannan zai taimaka wa-jen yin bayanin abin da ya sa ka kar�i kyauta amma ba ka

13. Wa�anne �alubale ne za ka fuskanta sa’ad da ka daina yin buku-kuwa?14, 15. Menene za ka yi idan aka yi maka barka da wani biki ko kumaidan wani ya so ya ba ka kyauta?

160 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

ba da kyauta a wannan lokaci ba. A wani �angare kuma,zai fi kyau kada ka kar�i kyauta idan an bayar ne domin anuna cewa ba ka manne wa abin da ka gaskata ko kuma ka�i abin da ka gaskata saboda abin duniya.

WA�ANDA SUKE CIKIN IYALINKA KUMA FA?16 Idan wani cikin iyali bai gaskata abin da ka gaskata

ba fa? Har ila, ka nuna basira. Babu bukatar ka ri�a mitadomin al’ada ko kuma biki da �an’uwanka ya za�i ya yi.Maimakon haka, ka fahimci cewa suna da ’yancin su ka-sance da ra’ayinsu, kamar yadda kake so su daraja naka’yancin. (Matta 7:12) Ka guji dukan wani abin da zai saka saka hannu cikin bikin. Duk da haka, ka kasance maisanin ya kamata idan ya kai ga batutuwa da ba su kasanceyin bikin ba. Hakika, ko da yaushe ka yi abin da zai sa la-mirinka ya kasance da tsabta.—1 Timothawus 1:18, 19.

17 Menene za ka yi domin kada ’ya’yanka su ji an cucesu domin ba ka yin bukukuwan arna? Yawanci ya danganabisa abin da kake yi a wasu lokatai na shekara. Wasu iyayesuna za�an lokaci da za su yi wa ’ya’yansu kyauta. Kyautamafi kyau da za ka yi wa ’ya’yanka ita ce lokaci da kula.

KA YI BAUTA TA GASKIYA18 Domin ka faranta wa Allah rai, dole ne ka guji bauta

ta �arya ka dage domin bauta ta gaskiya. Menene wan-nan ya �unsa? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mu lura da junadomin mu tsokani juna zuwa ga �auna da nagargarun ay-yuka; kada mu fasa tattaruwanmu, kamar yadda wa�ansusun saba yi, amma mu garga�adda juna; balle fa yanzu,

16. Ta yaya za ka nuna basira sa’ad da kake bi da batutuwa da sukashafi bukukuwa?17. Ta yaya za ka taimaki ’ya’yanka kada su ji cewa ka cuce su sa’adda suka ga wasu suna yin bukukuwan?18. Ta yaya halartar tarurruka na Kirista zai taimake ka ka dage do-min bauta ta gaskiya?

Ka Dage Domin Bauta ta Gaskiya 161

da kuna ganin ranan nan tana gusowa.” (Ibraniyawa 10:24, 25) Tarurruka na Kirista lokatai ne na farin ciki dominka bauta wa Allah a hanyar da ya amince da ita. (Zabura22:22; 122:1) A irin wa�annan tarurruka, ana “�arfafawa”juna a tsakanin Kiristoci masu aminci.—Romawa 1:12.

19 Wata hanya kuma da za ka dage domin bauta ta gas-kiya ita ce ta wajen gaya wa mutane game da abubuwa dakake koya daga nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jeho-bah. Mutane da yawa suna “ajiyar zuci, suna kuwa kuka”saboda mugunta da ake yi a duniya a yau. (Ezekiel 9:4)Wata�ila ka san mutane da suke jin haka. Ka gaya musugame da begenka daga Littafi Mai Tsarki game da nan gabakuwa? Sa’ad da kake hul�a da Kiristoci na gaskiya kumakake gaya wa mutane game da gaskiya mai ban sha’awa taLittafi MaiTsarki da ka koya, za ka ga cewa dukan abin mu-radi da kake da shi na al’adun addinin �arya a hankali zai�ace. Ka tabbata cewa za ka yi farin ciki �warai kuma zaka sami albarkatu masu yawa idan ka dage domin bauta tagaskiya.—Malachi 3:10.

19. Me ya sa yake da muhimmanci ka gaya wa mutane abin da kakoya daga Littafi Mai Tsarki?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

ˇ Ba a amince da siffofi ba ko bautar kakannia bauta ta gaskiya.—Fitowa 20:4, 5; KubawarShari’a 18:10-12.

ˇ Ba daidai ba ne mu saka hannu cikin bukuku-wa da suka samo asali daga bauta ta arna.—Afisawa 5:10.

ˇ Kiristoci na gaskiya su yi bayanin abin dasuka gaskata ga wasu cikin basira.—Kolossiya-wa 4:6.

162 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

Yin bauta ta gaskiya yanakawo farin ciki na gaske

IDAN aka gwada da sararin samaniya, duniya �an�anu-wa ce. Hakika, ga Jehobah “wanda ya yi sama da duniya,”al’ummai kamar �igon ruwa suke daga guga. (Zabura115:15; Ishaya 40:15) Duk da haka, Littafi Mai Tsar-ki ya ce: Jehobah “yana kusa da dukan wa�anda su kekira bisa gareshi, ga dukan wa�anda su ke kira gareshi dagaskiya. Za ya biya muradin wa�anda ke tsoronsa; za yakuma ji kukarsu, ya cece su.” (Zabura 145:18, 19) Ka yi tu-nanin abin da wannan yake nufi! Mahalicci mai iko dukayana kusa da mu kuma yana sauraronmu idan muka‘kira shi da gaskiya.’ Gata ce mu je gaban Allah cikin ad-du’a!

2 Amma idan muna so Jehobah ya saurari addu’armu,dole ne mu yi addu’a a hanyar da ya amince da ita. Zamu iya yin haka ne idan muka fahimci abin da LittafiMai Tsarki yake koyarwa game da addu’a. Yana da mu-himmanci mu fahimci abin da Nassosi suka ce game dawannan batu, domin addu’a tana taimakonmu mu ku-sanci Jehobah.

1, 2. Me ya sa za mu �auki addu’a cewa gata ce mai girma, kuma meya sa muke bukatar mu san abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwagame da ita?

BABI NA GOMA SHA BAKWAI

Ka Kusaci Allah CikinAddu’a

Me ya sa za mu yi addu’a ga Allah?

Menene dole ne mu yi domin Allah yasaurare mu?

Ta yaya Allah yake amsa addu’o’inmu?

ME YA SA ZA MU YI ADDU’A GA JEHOBAH?3 Wani dalili �aya mai muhimmanci da ya sa za mu yi

addu’a ga Jehobah shi ne cewa shi ya gayyace mu mu yihaka. Kalmarsa ta �arfafa mu: “Kada ku yi alhini cikin ko-wane abu; amma cikin kowane abu, ta wurin addu’a daro�o tare da godiya, ku bar ro�e ro�enku su sanu ga Allah.Salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, zata tsare zukatanku da tunaninku cikin Kristi Yesu.” (Filibbi-yawa 4:6, 7) Hakika kuwa ba za mu so mu yi banza da irinwannan tanadi da Mamallakin dukan sararin samaniya yayi mana ba!

4 Wani dalili kuma na addu’a a kai a kai ga Jehobah shine cewa hanyar �arfafa dangantakarmu da shi ne. Aboka-nai na gaskiya ba sai sa’ad da suke bukatar wani abu sukemagana da juna ba. Maimakon haka, abokanai nagari su-kan �aunaci juna, kuma dangantakarsu tana �arfafa sa’adda suka fa�i ra’ayinsu, damuwarsu, da kuma juyayinsu a

3. Wane dalili ne mai muhimmanci ya sa za mu yi addu’a ga Jeho-bah?4. Ta yaya addu’a a kai a kai ga Jehobah yake �arfafa dangantakarmuda shi?

“Wanda ya yi sama daduniya” yana shirye yasaurari addu’o’inmu

165

sake. A wasu yanayi, haka dangantakarmu da Jehobah Al-lah take. Da taimakon wannan littafin, ka koyi abubuwamasu yawa game da abin da Littafi Mai Tsarki yake koyar-wa game da Jehobah, mutuntakarsa, da kuma nufinsa. Kafahimci cewa shi wani ne da gaske. Addu’a tana ba ka zara-fi ka furta tunaninka da kuma motsin zuciyarka ga Ubankana samaniya. Sa’ad da ka yi haka, za ka kusaci Jehobah.—Ya�ub 4:8.

WA�ANNE BUKATU NE DOLE MU CIKA?5 Shin Jehobah yana sauraron dukan addu’o’i ne? Ka yi

la’akari da abin da ya gaya wa Isra’ilawa masu tawaye azamanin annabi Ishaya: “Sa’anda ku ke yi mini yawan ad-du’oi, ba ni ji ba: hannuwanku cike su ke da jini.” (Ishaya1:15) Saboda haka wasu ayyuka za su iya sa Allah ya �i sau-raron addu’o’inmu. Domin Allah ya saurari addu’o’inmuda tagomashi, dole ne mu cika wasu bukatu.

6 Bukata mai muhimmanci, ita ce ba da gaskiya. (Mar-kus 11:24) Manzo Bulus ya rubuta: “Ba shi kuwa yiwuwaa gamshe [Allah] ba sai tare da bangaskiya: gama mai-zuwa wurin Allah sai shi bada gaskiya akwai shi, kuma shimai-sakawa ne ga wa�anda ke bi�arsa.” (Ibraniyawa 11:6)Kasancewa da bangaskiya ta gaske ya fi kawai sanin cewaakwai Allah kuma cewa yana sauraro kuma yana amsa ad-du’o’i. Ta wajen ayyuka ake tabbatar da bangaskiya. Dolene mu tabbatar da cewa muna da bangaskiya ta yaddamuke rayuwa a kowace rana.—Ya�ub 2:26.

7 Jehobah yana bukatar wa�anda suka je gare shi cikinaddu’a su yi haka da tawali’u da kuma zuciya mai gaskiya.

5. Menene ya nuna cewa Jehobah ba ya sauraron dukan addu’o’i?6. Domin Allah ya saurari addu’o’inmu, mecece muhimmiyar buka-ta, kuma ta yaya za mu cika wannan?7. (a) Me ya sa ya kamata mu daraja Jehobah sa’ad da muke yin ma-gana da shi? (b) Sa’ad da muke addu’a ga Allah, ta yaya za mu nunatawali’u da kuma zuciya mai gaskiya?

166 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

Muna bukatar mu kasance da tawali’u sa’ad da muke ma-gana da Allah ko ba haka ba? Sa’ad da mutane suka samidamar magana da sarki ko kuma shugaban �asa, suna da-raja shi, suna �aukaka matsayi mai girma na mai mulkin.Muna bukatar ba wa Jehobah daraja fiye da haka ma! (Za-bura 138:6) Domin shi ne “Allah Al�adiru.” (Farawa 17:1)Sa’ad da muka yi addu’a ga Allah, yadda muka yi haka yakamata ya nuna cewa mun fahimci matsayinmu cikin ta-wali’u a gabansa. Irin wannan tawali’un zai kuma motsamu mu yi addu’a daga zuciyarmu cikin gaskiya, za mu gujewa maimaita addu’a.—Matta 6:7, 8.

8 Wani abu kuma da zai sa Allah ya saurare mu shi ne yinayyukan da suka jitu da addu’o’inmu. Jehobah yana so muyi iya gwargwadon �arfinmu mu yi abin da muka yi addu’adominsa. Alal misali, idan muka yi addu’a, “ka ba mu yauabincin yini,” dole ne mu yi aiki da �wazo a dukan aiki daza mu iya yi. (Matta 6:11; 2 Tassalunikawa 3:10) Idan mukayi addu’a domin mu magance wani rauni na jiki, dole nemu mai da hankali mu guji dukan wani yanayi da zai iyakai mu cikin jaraba. (Kolossiyawa 3:5) �ari ga wa�annanbukatu masu muhimmanci, da wasu tambayoyi game daaddu’a da za mu bukaci amsa.

AMSA WASU TAMBAYOYI GAME DA ADDU’A9 Ga waye ya kamata mu yi addu’a? Yesu ya koya wa ma-

biyansa su yi addu’a ga “Ubanmu wanda ke cikin sama.”(Matta 6:9) Saboda haka, addu’armu dole ne ta kasan-ce ga Jehobah Allah shi ka�ai. Amma kuma, Jehobah yabukaci mu fahimci matsayin �ansa maka�aici, Yesu Kristi.Kamar yadda muka koya a Babi na 5, an aiko Yesu duniyadomin ya fanshe mu daga zunubi da mutuwa. (Yohanna3:16; Romawa 5:12) Shi ne Babban Firist da kuma Al�ali da

8. Ta yaya za mu yi aiki da ya yi daidai da addu’armu?9. Ga wa za mu yi addu’a, kuma ta wurin wa?

Ka Kusaci Allah Cikin Addu’a 167

aka na�a. (Yohanna 5:22; Ibraniyawa 6:20) Saboda haka,Nassosi suka umurce mu mu yi addu’o’inmu ta wurinYesu. Shi kansa ya ce: “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne rai:ba mai-zuwa wurin Uban sai ta wurina.” (Yohanna 14:6)Domin a saurari addu’o’inmu, dole ne mu yi addu’a ga Je-hobah ta wurin �ansa.

10 Dole ne mu kasance cikin wani yanayi sa’ad da muke ad-du’a? A’a. Jehobah bai bukaci kasancewa cikin wani yanayiba, ko na hannu ko kuma na dukan jiki. Littafi Mai Tsarkiya koyar da cewa daidai ne a yi addu’a a cikin yanayi masuyawa. Wannan ya ha�a da yin addu’a a zaune, a dur�u-she, a tsaye. (1 Labarbaru 17:16; Nehemiah 8:6; Daniel 6:10;Markus 11:25) Abin da ya fi muhimmanci shi ne zuciyar kir-ki, ba abin da wasu mutane za su gani ba. Hakika, sa’ad damuke ayyukanmunayaudakullumkokuma sa’addamukafuskanci yanayi na gaggawa, muna iya yin addu’a a zuciyar-mu a dukan inda muke. Jehobah yana saurarar addu’a mada wasu ba su lura da ita ba.—Nehemiah 2:1-6.

11 Menene za mu ro�a? Littafi Mai Tsarki ya yi bayani:“Idan mun ro�i komi daidai da nufinsa, [Jehobah] yanajinmu.” (1 Yohanna 5:14) Saboda haka mu ro�i abubuwada suke bisa ga nufin Allah. Nufinsa ne mu yi ro�o game daabubuwa da suka dame mu? Hakika kuwa! Addu’a ga Jeho-bah za ta iya kasance kamar magana ne da aboki na kudda kud. Za mu iya ‘zazzage zuciyarmu’ ga Allah. (Zabura62:8) Daidai ne a gare mu mu yi ro�o domin ruhu mai tsar-ki, domin zai taimake mu mu yi abin da ke nagari. (Luka11:13) Za mu iya kuma yin ro�o domin ja-gora sa’ad damuke so mu yanke shawara, da kuma jimiri sa’ad da mukefuskantar matsaloli. (Ya�ub 1:5) Sa’ad da muka yi zunubi,

10. Me ya sa babu ta�aitaccen yanayi da ake bukata sa’ad da ake ad-du’a?11. Wa�anne damuwa ne namu za su kasance batutuwa da suka dacena addu’a?

168 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

ya kamata mu ro�i gafara bisa ga hadayar Kristi. (Afisa-wa 1:3, 7) Hakika, ba al’amuran kanmu ba ne ya kamatasu zama batutuwan addu’o’inmu. Mu yi wa wasu muta-ne addu’a—’yan iyalinmu da kuma ’yan’uwanmu masu bi.—Ayukan Manzanni 12:5; Kolossiyawa 4:12.

12 Batutuwa da suka shafi Jehobah Allah ya kamata musa su farko a addu’o’inmu. Dole ne mu furta yabo da godi-ya daga zukatanmu domin dukan alherinsa. (1 Labarbaru29:10-13) Yesu ya koyar da addu’ar misali, da ke rubuce aMatta 6:9-13, a ciki ya koyar damu mu yi addu’a cewa a tsar-kake sunan Allah. Mulkin Allah ya zo kuma bayan wannana yi nufinsa a duniya kamar yadda ake yi a sama. Bayan yagamadawa�annan batutuwada suka shafi Jehobahne Yesuya mai da hankali ga damuwa na mutane. Sa’ad da mukaba wa Allah wuri mai muhimmanci a addu’armu, munanuna cewa ba damuwarmu ba ce kawai ta dame mu.

13 Yaya ya kamata tsawon addu’armu ya kasance? LittafiMai Tsarki bai kafa iyaka ga tsawon lokacin da ya kama-ta mu yi muna addu’a, na kanmu ko ga jama’a ba. Zai iyakasancewa daga gajeriyar addu’a kafin cin abinci zuwa do-guwar addu’ar kanmu a nan muna iya bu�e cikinmu gaJehobah. (1 Sama’ila 1:12, 15) Amma fa, Yesu ya la’ancimutanen da suke nuna cewa suna da adalci, masu addu’adon mutane su yabe su. (Luka 20:46, 47) Irin wannan ad-du’o’i ba sa burge Jehobah. Abin da yake da muhimmancishi ne mu yi addu’a da ta fito daga zuciyarmu. Sabodahaka, tsawon addu’a da za a kar�a zai bambanta bisa ga bu-kata da kuma yanayi.

14 Sau nawa ya kamata mu yi addu’a? Littafi Mai Tsarki

12. Ta yaya za mu ba wa batutuwa da suka shafi Ubanmu na samawuri mai muhimmanci a addu’armu?13. Menene Nassosi suka nuna game da tsawon addu’a da za a kar�a?14. Menene Littafi Mai Tsarki yake nufi sa’ad da ya �arfafa mu mu “yiaddu’a,” a kai a kai kuma me ya sa wannan yake da ban �arfafa?

Ka Kusaci Allah Cikin Addu’a 169

ya �arfafa mu mu “yi addu’a,” a kai a kai mu “lizima ci-kin addu’a,” kuma ya ce mu “yi addu’a ba fasawa.” (Matta26:41; Romawa 12:12; 1 Tassalunikawa 5:17) Hakika, wa-�annan furci ba sa nufin cewa dole ne mu ri�a addu’a gaJehobah dare da rana ba. Maimakon haka, Littafi Mai Tsar-ki yana ariritarmu ne mu ri�a addu’a a kai a kai, mu ri�ayi wa Jehobah godiya domin alherinsa kuma mu ri�a zubamasa idanu domin ja-gora, �arfafa, da kuma �arfi. Ba abinfarin ciki ba ne mu sani cewa Jehobah bai kafa iyaka ba gatsawon lokaci da za mu yi muna addu’a ko kuma yawan lo-kaci da za mu yi masa addu’a ba? Idan muna �aukaka gataryin addu’a, za mu nemi zarafin yin addu’a ga Ubanmu nasama.

15 Me ya sa za mu ce “Amin” a �arshen addu’a? Kalmarnan “Amin” yana nufin “hakika,” ko kuma “hakan ya ka-sance.” Misalai na Nassosi sun nuna cewa daidai ne muce “Amin” a �arshen addu’ar kanmu ko kuma ga jama’a.(1 Labarbaru 16:36; Zabura 41:13) Ta wajen cewa “Amin” a�arshen addu’a, muna tabbatarwa ne cewa furcin da mukayi da gaske ne. Sa’ad da muka ce “Amin”—ko a hankaliko da babbar murya—a �arshen addu’ar wani, muna nunacewa mun yarda da abin da ya ce.—1 Korinthiyawa 14:16.

YADDA ALLAH YAKE AMSA ADDU’O’INMU16 Da gaske ne Jehobah yana amsa addu’o’i? Hakika

kuwa! Muna da dalilai masu �arfi na tabbata cewa mai “jinaddu’a” ne, yana amsa addu’o’i da miliyoyin mutane sukayi da zuciya �aya. (Zabura 65:2) Amsar Jehobah ga addu’ar-mu tana iya zuwa a hanyoyi dabam dabam.

17 Jehobahyana amfani da mala’ikunsa da kuma bayinsa

15. Me ya sa za mu ce “Amin” a �arshen addu’armu ko kuma ga ja-ma’a?16. Wane tabbaci ne za mu yi game da addu’a?17. Me ya sa za a iya cewa Allah yana amfani da mala’ikunsa da kumabayinsa na duniya wajen amsa addu’o’inmu?

170 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

na duniya ya amsa addu’o’i. (Ibraniyawa 1:13, 14) Da labarimasu yawa na mutane da suka yi addu’a ga Allah ya taima-ke su su fahimci Littafi Mai Tsarki ba da da�ewa ba bayanhaka bayin Jehobah suka same su. Irin wa�annan labaransun ba da tabbatacin ja-gorar mala’iku a aikin wa’azi naMulki. (Ru’ya ta Yohanna 14:6) Domin ya amsa addu’o’in-mu da muka yi a lokacin da muke da bukata, Jehobah yanamotsa wani Kirista ya taimake mu.—Misalai 12:25; Ya�ub2:16.

Yana iya sauraronaddu’armu a kowane lokaci

Ka Kusaci Allah Cikin Addu’a 171

18 Jehobah Allah kumayana amfani da ruhunsamai tsarki da kuma Kal-marsa, Littafi Mai Tsarki,ya amsa addu’o’in bayin-sa. Yana iya amsaaddu’armu na taimakomu jimre wa gwaji ta wa-jen yi mana ja-gora dakuma ba mu �arfi ta wa-jen ruhunsa mai tsarki.(2 Korinthiyawa 4:7) Sau da yawa amsar addu’armu dominja-gora daga Littafi Mai Tsarki take zuwa, a nan Jehobahyake yi mana taimako mu yanke shawara da ta dace. Anaiya samun Nassosi da za su yi taimako a lokacin nazarinLittafi Mai Tsarki na kanmu da kuma sa’ad da muka ka-ranta littatafai na Kirista, kamar irinwannan littafin. Wanibayani da muke bukata ana iya tuna mana shi ta wajenabin da aka fa�a a taron Kirista ko kuma ta wajen kalamindattijo a ikilisiya da ya damu da yanayinmu.—Galatiyawa6:1.

19 Idan kamar Jehobah yana jinkirin amsa addu’o’inmu,wannan ba domin ba zai iya amsa su ba ne. Maimakonhaka, dole mu tuna cewa Jehobah yana amsa addu’o’i nebisa ga nufinsa kuma a lokacinsa. Ya san abin da muke bu-kata da kuma yadda za mu magance su fiye da yadda mukasani. Sau da yawa yana �yale mu mu ‘yi ta ro�o, mu yi ta

18. Ta yaya Jehobah yake amfani da ruhunsa mai tsarki da kuma Kal-marsa ya amsa addu’o’in bayinsa?19. Menene ya kamata mu tuna idan kamar ba a amsa addu’o’in-mu ba?

Domin amsa addu’o’inmu,Jehobah yana iya motsaKiristoci su taimake mu

nema, mu yi ta �wan�wasawa.’ (Luka 11:5-10) Irin wannan naciya tana nuna waAllah cewa muradinmu yana da �arfikuma bangaskiyarmu ta gaskiya ce. Buguda �ari, Jehobah zai amsa addu’o’inmu ahanyar da ba za ta bayyana �iri �iri ba agare mu. Alal misali, zai amsa addu’armugame da wani gwaji, ba ta wajen kawar damatsalar ba, amma ta wajen ba mu �arfimu jimre.—Filibbiyawa 4:13.

20 Ya kamata mu zama masu godi-ya domin Mahaliccin wannan sararinsamaniya yana kusa da dukan wa�an-da suke kiransa cikin addu’ar da ta dace.(Zabura 145:18) Ya kamata mu yi amfa-

ni da zarafin yin addu’a. Idan muka yi haka, za mu samibege mai ban farin ciki na kusantar Jehobah, mai amsaaddu’o’i.

20. Me ya sa za mu yi amfani da zarafin addu’a?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

ˇ Yin addu’a ga Jehobah a kai a kai yana taima-konmu mu kusace shi.—Ya�ub 4:8.

ˇ Domin Allah ya saurari addu’o’inmu, dole nemu yi addu’a cikin bangaskiya da kuma zuci-ya mai gaskiya.—Markus 11:24.

ˇ Dole ne mu yi addu’a ga Jehobah shi ka�ai tawurin �ansa.—Matta 6:9; Yohanna 14:6.

ˇ Jehobah mai “jin addu’a” yana amfani damala’ikunsa, bayinsa na duniya, ruhunsa maitsarki, da kuma Kalmarsa wajen amsa ad-du’o’i.—Zabura 65:2.

173

“GA RUWA! Me za ya hana a yi mini baftisma?” Tamba-yar da Bahabashe ma’aikacin kotu ya yi ke nan a �arni nafarko. Wani Kirista mai suna Filib ya tabbatar masa cewaYesu shi ne Almasihu. Da abin da ya koya daga Nassosi

1. Me ya sa Bahabashe ma’aikacinkotu ya ro�i a yi masa baftisma?

BABI NA GOMA SHA TAKWAS

Baftisma da KumaDangantakarka da Allah

Ta yaya ake yin baftisma na Kirista?

Wa�anne matakai kake bukatar ka �auka dominka cancanci yin baftisma?

Ta yaya mutum yake ke�e kansa ga Allah?

Menene dalili na musammanna yin baftisma?

suka motsa zuciyarsa, sai Bahabashen ya �auki mataki.Ya nuna cewa yana so a yi masa baftisma!—Ayukan Man-zanni 8:26-36.

2 Idan ka yi nazarin babunan baya na wannan littafi dakyau da wani Mashaidin Jehobah, kana iya jin ya kai kayi tambaya, ‘Me za ya hana a yi mini baftisma?’ A yan-zu ka riga ka koyi game da alkawarin Littafi Mai Tsarkina rai madawwami a Aljanna. (Luka 23:43; Ru’ya ta Yo-hanna 21:3, 4) Kuma ka koyi game da yanayin gaske namatattu da kuma begen tashin matattu. (Mai-Wa’azi 9:5;Yohanna 5:28, 29) Wata�ila kana tarayya da Shaidun Je-hobah a taron ikilisiyarsu kuma ka gani da idanunkayadda suke yin addini na gaskiya. (Yohanna 13:35) Mafimuhimmanci ma, wata�ila ka fara �ulla dangantaka daJehobah Allah.

3 Ta yaya za ka nuna cewa kana so ka bauta wa Al-lah? Yesu ya gaya wa mabiyansa: ‘Ku tafi ku almajirtaddadukkan al’ummai, kuna yi masu baftisma.’ (Matta 28:19)Yesu kansa ya kafa misali ta wajen yin baftisma cikinruwa. Ba a yafa masa ruwa ba, ba kuwa zuba masa ruwakawai a ka ba. (Matta 3:16) Kalmar nan “baftisma” dagaHellenanci ce tana nufin “tsoma.” Saboda haka, baftismana Kiristoci tana nufin a tsoma, ko kuma a nutsa cikinruwa.

4 Baftisma cikin ruwa bukata ce ga dukan wa�andasuke so su �ulla dangantaka da Jehobah Allah. Yin baftis-ma a fili yana nuna muradinmu na bauta wa Allah. Yananuna cewa kana farin ciki ka yi nufin Jehobah. (Zabura40:7, 8) Domin ka cancanci baftisma, dole ne ka �aukiwasu matakai.

2. Me ya sa za ka yi tunani da kyau game da baftisma?3. (a) Wane umurni ne Yesu ya ba wa mabiyansa? (b) Yaya ake yinbaftisma na ruwa?4. Menene baftisma cikin ruwa yake nufi?

Baftisma da Kuma Dangantakarka da Allah 175

ANA BUKATAR SANI DA KUMA BANGASKIYA5 Ka riga ka fara �aukan mataki na farko. Ta yaya? Ta

wajen neman sanin Jehobah Allah da kuma Yesu Kris-ti ta nazarin Littafi Mai Tsarki a tsanake. (Yohanna 17:3)Amma da abubuwa da yawa na koyo har yanzu. Kiristo-ci suna so a cika su da ‘sanin nufin’ Allah. (Kolossiyawa1:9) Halartar tarurruka a ikilisiya na Shaidun Jehobahzai yi taimako a wannan. Yana da muhimmanci a halarciirin wa�annan tarurruka. (Ibraniyawa 10:24, 25) Halar-tar taro a kai a kai zai taimake ka ka �ara saninka naAllah.

6 Hakika, ba ka bukatar sanin dukan abin da ke ci-kin Littafi Mai Tsarki kafin ka cancanci a yi makabaftisma. Bahabashen ma’aikacin kotu yana da �ansani, amma ya bukaci taimako domin ya fahimci wasu�angarori na Nassosi. (Ayukan Manzanni 8:30, 31) Ha-kazalika, za ka bukaci ka koyi abubuwa masu yawa.Hakika, ba za ka ta�a daina koyo game da Allah ba.(Mai-Wa’azi 3:11) Amma, kafin a yi maka baftisma,kana bukatar ka sani kuma ka gaskata muhimman ko-yarwa na Littafi Mai Tsarki. (Ibraniyawa 5:12) Irinwa�annan koyarwa sun ha�a da gaskiya game da ya-nayin matattu da kuma muhimmancin sunan Allah dakuma Mulkinsa.

7 Sani kawai bai isa ba, domin “ba shi kuwa yiwuwaa gamshe [Allah] ba sai tare da bangaskiya.” (Ibraniyawa11:6) Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa wasu mutanea birnin Koranti na d

¯a suka saurari sa�on Kiristoci, suka

“bada gaskiya, aka yi musu baftisma.” (Ayukan Manzan-

5. (a) Menene mataki na �aya domin cancanta don baftisma? (b) Meya sa tarurruka na Kirista suke da muhimmanci?6. Yaya yawan ilimin Littafi Mai Tsarki da kake bukata domin ka can-canci yin baftisma?7. Yaya ya kamata yin nazarin Littafi Mai Tsarki ya shafe ka?

176 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

ni 18:8) Hakanan a yau, nazarin Littafi Mai Tsarki ya ka-mata ya cika ka da bangaskiya cewa lalle Kalmar Allahce hurarriya. Nazarin Littafi Mai Tsarki ya kamata ya tai-make ka ka gaskata alkawuran Allah da kuma ikon cetona hadayar Yesu.—Joshua 23:14; Ayukan Manzanni 4:12;2 Timothawus 3:16, 17.

KA SANAR DA MUTANE GASKIYARLITTAFI MAI TSARKI

8 Sa’ad da bangaskiya ta cika zuciyarka, zai yi makawuya ka rufe bakinka ka �i fa�ar abin da ka koya. (Irmiya20:9) Za ta motsa ka ka gaya wa mutane game da Allah dakuma nufinsa.—2 Korinthiyawa 4:13.

9 Za ka iya fara gaya wa wasu game da gaskiyar Litta-fi Mai Tsarki cikin basira ta wajen yin magana game daita ga danginka, abokananka, ma�wabta, da kuma abo-kan aiki. Bayan wani lokaci, za ka so ka fara aikinwa’azi da Shaidun Jehobah. A wannan lokaci, kana iyatattauna batun da Mashaidin da ya koya maka gaski-ya ta Littafi Mai Tsarki. Idan ka cancanci ka fita wa’azina fage, za a yi shiri kai da malaminka ku sadu da datta-wan ikilisiya.

10 Wannan zai taimaka maka ka san wasu dattawa Ki-ristoci, wa�anda suke kiwon garken Allah. (AyukanManzanni 20:28; 1 Bitrus 5:2, 3) Idan wa�annan dat-tawa suka fahimci cewa kana da muhimman sani naLittafi Mai Tsarki, kuma kana rayuwa cikin jituwa damizanan Allah, kuma da gaske kana so ka zama Mashai-din Jehobah, za su sanar da kai cewa ka cancanci ka fitahidimar fage ka zama mai shela da bai yi baftisma ba.

8. Mecece za ta motsa ka ka gaya wa wasu abin da ka koya?9, 10. (a) Ga wa za ka iya fara sanar da gaskiyar Littafi Mai Tsarki?(b) Menene za ka yi idan kana so ka yi aikin wa’azi da Shaidun Jeho-bah?

Baftisma da Kuma Dangantakarka da Allah 177

11 A wani �angare kuma, wata�ila ka bukaci ka yi wasucanje-canje a hanyoyin rayuwarka ko halayenka dominka cancanci fita wa’azi. Wa�annan za su ha�a da wasu ay-yuka da kake yi a �oye. Hakika, kafin ka ce za ka zamamai shela da bai yi baftisma ba, kana bukatar ka rabuda yin zunubai masu tsanani, kamar su lalata, maye, dashan miyagun �wayoyi.—1 Korinthiyawa 6:9, 10; Galati-yawa 5:19-21.

TUBA DA JUYOWA12 Dole ne a �auki wasu matakai kafin a cancanci yin

baftisma. Manzo Bitrus ya ce: “Ku tuba fa, ku juyo, do-min a shafe zunubanku.” (Ayukan Manzanni 3:19) Tubayin nadama ne matu�a domin wani abin da ka yi. Tubata dace idan mutum ya yi rayuwa ta lalata, kuma dolene ko da mutum ya yi rayuwa mai tsabta. Me ya sa? Do-min dukan mutane masu zunubi ne kuma muna bukatargafarar Allah. (Romawa 3:23; 5:12) Kafin ka yi nazarinLittafi Mai Tsarki, ba ka san ko menene nufin Allah ba.Saboda haka, ba zai yiwu ka rayu cikin cikakkiyar jituwada nufinsa ba. Domin haka, tuba ta wajaba.

13 Dole ne kuma juyowa ya bi tuba. Dole ne ka yi abinda ya fice nadama kawai. Kana bukatar ka guji irin ra-yuwarka ta d

¯a kuma ka �uduri niyyar yin abin da yake

nagari daga yanzu har zuwa gaba. Tuba da juyowa mata-kai ne da dole ka �auka kafin ka yi baftisma.

KE�E KANKA14 Da wani mataki mai muhimmanci da za ka �auka

11. Wa�anne canje-canje wasu za su bukaci su yi domin su cancancifita wa’azi?12. Me ya sa tuba ta wajaba?13. Menene juyowa?14. Wane mataki ne mai muhimmanci dole ne ka �auka kafin ka yibaftisma?

178 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

kafin ka yi baftisma. Dole ne ka ke�e kanka ga JehobahAllah.

15 Sa’ad da ka ke�e kanka ga Jehobah Allah a cikin ad-du’a, ka yi masa alkawari ne cewa za ka bauta masa shika�ai har abada. (Kubawar Shari’a 6:15) Me ya sa, mu-tum zai so ya yi haka? Alal misali, a ce wani mutumyana neman wata yarinya da aure. Da zarar ya fahim-ci tana da halin kirki, hakan nan zai ci gaba dasha’awarta. Bayan wani �an lokaci, zai ce zai aure ta.Hakika, yin aure yana nufin zai �ara hakkin da zai �au-ka a gare ta. Amma �auna za ta motsa shi ya �aukiwannan hakkin.

16 Sa’ad da ka fahimci kuma ka �aunaci Jehobah, za kamotsa ka bauta masa ba tare da ja da baya ba kokuma kafa wani iyaka ga bautarsa. Duk wanda yake soya bi �an Allah, Yesu Kristi, dole ne ya yi “musun kan-sa.” (Markus 8:34) Muna musun kanmu ta wajen tabbatacewa babu wani muradinmu ko kuma makasudi da yatare hanyar yi wa Allah cikakkiyar biyayya. Kafin a yimaka baftisma yin nufin Allah dole ne ya kasance aini-hin ma’anar rayuwarka.—1 Bitrus 4:2.

CIM MA TSORON KASAWA17 Wasu suna �in ke�e kansu ga Jehobah domin suna

tsoron �aukan irin wannan mataki mai muhimmanci.Suna iya tsoron ba da lissafi ga Allah domin sun ke�ekansu sun zama Kiristoci. Suna tsoron kada su gaza suba Jehobah kunya, suna tunanin cewa ya fi kada su ke�emasa kansu.

18 Sa’ad da ka koyi ka �aunaci Jehobah, za ka motsa

15, 16. Menene yake nufi ka ke�e kanka ga Allah, kuma menene yakemotsa mutum ya yi haka?17. Me ya sa wasu suke �in ke�e kansu ga Allah?18. Menene zai motsa ka ka ke�e kanka ga Jehobah?

Baftisma da Kuma Dangantakarka da Allah 179

ka ke�e masa kanka kumaka yi iya �o�arinka ka cikawannan. (Mai-Wa’azi 5:4) Bayan ka ke�e masa kanka,tabbatacce ne za ka so ka ‘cancanci bautar Ubangiji, kanafaranta masa ta kowane fanni.’ (Kolossiyawa 1:10) Do-min �aunarka ga Allah, ba za ka yi tunanin cewa yana dawuya a yi nufinsa ba. Babu shakka za ka yarda da abinda manzo Yohanna, ya rubuta: “�aunar Allah ke nan, mukiyaye dokokinsa; dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba.”—1 Yohanna 5:3.

19 Ba dole sai ka kamilta ba kafin ka ke�e kanka ga Al-lah. Jehobah ya san kasawarka kuma ba ya bukatar ka yi

19. Me ya sa bai kamata ka ji tsoron ke�e kanka ga Allah ba?

Samun cikakken sanina Kalmar Allah mataki nemai muhimmnanci domin

cancanta ga baftisma

Bangaskiya ya kamata tamotsa ka ka gaya wa

mutane abin da ka gaskata

abin da ba za ka iya yi ba. (Zabura 103:14) Yana so ka yinasara kuma zai tallafa maka kuma ya taimake ka. (Isha-ya 41:10) Ka tabbata cewa idan ka dogara ga Jehobah dadukan zuciyarka, shi kuma “za ya daidaita hanyoyinka.”—Misalai 3:5, 6.

KA NUNA KE�E KANKA TA WAJEN BAFTISMA20 Tuna abin da muka tattauna yanzu zai taimake ka

20. Me ya sa ke�e kai ga Jehobah ba zai ci gaba da kasancewa abinsirri ba?

Ka ke�e kanka gaAllah kuwa cikin

addu’a? Baftisma tana nufinmutuwa a hanyar

rayuwarka ta d¯

a da kumakasancewa a raye domin

yin nufin Allah

Baftisma da Kuma Dangantakarka da Allah 181

ka ke�e kanka ga Jehobah cikin addu’a. Duk wanda yake�aunar Allah dole ne ‘da baki ya yi shaida zuwa ceto.’(Romawa 10:10) Ta yaya za ka yi wannan?

21 Ka sanar da mai tsara ayyukan rukunin dattawa naikilisiyarku cewa kana so ka yi baftisma. Zai shirya wasudattawa su maimaita wasu tambayoyi game da koyarwamasu muhimmanci na Littafi Mai Tsarki. Idan wa�annandattawa sun yarda cewa ka cancanta, za su gaya makacewa za ka yi baftisma sa’ad da zarafi ya samu.� Ana ba dajawabi da yake ba da bayani game da ma’anar baftisma airinwannan lokaci. Sai mai jawabin ya gayyaci dukan wa-�anda suke da niyyar baftisma su amsa tambayoyi biyumasu sau�i, wannan hanya ce ta ‘shaidar’ bangaskiyarsu.

22 Baftismar ce take nuna a fili cewa kai mutum ne daya ke�e kansa ga Allah kuma a yanzu ka zama MashaidinJehobah. Ana nitsar da masu niyyar baftisma cikin ruwasu nuna a fili sun ke�e kansu ga Jehobah.

MA’ANAR BAFTISMARKA23 Yesu ya ce za a yi wa mabiyansa baftisma da “sunan

Uba, da na �a, da na Ruhu Mai-Tsarki.” (Matta 28:19)Wannan yana nufin cewa wanda yake da niyyar baftis-ma ya fahimci ikon Jehobah Allah da kuma Yesu Kristi.(Zabura 83:18; Matta 28:18) Kuma ya fahimci matsayi dakuma ayyukan ruhu mai tsarki na Allah, ko kuma ikonaikinsa.—Galatiyawa 5:22, 23; 2 Bitrus 1:21.

24 Amma, baftisma ba wanka ba ne kawai. Alama ce

� Ana yin baftisma shekara shekara a manyan tarurruka da kumataron gunduma na Shaidun Jehobah.

21, 22. Taya za ka ‘yi shaidar’ bangaskiyarka?23. Menene ake nufi a yi baftisma da “sunan Uban, da na �a, da naRuhu Mai-Tsarki”?24, 25. (a) Baftisma alamar menene ne? (b) Wace tambaya ce takebukatar amsa?

182 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

ta wani abu mai muhimmanci. Nitsewa cikin ruwa ala-ma ce ta cewa ka mutu ga hanyar rayuwarka ta d

¯a.

Fito da kai daga cikin ruwa yana nuna cewa yanzukana raye domin ka yi nufin Allah. Ka tuna kuma cewaka ke�e kanka ga Jehobah Allah, ba ga aiki ba, ko kumawani tafarki, ko kuma wasu mutane, ko kuma �ungi-ya. Ke�ewar kanka da kuma yin baftisma mafari nena abokantaka da Allah, da kuma kasancewa amininsa.—Zabura 25:14.

25 Baftisma ba ta ba da tabbacin ceto. Manzo Bulus yarubuta: “Ku yi aikin cetonku da tsoro da rawan jiki.” (Fi-libbiyawa 2:12) Baftisma mafari ne kawai. Tambayar itace, Ta yaya za ka kasance cikin �aunar Allah? Babin muna gaba zai amsa wannan tambayar.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

ˇ Baftisma ta Kiristoci ta �unshi nutsarwa cikinruwa, ba yafa ruwa ba kawai.—Matta 3:16.

ˇ Matakai da suke kai wa ga baftisma suna fa-rawa ne da neman sani da kuma nunabangaskiya ta wajen tuba da juyowa, da kumake�e kai ga Allah.—Yohanna 17:3; AyukanManzanni 3:19; 18:8.

ˇ Domin ka ke�e kanka ga Jehobah, dole neka yi musun kanka, kamar yadda mutanesuka yi musun kansu domin su bi Yesu.—Markus 8:34.

ˇ Baftisma alama ce ta mutuwa ga hanyar ra-yuwa ta da da kuma kasancewa a raye dominyin nufin Allah.—1 Bitrus 4:2.

Baftisma da Kuma Dangantakarka da Allah 183

KA YI tunani kana tafiya a cikin hadari maiiska. Gari ya yi duhu. Aka fara wal�iya, araduya fara kara, aka fara ruwa kamar da bakinkwarya. Ka fara sauri kana neman mafaka. Ananbakinhanya, ka ga gida.Wurin zai zamamaka da muhimmanci!

2 Muna rayuwa ne a lokacin hadari maiiska. Yanayin duniya yana da�a �aci. Ammada mafaka, da za ta k

¯are mu daga rauni

na dindindin. Mecece wannan? Ka lura daabinda LittafiMaiTsarki yake koyarwa: “Zance da Ubangiji, shi ne mafakata da marayatakuma; Allahna, a gareshi ni ke dogara.”—Za-bura 91:2.

3 Ka yi tunanin wannan! Jehobah, Maha-licci, kuma Mamallakin sararin samaniya,zai zama maka mafaka mai k

¯ariya. Zai iya

k¯are mu domin ya fi kowa da kome da zai

iya yi mana rauni �arfi. Ko ma mun samirauni, Jehobah yana iya magance wannan.

1, 2. A ina za mu sami mafaka mai kyau a yau?3. Ta yaya za mu mai da Jehobah mafakarmu?

BABI NA GOMA SHA TARA

Ka Tsare Kanka Cikin�aunar Allah

Menene yake nufi a �aunaci Allah?

Ta yaya za mu tsare kanmu cikin �aunar Allah?

Ta yaya Jehobah zai saka wa wa�andasuka kasance cikin �aunarsa?

Za ka maida Jehobah

mafakanka acikin wannan

lokaci maihadari da iska?

Ta yaya za mu mai da Jehobah mafakarmu? Muna buka-tar mu dogara a gare shi. Bugu da �ari, Kalmar Allah taaririce mu: “Ku tsare kanku cikin �aunar Allah.” (Yahu-da 21) Hakika, muna bukatar mu tsare kanmu cikin�aunar Allah, muna kyautata dangantakarmu da Ubanmuna sama. Da haka muna iya tabbata cewa shi mafaka ne agare mu. Amma ta yaya za mu iya �ulla wannan danganta-kar?

KA FAHIMCI KUMA KA AMSA �AUNAR ALLAH4 Domin mu tsaya ga �aunar Allah, muna bukatar mu fa-

himci yadda Jehobah ya nuna �aunarsa a gare mu. Ka yitunanin wasu koyarwar Littafi Mai Tsarki da ka koya da tai-makon wannan littafin. Tun da Mahalicci ne, Jehobah yaba mu duniya ta zama mana gida mai ban sha’awa. Kumaya cika ta da abinci da ruwa mai dumbin yawa, ma’adinai,dabbobi, da kuma kyawawanwurare. A matsayinMawallafinLittafi Mai Tsarki, Allah ya bayyana mana sunansa da kumahalayensa. �ari ga haka, Kalmarsa ta nuna cewa ya aiko da�ansa da yake �auna zuwa duniya, ya �yale shi ya wahalakuma ya mutu dominmu. (Yohanna 3:16) Menene wannankyauta take nufi a gare mu? Ta ba mu bege na rayuwa maikyau a nan gaba.

5 Begenmu har ila ya dangana ne kuma bisa wani abin daAllah ya yi. Jehobah ya kafa gwamnati a sama, Mulkin Al-masihu. Zai kawo �arshen dukan wahaloli ba da da�ewa bakuma ya mai da duniya aljanna. Ka yi tunani! Za mu rayu anan cikin salama da farin ciki har abada. (Zabura 37:29) Ayanzu, Allah yana yi mana ja-gora a kan yadda za mu rayua hanya mafi kyau. Kuma ya yi mana kyautar addu’a, han-yar magana da shi. Wa�annan wasu hanyoyi ne da Jehobahya nuna �auna ga dukan mutane kuma musamman ma agare ka.

4, 5. A wa�anne hanyoyi ne Jehobah ya nuna yana �aunarmu?

Ka Tsare Kanka Cikin �aunar Allah 185

6 Tambaya mai muhimman-ci da ya kamata ka yi shi ne:Ta yaya zan amsa �aunar da Je-hobah yake yi mini? Mutane dayawa za su ce, “Ni ma zan nunaina �aunar Jehobah.” Kai ma

haka kake ji? Yesu ya ce wannandoka ita ta fi kowace: “Ka yi �aunar Uban-

giji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukanazancinka.” (Matta 22:37) Hakika kana da dalilai masu yawana �aunar Jehobah Allah. Yadda kake ji shi ne ake nufi da�aunar Jehobah da dukan zuciyarka, ranka, da kuma hanka-linka?

7 Kamar yadda aka kwatanta a cikin LittafiMaiTsarki, �au-nar Allah ta wuce motsin zuciya kawai. Hakika, jin muna�aunar Jehobah yana da muhimmanci, wannan motsin zu-ciyar farkon �auna ta gaskiya ce kawai. �wallon mangwarone yake girma ya zama itacen mangwaro. Amma idan kanaso ka sha mangwaro, sai wani ya ba ka �wallon, hakan zaiishe ka? Da �yar! Haka nan, jin kana �aunar Jehobah Allahmafarine kawai. LittafiMaiTsarki yana koyarwa: “�aunarAl-lah ke nan, mu kiyaye dokokinsa: dokokinsa fa ba su da banciwo ba.” (1 Yohanna 5:3) Domin ta kasance na gaskiya �au-nar Allah dole ne ta ba da amfanimasu kyau.Dole ne a nunata cikin ayyuka.—Matta 7:16-20.

8 Munanuna �aunarmugaAllah sa’ad damuka kiyaye do-kokinsa kuma muka bi mizanansa. Ba shi da wuya a yi haka.Maimakon su kasance matsananta, Jehobah ya tsara su nesu taimake mu mu yi rayuwa mai kyau, mai farin ciki, maigamsarwa. (Ishaya 48:17, 18) Ta wajen rayuwa cikin jituwada ja-gorar Jehobah, muna nuna wa Ubanmu na sama cewa

6. Ta yaya za ka amsa �auna da Jehobah ya nuna maka?7. Motsin zuciya ce kawai �aunar Allah? Ka yi bayani.8, 9. Ta yaya za mu nuna �aunarmu ga Allah kuma mu nuna munayi masa godiya?

Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

muna godiya �warai domindukan abubuwa da ya yi domin-mu. Abin ba�in ciki, mutane �alilan ne a duniya a yau sukenuna irin wannan godiyar. Bai kamata mu zama masu bu-tulci ba, kamar wasu mutane da suka rayu sa’ad da Yesu yakeduniya. Yesu ya warkar da kutare goma, amma �aya ne ka-wai ya dawo ya yi masa godiya. (Luka 17:12-17) Hakika, zamu so mu zama kamar mai godiyan, ba kamar marasa godi-yan ba!

9 To, menene dokokin Jehobah da muke bukatar mu kiya-ye? Mun riga mun tattauna wasunsu cikin wannan littafin,amma bari mu maimaita wasu ka�an. Kiyaye dokokin Allahzai taimake mu mu tsare kanmu cikin �aunar Allah.

KA KUSACI JEHOBAH SOSAI10 Koyo game da Jehobah mataki ne na �aya na kusantar-

sa. Abu ne da bai kamata ya �are ba. Idan kana waje a cikinsanyin dare kana �uma jikinka da wuta, za ka

10. Ka yi bayanin abin da ya sa yake da muhim-manci mu ci gaba da �ara sani game da JehobahAllah.

Kamar wuta, �aunarka gaJehobah tana bukatar a ri�arura ta domin ta ci gaba da ci

Ka Tsare Kanka Cikin �aunar Allah 187

bar wutar ta lafa ne ta mutu? A’a. Za ka ci gaba da �ara itacedomin wutar ta ci gaba da kamawa. Wata�ila ka dogara nema a kan wutar! Kamar yadda itace ke sa wuta ta ci, haka,“saninAllah” yake �arfafa �aunarmuga Jehobah.—Misalai 2:1-5.

11 Yesu yana so mabiyansa su ci gaba da �aunar Jehobahda kuma gaskiyar Kalmarsa mai tamani. Bayan ya tashi dagamatattu, Yesu ya koyar da almajiransa biyu game da wasuannabce-annabce a Nassosin Ibrananci da suka cika a kansa.Menene sakamakon haka? Daga baya suka ce: “Zuciyarmuba ta �una daga cikinmu ba, sa’anda yana yi mamu zance akan hanya, yana bayyana mamu littattafai?”—Luka 24:32.

12 Sa’ad da ka koyi abin da Littafi Mai Tsarki yake koyar-wa da gaske, shin zuciyar ka ba ta yi annuri ba ne, ba ta cikada himma, da �auna ga Allah ba? Hakika haka yake. Mutaneda yawa suna jin haka. �alubalen yanzu shi ne ka ci gaba dawannan �auna kuma ka sa ta �arfafa. Ba ma so mu bi yayinduniya ta yau. Yesu ya annabta: “�aunar yawancin mutaneza ta yi sanyi.” (Matta 24:12) Ta yaya za ka kiyaye �aunarkaga Jehobah da kuma Littafi Mai Tsarki daga yin sanyi?

13 Ka ci gaba da �ara sanin Jehobah Allah da kuma YesuKristi. (Yohanna 17:3) Ka yi bimbini ko kuma tunani sosai, akan abin da ka koya daga Kalmar Allah ka tambayi kanka:‘Menene wannan yake koya mini game da Jehobah Allah?Wa�anne �arin dalilai wannan ya ba ni in �aunace shi dadukan zuciyata, hankalina, da kuma raina?’ (1 Timothawus4:15) Irinwannanbimbini zai ri�a rurawutar �aunarka ga Je-hobah.

14 Wata hanyar rura wutar �aunarmu ga Jehobah ita ce

11. Yaya koyarwar Yesu ya shafi mabiyansa?12, 13. (a) A tsakanin yawancin mutane a yau, menene ya faru da�aunar Allah da kuma Littafi Mai Tsarki? (b) Ta yaya za mu kiyaye �au-narmu daga yin sanyi?14. Ta yaya addu’a za ta taimake mu mu rura wutar �aunarmu ga Je-hobah?

188 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

addu’a a kai a kai. (1 Tassalunikawa 5:17) A Babi na 17 nawannan littafin, mun koyi cewa addu’a kyauta ce mai mu-himmanci daga Allah. Kamar yadda dangantaka tsakaninmutane take ci gaba domin sadawa da ke tsakaninsu, hakanandangantakarmuda Jehobah za ta kasance a raye sa’ad damuka yi addu’a a gare shi a kai a kai. Yana da muhimman-ci kada addu’armu ta zama je-ki-na-yi-ki, kalmomi kawai damuke furtawa babu motsin zuciya ko ma’ana. Muna bukatarmu yi magana ga Jehobah kamar yadda yaro zai yi maga-na da ubansa abin �auna. Hakika, muna bukatar mu yimagana da daraja, magana ta gaskiya daga zuciyarmu. (Za-bura 62:8) Nazarin Littafi Mai Tsarki da kanmu da kumaaddu’a daga zuciyarmu �angarorin bautarmu ne masu mu-himmanci, kuma suna taimakonmu mu tsare kanmu cikin�aunar Allah.

KA YI FARIN CIKI A BAUTARKA15 Nazarin Littafi Mai Tsarki na kanmu �angaren bauta ne

da muke yi a gida. Amma bari yanzu mu bincika wani �an-garen bautarmu da muke yi a fili: yin magana da wasu gameda abin da muka gaskata. Ka riga ka sanar da wasu game dagaskiya ta Littafi Mai Tsarki kuwa? Idan haka ne, to, ka moregata mai ban sha’awa. (Luka 1:74) Sa’ad da muka sanar damutanegaskiyadamukakoya gameda JehobahAllah,munayinwani aikinemaimuhimmancida akabaiwadukanKiris-toci—aikin wa’azin bisharar Mulkin Allah.—Matta 24:14; 28:19, 20.

16 Manzo Bulus ya �auki hidimarsa da muhimmanci, yakira ta kaya mai daraja. (2 Korinthiyawa 4:7) Yin magana damutane game da Jehobah Allah da kuma nufinsa shi ne aikimafikyauda za kayi.Hidimace gaMaigidanakirki, kuma zata kawo lada masu kyau. Ta wajen saka hannu cikin wannanaikin, kana taimakon mutane masu zukatan kirki su kusaci

15, 16. Me ya sa za mu �auki aikin wa’azin Mulki gata ce da kumakaya mai daraja?

Ka Tsare Kanka Cikin �aunar Allah 189

Ubanmu na sama kuma su kasance a kan hanyar zuwa rai!Wane aiki zai fiwannangamsarwa? �ari ga haka, yin shaidarJehobah da kuma Kalmarsa tana �ara bangaskiyarmu kumatana �arfafa �aunar da muke yi masa. Kuma Jehobah yanayin farin ciki da �o�arce-�o�arcenka. (Ibraniyawa 6:10) Du-

Jehobah yana so ka more “raiwanda shi ke hakikanin rai.”

Za ka more kuwa?

190 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

�ufa cikin irinwannan aikin yana taimakonka ka tsaya a kan�aunar da Allah yake mana.—1 Korinthiyawa 15:58.

17 Yana da muhimmancimu tuna cewa aikinwa’azin Mul-ki aiki ne na gaggawa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka yi wa’azinkalma; ka yi naciya.” (2 Timothawus 4:2) Me ya sa aikin yakeda gaggawa haka a yau? Kalmar Allah ta gaya mana: “Babbarranar Ubangiji ta kusa, kurkusa ce, tana kuwa gaggabta �wa-rai.” (Zephaniah 1:14) Hakika, lokacin yana zuwa da sauri daJehobah zai halaka wannan zamani. Mutane suna bukatara yi musu kashedi! Suna bukatar su sani cewa yanzu lokaciya yi da za su za�i Jehobah ya zama Mamallakinsu. �arshen“ba za ta yi jinkiri ba.”—Habakkuk 2:3.

18 Jehobah yana so mu bauta masa a fili cikin cu�anya daKiristoci na gaskiya. Abindaya sa kenanKalmarsa ta ce: “Barikumamu lurada junadominmu tsokani juna zuwaga �aunada nagargarun ayyuka; kada mu fasa tattaruwanmu, kamaryaddawa�ansu sun sabayi, ammamugarga�adda juna; ballefa yanzu, da kuna ganin ranan nan tana gusowa.” (Ibraniya-wa 10:24, 25) Sa’ad da muka taru da ’yan’uwanmu masu bia taron Kiristoci, muna samun zarafi na bautawa Allah kumamu yabe shi. Muna kuma gina wasu muna �arfafa su.

19 Sa’ad da muka yi hul�a da wasu masu bauta wa Jeho-bah, muna �arfafa �auna da kuma abota a cikin ikilisiya.Yana da muhimmanci kuma mu ri�a kula da halayen kir-ki na juna, kamar yadda Jehobah yake kula da halayenmuna kirki. Kada ka zaci cewa ’yan’uwanka Kiristoci kamilai ne.Ka tuna cewa kowa manyantarsa na ruhaniya ya bambanta,kuma dukanmu muna yin kuskure. (Kolossiyawa 3:13) Ka yi�o�ari ka �ulla abota da wa�anda suke �aunar Jehobah �wa-rai, za ka ga cewa kana �aruwa ruhaniya. Hakika, bauta waJehobah tare da ’yan’uwanka maza da mata na ruhaniya zai

17. Me ya sa hidimar Kirista take da gaggawa a yau?18. Me ya sa za mu bauta wa Jehobah a fili cikin cu�anya da Kiristo-ci na gaskiya?19. Ta yaya za mu �arfafa �auna a cikin ikilisiya ta Kirista?

Ka Tsare Kanka Cikin �aunar Allah 191

taimake ka ka tsare kanka cikin �aunar Allah. Ta yaya Jeho-bah yake ba da lada ga wa�anda suka bauta masa da amincikuma suke tsare kansu cikin �aunarsa?

KA CANCANCI “RAI WANDA SHIKE NA HAKIKANIN RAI”

20 Jehobah yana bai wa bayinsa masu aminci ladar rai,amma wane irin rai? To, kana rayuwa kuwa a yanzu? Ya-wancinmu za mu ce hakika kuwa. Domin muna numfashi,muna cimuna sha. Babu shakka,muna raye. Kuma a lokacinda muke farin ciki, muna iya ma ce, “Kai muna more rayu-wa da gaske!” Amma dai, Littafi Mai Tsarki ya nuna a watahanya mai muhimmanci cewa babu mutumin da yake rayeda gaske.

21 Kalmar Allah ta aririce mu mu “ruski rai wanda shike hakikanin rai.” (1 Timothawus 6:19) Wa�annan kalmo-mi sun nuna cewa “rai wanda shi ke na hakikanin” waniabu ne da muke begen samu a nan gaba. Hakika, sa’adda muka zama kamilai, za mu zama masu rai a cikakkiyarma’anarta, dominzamurayukamar yaddaAllahyanufa tunfarko. Sa’ad da muke raye cikin aljanna a duniya da cikak-ken koshin lafiya, salama, farin ciki, a �arshe za mu more“rai wanda shi ke hakikanin rai”—rai madawwami. (1 Timo-thawus 6:12) Wannan ba bege ba ne mai ban sha’awa?

22 Ta yaya za mu “ruski rai wanda shi ke hakikanin rai”? Acikinwasi�ar, Bulus ya aririci Kiristoci “su yi alheri” da kuma“mawadata cikin kyawawan ayyuka.” (1 Timothawus 6:18)To, a bayyane yake cewa ya dangane ne bisa yadda muka yiamfani da gaskiya da muka koya daga cikin Littafi Mai Tsar-ki. Amma Bulus yana nufi ne cewa za mu sami “rai wandashi ke hakikanin rai” tawajenyin ayyuka nagari? A’a, dominirinwannanbege ya dangana ne bisa samun“alherin”Allah.

20, 21. Menene “rai wanda shi ke hakikanin rai,” kuma me ya sa begene mai ban sha’awa?22. Ta yaya za ka “ruski rai wanda shi ke hakikanin rai”?

192 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

(Romawa 5:15) Duk da haka, Jehobah yana farin cikin ba dalada ga wa�anda suka bauta masa cikin aminci. Yana son yaga ka sami “rai wanda shi ke hakikanin rai.” Irin wannan raimadawwami na farin ciki, da salama, yana gaban wa�andasuka tsaya a kan �aunar da Allah yake yi musu.

23 Yana da kyau kowanenmu ya tambayi kansa, ‘Ina bautawa Allah a hanyar da ya kafa kuwa cikin Littafi Mai Tsar-ki?’ Idan mun tabbata, kowace rana, cewa amsar mu e ce, to,muna kan hanya da take daidai. Za mu yi ta tabbatawa cewaJehobah mafakanmu ne. Zai kuma kare mutanensa masuaminci a cikinwa�annankwanakina�arshenabala’inawan-nan zamani. Jehobah kuma zai kai mu cikin sabuwar duniyamai �aukaka da ta yi kusa. Zai kasance abin farin ciki mu gawannan lokaci! Kuma za mu yi farin cikin mun za�i abin dayafiawannankwanakina�arshe! Idankaza�iwannanayan-zu, zakamore“raiwanda shikehakikanin rai,” rayuwakamaryadda Jehobah Allah ya nufa a cikin dukan dawwama!

23. Me ya sa yake da muhimmanci mu tsaya a kan �aunar da Allahyake yi mana?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

ˇ Muna nuna �auna ta gaskiya ga Allah ta wa-jen kiyaye dokokinsa da kuma bin mizanansa.—1 Yohanna 5:3.

ˇ Nazarin Kalmar Allah, yin addu’a ga Jehobahdaga zukatanmu, koyar da mutane game dashi, da kuma bauta masa a taron Kiristoci zasu taimake mu mu tsare kanmu cikin �aunarAllah.—Matta 24:14; 28:19, 20; Yohanna 17:3;1 Tassalunikawa 5:17; Ibraniyawa 10:24, 25.

ˇ Wa�anda suka tsare kansu cikin �aunar Allahsuna da begen more “rai wanda shi ke hakika-nin rai.”—1 Timothawus 6:12, 19; Yahuda 21.

Ka Tsare Kanka Cikin �aunar Allah 193

BATU SHAFI

Ma’anar Sunan Allah da Yadda Ake Amfani da Shi � � � � � � � � 195

Yadda Annabcin Daniel ya Bayyana Zuwan Almasihu � � � � � � 197

Yesu Kristi—Almasihu da Aka Yi Alkawarinsa � � � � � � � � � � � � 199

Gaskiya Game da Uba, �a, da Kuma Ruhu Mai Tsarki � � � � � 201

Abin da Ya Sa Kiristoci naGaskiya ba Sa Amfani da Gicciye Wajen Bauta � � � � � � � � � � � 204

Jibin Maraice na Ubangiji—Farilla da Ke Daraja Allah � � � � � � 206

“Kurwa” da Kuma “Ruhu”—Menene Ainihi Ma’anar Wa�annan Kalmomi? � � � � � � � � � 208

Menene Sheol da Kuma Hades? � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � 212

Mecece Ranar Shari’a? � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � 213

1914—Shekara Mai Muhimmanci a AnnabcinLittafi Mai Tsarki � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � 215

Wanene Mika’ilu Shugaban Mala’iku? � � � � � � � � � � � � � � � � � 218

Gano “Babila Babba” � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � � 219

A Watan Disamba ne Aka Haifi Yesu? � � � � � � � � � � � � � � � � � � 221

Ya Kamata Ne Mu Kiyaye Ranaku Masu Tsarki? � � � � � � � � � � 222

RATAYE

A NAKA Littafi Mai Tsarki, yaya aka fassara Zabura 83:18? NewWorld Translation of the Holy Scriptures ya fassara shi haka:“Domin mutane su sani, kai wanda sunanka ne Jehobah, kaika�ai ne Ma�aukaki bisa dukan Duniya.” Wasu fassara na Lit-tafi Mai Tsarki ma sun fassara shi kusan haka. Duk da haka,fassara masu yawa sun cire sunan Jehobah, sun sauya shi da la-�abi irin su “Ubangiji” ko kuma “Madawwami.” Me ya kamataya kasance a wannan ayar? La�abi ko kuma sunan Jehobah?

Wannan ayar ta yi magana game da sunan. A Ibrananci naasali da aka rubuta Littafi Mai Tsarki dashi, suna marar na biyunsa ya bayyanaa nan. An rubuta shi haka ˘˙˘˝ (YHWH)da ba�a�en Ibrananci. A Hausa, ana ki-ran sunan “Jehobah” ne.Wannan sunanya bayyana ne kawai a aya �aya ta Litta-fi Mai Tsarki? A’a. Ya bayyana a rubutunainihi na Ibrananci sau 7,000!

Yaya muhimmancin sunan Allah? Ka yi la’akari da addu’aralama da Yesu Kristi ya koya mana. Ya fara ta da cewa: “Uban-mu wanda ke cikin sama, a tsarkake sunanka.” (Matta 6:9)Daga baya, Yesu ya yi addu’a: “Ya Uba, ka �aukaka sunanka.”Allah ya amsa daga sama, yana cewa: “Na rigaya na �aukakashi, kuma ni sake �aukaka shi.” (Yohanna 12:28) Babu shak-ka, sunan Allah yana da muhimmanci �warai. To, me ya sa,wasu masu fassara suka sake sunan da la�abi a Littafi Mai Tsar-ki da suka fassara?

Kamar dai dalilan biyu ne. Na farko, wasu suna da’awarcewa bai kamata a yi amfani da sunan ba tun da ba a sanyadda ake furta shi ba a yau. Ba a rubuta Ibrananci na da dawasula. Saboda haka, a yau babu wanda ya tabbata yadda mu-tanen zamanin Littafi Mai Tsarki suka furta YHWH. Amma, yakamata ne wannan ya hana mu amfani da sunan Allah? A za-manin Littafi Mai Tsarki, sunan nan Yesu wata�ila ana furta

Ma’anar Sunan Allahda Yadda Ake Amfani da Shi

˘˙˘˝Sunan Allahda ba�a�enIbrananci

195

shi ne Yeshua ko kuma Yehoshua—babu wanda zai iya tabba-tawa. Duk da haka, mutane a dukan duniya suna amfani dasuna Yesu yadda aka fi sabawa da shi a yarensu. Ba sa yin jin-kirin amfani da sunan domin ba su san yadda ake furta shi baa �arni na farko. Hakazalika, idan ka tafi wata �asa, za ka gacewayadda suke furta sunanka zai bambanta. Saboda haka, ra-shin tabbacin yadda ake furta sunan Allah a da ba dalili ba nena �in amfani da shi.

Wanidalili kumada akebayarwanacire sunanAllahdaga Lit-tafi Mai Tsarki shi ne tsohuwar al’adar Yahudawa. Yawancinsusun yi imani cewa bai kamata a furta sunan Allah ba. Wannanimani a bayyane yake cewa ya samo asalinsa ne daga rashin fa-himtar doka ta Littafi Mai Tsarki da ya ce: “Ba za ka kama sunanUbangiji Allahnka banza ba; gama Ubangiji ba za ya ku�utad-da wanda yana kama sunansa banza ba.”—Fitowa 20:7.

Wannan dokar ta hana kama sunan Allah a banza. Amma tahana kama sunan Allah ne da daraja? Ko ka�an. MarubutanLittafin Mai Tsarki na Ibrananci (“Tsohon Alkawari”) dukansu mutane ne masu aminci wa�anda suka kiyaye Dokar da Al-lah ya bai wa Isra’ila ta da. Duk da haka, suna kama sunanAllah sau da yawa. Alal misali, sun saka shi cikin zabura da ja-ma’a masu yawa suke rerawa lokacin bauta. Jehobah Allah yaumurci masu bauta masa su kira sunansa, kuma masu amincisun yi biyayya da hakan. (Joel 2:32; Ayukan Manzanni 2:21)Saboda haka, Kiristoci a yau ba sa �in kama sunan Allah da da-raja, kamar yadda Yesu ya yi.—Yohanna 17:26.

Masu fassarar Littafi Mai Tsarki sun yi kuskure mai tsana-ni wajen sauya sunan Allah da la�abi. Sun sa Allah ya kasanceyana da nesa kuma ba zai yiwu a �ulla dangantaka da shi ba,alhali kuma Littafi Mai Tsarki ya aririci mutane su yi �o�ari‘Allah ya amince da su.’ (Zabura 25:14 Littafi Mai Tsarki) Ka yitunaninwani amininka. Ta yaya za ku zama aminai idan ba kasan sunan abokinka ba? Hakazalika, sa’ad da aka bar mutanecikin duhu game da sunan Allah, Jehobah, ta yaya za su ku-saci Allah? Bugu da �ari, sa’ad da mutane ba sa kama sunanAllah, jahilai ne ga ma’anarsa mai ban mamaki. Menene ma’a-nar sunan Allah?

196 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

Allah da kansa ya yi bayani game da ma’anar sunansa ga ba-wansa mai aminci Musa. Sa’ad da Musa ya yi tambaya game dasunan Allah, Jehobah ya amsa yana cewa: “Zan Kasance yaddana ga dama.” (Fitowa 3:14; Rotherham) Saboda haka, Jehobahzai kasance dukan abin da ake bukata domin ya cika nufinsa.

Da a ce kana iya kasancewa dukan abin da ka ga dama. Dame za ka yi wa abokananka? Idan �aya daga cikinsu ya fa�a ra-shin lafiya, za ka zama likita domin ka yi masa magani. Idanwani kuma ya yi hasarar dukiyarsa, za ka zama mai arziki do-min ka taimake shi. Gaskiya ita ce, ba za ka iya yin haka ba.Hakika dukanmu. Sa’ad da ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki zaka yi mamakin ganin yadda Jehobah ya kasance dukan abinda ake bukata domin ya cika alkawuransa. Kuma yana farantamasa rai ya yi amfani da ikonsa ya amfani wa�anda suke �au-narsa. (2 Labarbaru 16:9) Wa�anda ba su san sunansa ba sun yihasarar wannan �angaren na mutuntakar Jehobah.

A bayyane yake cewa ya kamata a yi amfani da sunan Jeho-bah a cikin Littafi Mai Tsarki. Sanin ma’anarsa da kuma yinamfani da shi wajen bauta suna taimakawa �warai wajen ku-santar Ubanmu na sama, Jehobah.�

� Domin �arin bayani game da sunan Allah, ma’anarsa, da kuma dalilinda ya sa ya kamata a yi amfani da shi wajen bauta, dubi mujallar nan TheDivine Name That Will Endure Forever, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

Rataye 197

ANNABI Daniel ya rayu shekaru 500 kafin a haifi Yesu. Duk dahaka, Jehobah ya nuna wa Daniel bayani da ya taimaka wajennuna lokaci da za a shafa Yesu, ko kuma a na�a shi ya zamaAlmasihu, ko kuma Kristi. An gaya wa Daniel: “Ka sani fa, ka fa-himta kuma, tun daga loton fitowar doka a maida Urushalima,a gine ta kuma, har zuwan loton Masiya sarki, za a yi bakwaibakwai: cikin bakwai sattin da biyu.”—Daniel 9:25.

Yadda Annabcin Daniel ya BayyanaZuwan Almasihu

Domin mu fahimci lokacin da Almasihun zai zo, kana bu-katar ka sani da farko lokacin da zai kai ga zuwan Almasihu.Annabcin ya ce, “daga loton fitowar doka a maida Urushali-ma.” Yaushe ne aka ba da wannan “doka”? In ji MarubucinLittafi Mai Tsarki Nehemiya, an ba da dokar a sake ginaganuwa a kewaye Urushalima “cikin shekara ta ashirin ta Ar-taxerxes sarki.” (Nehemiah 2:1, 5-8) ’Yan tarihi sun tabbatarda cewa shekara ta 474 K.Z., ita ce cikakkiyar shekara ta far-ko ta Artaxerxes a gadon sarauta. Saboda haka, shekararsa taashirin a sarauta ita ce shekara ta 455 K.Z. A yanzu mun fa-

198 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

“BAKWAI HAR SABA’IN”

Shekaru 490

Bakwai sau 7(Shekaru 49)

Bakwai sau 62(Shakaru 434)

Bakwai sau 1(Shekara 7)

455 406 & K.Z. A.Z. ) 29 33 36

“Doka amaida

Urushalima”

An s¯

ake ginaUrushalima

Almasihuya zo

“Datse”Almasihu

�arshen“bakwai har

saba’in”

himci farkon lokacin Annabcin Daniel na Almasihu, shekarata 455 K.Z.

Daniel ya nuna tsawon lokacin da zai �auka kafin “Masiyasarki” ya zo. Annabcin ya ce “za a yi bakwai bakwai: ci-kin bakwai sattin da biyu”—gaba �aya sun zama bakwai 69.Yaya tsawon wannan lokaci yake? Yawancin fassarar LittafiMai Tsarki sun fahimci cewa wa�annan ba bakwai na kwanabakwai ba ne, amma bakwai ne na shekaru. Wato, kowa-ne bakwai yana nufin shekara bakwai. Yahudawa da suna saneda wannan yanayin na bakwai na shekaru. Alal misali, sunakiyaye Asabarci na shekara bayan kowace shekara bakwai. (Fi-towa 23:10, 11) Saboda haka, bakwai 69 na annabci shekaru 7ne sau 69, ko kuma shekaru 483.

Yanzu abin da za mu yi shi ne mu lissafa. Idan muka �irgashekaru 483 daga shekara ta 455 K.Z., zai kai mu ga shekara ta29 A.Z. Wannan shi ne daidai lokaci da Yesu ya yi baftismaya zama Almasihu!� (Luka 3:1, 2, 21, 22) Wannan ba cikar an-nabcin Littafi Mai Tsarki ba ne mai ban mamaki?

� Daga shekara ta 455 K.Z., zuwa shekara ta 1 K.Z., shekaru 454 ne. Dagashekara ta 1 K.Z., zuwa shekara ta 1 A.Z., shekara �aya ce (babu shekara tasifili). Kuma daga shekara ta 1 A.Z., zuwa shekara ta 29, shekaru 28 ne. Idanmuka ha�a wa�annan adadi uku wuri �aya za mu sami shekaru 483. An‘datse’ Yesu a shekara ta 33 A.Z., a cikin bakwai na 70. (Daniel 9:24, 26)Dubi littafin nan Pay Attention to Daniel’s Prophecy! babi na 11, da kumaInsight on the Scriptures, Littafi na 2, shafuffuka na 899-901. Shaidun Jeho-bah ne suka wallafa su.

DOMIN a taimake mu mu gane Almasihu, Jehobah Al-lah ya huri annabawan Littafi Mai Tsarki da yawa su ba dabayani game da haihuwa, hidima, da kuma mutuwar wan-nan Mai Ceto. Dukan wa�annan annabce-annabce na LittafiMai Tsarki sun cika a kan Yesu Kristi. Abin ban sha’a-wa, daidai suke a bayaninsu. Alal misali, bari mu bincika

Yesu Kristi—Almasihu da Aka Yi Alkawarinsa

Rataye 199

wasu annabce-annabce da suka fa�i abubuwa da suka shafihaihuwa da kuma yaranta na Almasihu.

Annabi Ishaya ya annabta cewa Almasihu zai fito daga zuri-yar Sarki Dauda. (Ishaya 9:7) Kuma hakika an haifi Yesu dagazuriyar Dauda.—Matta 1:1, 6-17.

Mi�ah wani annabin Allah, ya annabta cewa wannan �an

ANNABCE-ANNABCE GAME DA ALMASIHU

AUKUWA ANNABCI CIKA

Haifa a zuriyar Yahuda Farawa 49:10 Luka 3:23-33

Budurwa za ta haife shi Ishaya 7:14 Matta 1:18-25

Daga zuriyar Sarki Dauda Ishaya 9:7 Matta 1:1, 6-17

Jehobah ya furta cewa �ansa ne Zabura 2:7 Matta 3:17

Ba a gaskata shi ba Ishaya 53:1 Yohanna 12:37, 38

Ya shiga Urushalima a kan jaki Zechariah 9:9 Matta 21:1-9

Abokinsa na kusa ya ci amanarsa Zabura 41:9 Yohanna 13:18, 21-30

An ci amanarsa domin zinariya 30 Zachariah 11:12 Matta 26:14-16

Ya yi shiru a gaban masu zarginsa Ishaya 53:7 Matta 27:11-14

An jefa �uri’a domin tufafinsa Zabura 22:18 Matta 27:35

An zazzage shi a kan gungume Zabura 22:7, 8 Matta 27:39-43

Ba a fasa �asusuwansa ko �aya ba Zabura 34:20 Yohanna 19:33, 36

An binne shi da masu arziki Ishaya 53:9 Matta 27:57-60

An ta da shi kafin ya ru�e Zabura 16:10 Ayukan Manzanni 2:24, 27

Yana tsaye dama ga Allah Zabura 110:1 Ayukan Manzanni 7:56

200 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

zai zama sarki a �arshe kuma ya ce za a haife shi a “Bai’-talahmi Ephrathah.” (Mi�ah 5:2) Sa’ad da aka haifi Yesu,akwai garuruwa biyu a Isra’ila da ake kira Bai’talahmi.�aya tana kusa da Nazarat a yankin arewaci na �asar, �a-yar kuma tana kusa da Urushalima ta Yahuda. Bai’talahmida ke kusa da Urushalima a da ana kiranta Ephrathah. Anhaifi Yesu a wannan garin, daidai yadda aka ce a annabcin!—Matta 2:1.

Wani annabci na Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa Allahzai kira �ansa daga “Masar.” An �auki Yesu zuwa Masar. Anmai da shi bayan mutuwar Herod, da haka ya cika annabcin.—Hosea 11:1; Matta 2:15.

A taswira da ke shafi na 200, nassosi da aka jere a �ar�ashin“Annabci” suna �auke da bayani dalla-dalla game da Almasi-hun. Don Allah ka gwada da nassosi da aka jera a �ar�ashin“Cika.” Yin haka zai sake �arfafa bangaskiyarka game da gas-kiyar Kalmar Allah.

Sa’ad da kake bincika wa�annan nassosin, ka tuna cewawa�annan annabci ne da aka rubuta su shekaru �arurruwakafin a haifi Yesu. Yesu ya ce: “Dukan abin da aka rubuta akaina a cikin Attaurat ta Musa, da Annabawa, da Zabura, dolea cika su.” (Luka 24:44) Kamar yadda za ka gani a cikin nakaLittafi Mai Tsarki, hakika sun cika!

MUTANE da suka yarda da koyarwar Allah-Uku-Cikin-�ayasuka ce Allah ya �unshi mutane uku—Uba, �a, da kuma RuhuMai Tsarki. Kowane cikin wa�annan uku an ce daidai suke,dukansu masu iko duka ne, kuma ba su da farko. Sabodahaka, in ji koyarwar Allah-Uku-Cikin-�aya, Uban Allah ne,�an ma Allah ne, kuma Ruhu Mai Tsarki ma Allah ne, kumawa�annan Allah �aya ne.

Gaskiya Game da Uba, �a, da KumaRuhu Mai Tsarki

Rataye 201

202 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

Da yawa da suka gaskata da Allah-Uku-Cikin-�aya sun yar-da cewa ba za su iya yin bayani ba a kan wannan koyarwa.Duk da haka, wata�ila suna jin cewa Littafi Mai Tsarki ne yakoyar da shi. Amma ya kamata a lura cewa kalmomin nan“Allah-Uku-Cikin-�aya” ba su bayyana ba a cikin Littafi MaiTsarki. Amma da ra’ayin ne cikin Littafi Mai Tsarki? Dominmu sami wannan tabbaci bari mu bincika nassi da wa�andasuka gaskata da shi suke amfani da shi su tabbatar da Allah-Uku-Cikin-�aya.

“KALMAN KUWA ALLAH NE”

Yohanna 1:1 ta ce: “A cikin farko akwai Kalma, Kalmankuwa tare da Allah ne, Kalman kuwa Allah ne.” (Yohanna1:1) Daga baya a wannan sura, manzo Yohanna ya nuna babushakka cewa “Kalman” Yesu ne. (Yohanna 1:14) Tun da ankira Kalmar Allah, wasu sun kammala da cewa, ‘�an da Ubandole ne su kasance cikin Allah �aya.’

Ka tuna cewa wannan �angaren Littafi Mai Tsarki asali anrubuta shi ne da Hellenanci. Daga baya, masu fassara sukafassara shi zuwa wasu harsuna. Wasu Masu fassara na Litta-fi Mai Tsarki ba su yi amfani da furcin nan “Kalman kuwaAllah ne” ba. Me ya sa? Bisa ga yadda suka fahimci Helle-nanci na Littafi Mai Tsarki, wa�annan masu fassara sun cewannan furcin “Kalman kuwa Allah ne” ya kamata a fas-sara shi a wata hanya dabam. Wace hanya? Ga wasumisali: “Kalmar nan Allah ne.” (A New Translation of the Bi-ble) “Kalmar wata allah ce.” (The New Testament in anImproved Version) “Kalmar tana tare da Allah, kuma tana ka-maninsa.” (The Translator’s New Testament) In ji wa�annanfassaran, Kalmar ba Allah ba ce kanta.�Maimakon haka, do-min matsayinsa a tsakanin halittun Jehobah, aka kiraKalmar wata “allah.” A nan kalmar nan “allah” tana nufin“mai iko.”

� Don �arin bayani a kan Yohanna 1:1, ka duba shafuffuka na 24-25 naHasumiyar Tsaro ta 1 ga Nuwamba, 2008, Shaidun Jehobah ne suka wal-lafa.

Rataye 203

KA NEMI �ARIN BAYANI

Mutane da yawa ba su iya Hellenanci na Littafi MaiTsarki ba. To, ta yaya za ka tabbata ainihin abin da manzoYohanna yake nufi? Ka yi tunani a kan wannan misalin: Mala-min makaranta ya yi wa �alibansa bayani a kan wani darasi.Daga baya, �aliban ra’ayinsu ya bambanta game da bayanin.Ta yaya �aliban za su warware matsalar? Za su tambayi mala-min ya sake ba su bayani. Babu shakka, samun �arin bayanizai taimake su su fahimci batun. Hakazalika, domin ka fahim-ci ma’anar Yohanna 1:1, za ka sake bincika Lingilar Yohannadomin �arin bayani game da matsayin Yesu. Samun �arin ba-yani game da wannan batun babu shakka zai taimake ka kafahimci batun yadda ya kamata.

Alal misali, ka yi la’akari da abin da Yohanna ya rubutaa sura 1, aya 18: “Ba wanda ya ta�a ganin Allah [Maka�aici]ba da�ai.” Amma, mutane sun ga Yesu, �an, domin Yohan-na ya ce: “Kalman [Yesu] ya zama jiki, ya zauna a wurinmumuka duba �aukakarsa.” (Yohanna 1:14) To, ta yaya ne �anzai kasance �angare na Allah Maka�aici? Yohanna kuma ya ceKalmar yana ‘tare da Allah.’ Ta yaya mutum zai kasance yanatare da wani kuma ya kasance cewa shi ne wannan mutumin?(Yohanna 1:34) Duk da haka, kamar yadda aka rubuta a Yo-hanna 17:3, Yesu ya bambanta kansa da kuma Ubansa da kesama. Ya kira Ubansa, “Allah maka�aici mai-gaskiya.” A kusan�arshen Lingilarsa, Yohanna ya kammala yana cewa: “An ru-buta wa�annan, domin ku bada gaskiya Yesu Kristi ne, �anAllah. (Yohanna 20:31) Ka lura cewa ba a kira Yesu Allah ba,amma �an Allah. Wannan �arin bayani daga Lingilar Yohan-na ta nuna yadda ya kamata a fahimci Yohanna 1:1. Yesu,Kalmar, wani “Allah” ne domin yana da matsayi mai girmaamma ba domin �aya yake da Allah Maka�aici ba.

KA TABBATAR DA BAYANIN

Ka sake tunani game da misalin na malamin makaranta da�alibai. A ce har yanzu wasu suna shakka, har bayan sun sau-rari �arin bayani daga wurin malamin. Me ya kamata su yi?Suna iya zuwa wurin wani malami domin �arin bayani a kan

204 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

wannan batun. Idan malamin na biyu ya tabbatar da bayanina malami na farkon, za a warware shakka ta yawancin �ali-ban. Hakazalika, idan ba ka tabbatar da abin da marubucinLittafi Mai Tsarki Yohanna yake fa�a ba game da dangantakarda ke tsakanin Yesu da Allah Maka�aici, kana iya juyawa gawani marubucin Littafi Mai Tsarki domin �arin bayani. Alalmisali ka yi la’akari da abin da Matta ya rubuta. Game da �ar-shen wannan zamani, ya yi �aulin Yesu yana cewa: “Ammazancen ranan nan da sa’an nan ba wanda ya sani ba, ko ma-la’iku na sama, ko �a, sai Uba ka�ai.” (Matta 24:36) Ta yayawa�annan kalmomi suka nuna cewa Yesu ba Allah Maka�aiciba ne?

Yesu ya ce Uba yana da sani fiye da �an. Idan Yesu �angarene na Allah Maka�aici, da ya san abin da Uban ya sani. Sabo-da haka, �a da Uban ba za su ta�a zama �aya ba. Duk da hakawasu za su ce: ‘Yesu yana da yanayi biyu. A nan yana maga-na ne a mutum.’ Amma idan haka ne ma, ruhu mai tsarki fa?Idan ruhu mai tsarki Allah ne daidai da Uba, me ya sa Yesu baice ya san abin da Uba ya sani ba?

Sa’ad da ka ci gaba da nazarinka na Littafi Mai Tsarki, zaka fahimci wurare da yawa na Littafi Mai Tsarki da suka shafiwannan batu. Sun tabbatar da gaskiya game da Uba, da �a, dakuma ruhu mai Tsarki.—Zabura 90:2; Ayukan Manzanni 7:55;Kolossiyawa 1:15.

MILIYOYIN mutane suna �auna kuma suna �aukaka gicciye.The Encyclopædia Britannica ya kira gicciye “ainihin alama taaddinin Kirista.” Duk da haka, Kiristoci na gaskiya ba sa amfa-ni da gicciye wajen bauta. Me ya sa?

Dalili �aya mai muhimmanci shi ne cewa Yesu Kristi baimutu a kan gicciye ba. Kalmar Hellenanci da galibi ake fassara

Abin da Ya Sa Kiristoci na Gaskiya baSa Amfani da Gicciye Wajen Bauta

Rataye 205

ta “gicciye” stau·ros� ce. Tana nufin “mi�a��en gungume kosanda.” Littafi Mai Tsarkin nan Companion Bible ya ce: “[Stau-ros�] bai ta�a nufin gumagumai biyu ba, da aka �ora a kanjuna ko ta wane hali . . . Babu ma wani abu a Hellenanci na[Sabon Alkawari] da ya yi kusa da gumagumai biyu.”

A wasu wurare da yawa, marubutan Littafi Mai Tsarki sun yiamfani da wata kalma wajen kwatanta abin da aka kashe Yesua kai. Kalmar Hellenanci ce xy�lon. (Ayukan Manzanni 5:30;10:39; 13:29; Galatiyawa 3:13; 1 Bitrus 2:24) Ma’anar wannankalmar ita ce “katako” ko kuma “sanda ko kulki, ko kuma ita-ce.”

Da yake ba da bayani a kan abin da ya sa sau da yawa akeamfani da sanda domin kisa, littafin nan Das Kreuz und dieKreuzigung (Gicciye da kuma Gicciya), na Hermann Fulda,ya ce: “Babu itatuwa a wurare da aka za�a domin kisa. Sabo-da haka ake kafa gungume a �asa. A kan wannan ake kafa kokuma �aure hannu da �afafuwansu masu laifi a sama.”

Tabbaci mafi �arfi ta fito ne daga Kalmar Allah. Manzo Bu-lus ya ce: “Kristi ya fanshe mu daga la’anar shari’a, da ya zamala’ana maimakonmu: gama an rubuta, kowane wanda an rata-ye shi ga itace la’ananne ne.” (Galatiyawa 3:13) A nan Bulusya yi �aulin Kubawar Shari’a 21:22, 23, wadda ta yi maganaritace, ba giciye ba. Tun da irin wannan kisa yana mai da mu-tum “la’ananne,” ba daidai ba ne Kristoci su yi wa gidajensuado da siffan Kristi a rataye.

Babu tabbaci cewa Shekaru 300 bayan mutuwar Kristi, wa-�anda suka yi da’awar cewa su Kristoci ne sun yi amfanida giciye wajen bauta. Amma a �arni na hu�u, arnen DaulaConstantine ya kar�i Kiristanci na ’yan ridda kuma ya ya�agicciye a matsayin alamarta. Ko da menene dalilinsa, babuabin da ya ha�a gicciye da Yesu Kristi. Gicciye, ainihi dagaarna aka samo shi. New Catholic Encyclopedia ya ce: “Gic-ciye ta wanzu a al’adu na zamanin kafin Kirisanci da kumazamanin da babu Kiristanci.” Wasu masana suna nuna ala�atsakanin giciye da bautar yanayi da kuma al’adun jima’i naarna.

Me ya sa aka �aukaka wannan alama na arna? Domin yakasance da sau�i arna su kar�i “Kiristanci.” Duk da haka, Lit-tafi Mai Tsarki ya la’anta bauta ga dukan wani alama ta arna.(2 Korinthiyawa 6:14-18) Nassosi kuma sun hana dukan waniire-iren bautar gumaka. (Fitowa 20:4, 5; 1 Korinthiyawa 10:14)Saboda haka, domin kyawayan dalilai Kiristoci na gaskiya basa amfani da gicciye wajen bauta.�

� Domin �arin bayani game da gicciye, ka dubi shafuffuna na 89-93 nalittafin nan Reasoning From the Scriptures, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

206 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

AN UMURCI Kiristoci su kiyaye Farilla ta Tuna Mutuwar Kristi.Wannan farillar kuma ana kiranta “jibin Ubangiji.” (1 Korin-thiyawa 11:20) Wane muhimmanci yake da shi? Yaushe kumata yaya za a kiyaye farillar?

Yesu Kristi ya kafa wannan farillar a daren bikin �e-tarewa na Yahuduwa a shekara ta 33 A.Z. Ana bikin�etarewa ne sau �aya a shekara a ranar 14 ga watanNisan a kalandar Yahudawa. Domin su �irga kwa-nan watan wata�ila Yahudawa suna jira ne har saifarkon damina lokacin da rana da dare tsawonsu�aya. Wannan ita ce ranar da take da kusan awoyi12 na dare da kuma awoyi 12 na rana. Fitowan sa-bonwata na kusa dawannan ranar shi ne farkonwatanNisan. Ana bikin �etarewa a rana ta 14 bayan fa�uwar rana.

Yesu ya yi bikin �etarewa tare da manzanninsa, yasallami Yahuda Iskariyoti, saikuma ya kafa farilla ta Ji-bin Maraice na Ubangiji.Wannan farillar ta canji bikin�etarewa na Yahudawa saboda hakaya kamata a yi ta sau �aya a shekara.

Jibin Maraice na Ubangiji—Farilla da Ke Daraja Allah

Rataye 207

Linjilar Matta ya ce: “Yesu ya �auki gurasa, ya yi godiya, yakarya; ya ba almajiran, ya ce, Ku kar�a, ku ci; wannan jikinane. Kuma ya �auki �o�o, ya yi godiya, ya ba su kuma, ya ce,Dukanku ku sha daga cikinsa; gama wannan jinina ne na al-kawari, wanda an zubar domin mutane dayawa zuwa gafararzunubai.”—Matta 26:26-28.

Wasu sun gaskata cewa Yesu ya juya burodin ya zama na-mansa, giyar kuma ta zama jininsa. Amma, jikin Yesu acike yake sa’ad da ya ba da burodin. Da gaske ne cewa man-zannin sun ci namansa a zahiri kuma sun sha jininsa? Dawannan zai taka dokar Allah. (Farawa 9:3, 4; Leviticus 17:10)In ji Luka 22:20, Yesu ya ce: “Wannan �o�on sabon alkawa-ri ne cikin jinina, wanda an zubar dominku.” �o�on ya juyane ya zama “ sabon alkawari” a zahiri? Hakan ba zai yiwuba, tun da alkawari yarjejeniya ne ba abin da za a iya ri�ewada hannu ba ne.

Saboda haka, burodin da giyar alamu ne kawai. Burodinalamar jikin Kristi ne marar zunubi. Yesu ya yi amfani da ra-guwar burodi na bikin �etarewa. An yi burodin ba tare da yistiba. (Fitowa 12:8) Sau da yawa, a Littafi Mai Tsarki yisti yananufin zunubi. Saboda haka, burodin alamar kamiltaccen jikida Yesu ya ba da hadaya ne. Ba shi da zunubi.—Matta 16:11, 12; 1 Korinthiyawa 5:6, 7; 1 Bitrus 2:22; 1 Yohanna 2:1, 2.

Jar giya alama ce ta jinin Yesu. Wannan jinin ta kafa sa-bon alkawari. Yesu ya ce an zubar da jininsa domin “gafararzunubai.” Saboda haka mutane suna iya zama masu tsabta agaban Allah kuma za su iya shiga sabon alkawari da Jehobah.(Ibraniyawa 9:14; 10:16, 17) Wannan alkawari ya sa ya yiwuKiristoci masu aminci 144,000 su tafi sama. A nan za su zamasarakuna da firistoci domin albarkar dukan ’yan adam.—Fara-wa 22:18; Irmiya 31:31-33; 1 Bitrus 2:9; Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10; 14:1-3.

Waye zai ci wannan alamu na tuna Mutuwar Yesu? Wa�an-da kawai suke cikin sabon alkawarin ne—wato, wa�anda sukeda begen zuwa sama—su ne kawai ya kamata su ci burodinkuma su sha giyar. Ruhun Allah yake tabbatar wa wa�annan

208 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

cewa an za�e su su zama sarakuna a samaniya. (Romawa 8:16)Kuma suna cikin alkawarin Mulki da Yesu.—Luka 22:29.

Wa�anda suke da begen rayuwa har abada a Aljanna a duni-ya fa? Suna yin biyayya ga umurnin Yesu kuma suna halartarbikin Jibin Maraice na Ubangiji, suna zuwa ne domin su lura,ba don su ci ko su sha ba. Sau �aya a shekara bayan fa�u-war rana, a ranar 14 ga watan Nisan, Shaidun Jehobah sunakiyaye farilla ta Jibin Maraice na Ubangiji. Ko da yake dubbaikalilan ne kawai suke da’awar zuwa sama, wannan farilla tanada muhimmanci ga dukan Kiristoci. Lokaci ne na yin bimbi-ni bisa �auna ta Jehobah Allah da kuma Yesu Kristi.—Yohanna3:16.

SA’AD da ka ji kalmomin nan “kurwa” ko kuma “ruhu,” me-nene yake fa�o maka a zuciya? Mutane da yawa sun gaskatacewa wa�annan kalmomi suna nufin wani abu marar ganuwada ke zaune cikin mu. Suna tsammanin cewa sa’ad da mutumya mutu wannan abin sai ya fice daga jikin mutum ya ci gabada rayuwa. Tun da yake wannan koyarwar ta ya�u sosai, mu-tane da yawa sun yi mamaki da suka fahimci cewa wannan bakoyarwar Littafi Mai Tsarki ba ce. To, menene kurwa, kumamenene ruhu bisa koyarwar Kalmar Allah?

“KURWA” YADDA AKA YI AMFANI DA ITACIKIN LITTAFI MAI TSARKI NA ASALI

Da farko, bari mu bincika kurwa. Za ka tuna cewa ainihi anrubuta Littafi Mai Tsarki ne da Ibrananci da kuma Helenanci.Sa’ad da suke rubutu game da kurwa, marubutan Littafi MaiTsarki sun yi amfani da kalmar nan ne�phesh a Ibrananci kokuma kalmar Helenanci psy·khe�. Wa�annan kalmomi biyusun bayyana fiye da sau 800 a cikin Nassosi, kuma New World

“Kurwa” da Kuma “Ruhu”—MeneneAinihi Ma’anar Wa�annan Kalmomi?

Rataye 209

Translation ya fassara su “kurwa.” Idan ka bincika yadda aka yiamfani da wannan kalmar “kurwa” a cikin Littafi Mai Tsarki,za ka ga cewa wannan kalmar ainihi tana nufin (1) mutane,(2) dabbobi, ko kuma (3) ran mutum ko na dabba. Bari mudubi wasu nassosi da suka gabatar wannan.

Mutane.“A zamanin Nuhu, . . . mutane kima, watau masu-rai takwas, suka tsira ta wurin ruwa.” (1 Bitrus 3:20) A nankalmar nan “masu-rai” a bayyane yake cewa tana nufin muta-ne—Nuhu, matarsa, ’ya’yansa uku, da matansu. Fitowa 16:16ta yi maganar umurni da aka ba wa Isra’ilawa game da taramanna. An gaya musu: “tara . . . gwalgwadon yawan masu-rainaku, haka za ku �iba, kowane mutum domin wa�anda ke ci-kin [tanti] nasa.” Saboda haka yawan manna da aka tara bisaga yawan mutane da ke cikin kowace iyali ne. Wasu wurareda Littafi Mai Tsarki ya yi maganar “masu-rai” ga mutum komutane ana samun su a Farawa 46:18; Joshuwa 11:11; AyukanManzanni 27:37 da kuma Romawa 13:1.

Dabbobi. A cikin tarihin halitta na Littafi Mai Tsarki munkaranta: “Allah ya ce, Bari ruwaye su yawaita haifan masu-motsi wa�anda ke da rai, tsuntsaye kuma su tashi birbishinduniya cikin sararin sama. Allah kuwa ya ce, Bari �asa ta fid-da mai-rai kowane bisa ga irinsa, bisashe, da masu-rarrafe, dadabbobin duniya bisa ga irinsu: haka kuwa ya zama.” (Farawa1:20, 24) A nan, kifaye, tsuntsaye, dabbobi, da kuma namundaji duka an kira su da kalma guda—“masu-rai.” An kira dab-bobi masu-rai a Farawa 9:10, Leviticus 11:46; da kuma Lissafi31:28.

Ran mutum. A wasu lokatai kalmar nan “kurwa” tana nu-fin ran mutum. Jehobah ya gaya wa Musa: “Dukan mutanenda suka nemi ranka sun mutu.” (Fitowa 4:19) Menene abokangaban Musu suke nema? Suna �o�ari ne su kashe Musa. Dafarko, sa’ad da Rahila take haifan Banyamin, “sa’anda rantayana fita, (gama ta mutu).” (Farawa 35:16-19) A wannan loka-ci Rahila ta mutu. Ka yi la’akari kuma da kalmomin Yesu: “Nine makiyayi mai-kyau: makiyayi mai-kyau ya kan bada ransadomin tumaki.” (Yohanna 10:11) Yesu ya ba da kurwarsa, kokuma ransa, domin mutane. A wannan wurare na Littafi Mai

210 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

Tsarki, kalmar nan “kurwa” a yare na asali bayyane yake cewatana nufin ran mutum. Za ka sami �arin misalai na wannana 1 Sarakuna 17:17-23; Matta 10:39; Yohanna 15:13; da kumaAyukan Manzanni 20:10.

�ara nazarin Kalmar Allah za ta nuna maka cewa babu indaaka ha�a kalmar nan “kurwa” da “rashin mutuwa” ko “daw-wama.” Maimakon haka, Nassosi a yare na asali sun ce kurwatana mutuwa. (Ezekiel 18:4, 20) Saboda haka, Littafi Mai Tsar-ki yake kiran wanda ya mutu “gawa.”—Leviticus 21:11.

AN GANO “RUHU”

Bari yanzu mu bincika yadda Littafi Mai Tsarki ya yi amfanida kalmar nan “ruhu.” Wasu mutane suna tsammani “ruhu”wata kalma ce mai nufin “kurwa.”Amma ba haka yake ba. Lit-tafi Mai Tsarki ya bayyana sarai cewa “ruhu” da “kurwa” sunanufin abubuwa biyu ne da suka bambanta. Ta yaya suka bam-banta?

Marubutan Littafi Mai Tsarki sun yi amfani da kalmar Ib-rananci ru�ach ko kuma ta Helenanci pneu�ma sa’ad da sukerubutu game da “ruhu.” Nassosi kansu sun bayyana ma’anarwa�annan kalmomi. Alal misali, Zabura 104:29 ta ce:‘Idan ka [Jehobah] swance numfashinsu [ru�ach], sun mutu,sun koma tur�ayarsu.’ Ya�ub 2:26 ta ce “jiki ba tare da ruhu[pneu�ma] matacce ce.”Awa�annan ayoyi, “ruhu” yana nufinabin da yake ba da rai ga jiki. In ba tare da ruhu ba jiki matac-ce ne. Saboda haka, a cikin Littafi Mai Tsarki an fassara kalmarnan ru�ach ba kawai ruhu ba amma kuma “rai.” Alal misa-li, game da Ambaliyar zamanin Nuhu, Allah ya ce: “Ina kaworuwan tufana a bisa duniya, domin a hallaka dukan mai-rai,wanda ke da numfashin [ru�ach] rai a cikinsa, daga �ar�ashinsama.” (Farawa 6:17; 7:15, 22) Saboda haka, “ruhu” yana nu-fin iko marar ganuwa da ke motsa dukan abubuwa masu rai.

Kurwa da kuma ruhu ba �aya ba ne. Menene bambancin-su? Jiki yana bukatar ruhu kamar yadda rediyo yake bukatarwutar lantarki—domin ya yi magana. Domin �arin misali, kayi tunanin �an rediyo. Sa’ad da ka saka batir a cikin rediyo,wutar da take cikin batir �in za ta sa rediyon ta yi magana.

Rataye 211

Amma idan babu batir sai rediyon ya mutu. Haka kuma re-diyon da aka cire daga wutan lantarki. Hakazalika, ruhu shine iko da ke ba da rai ga jiki. Kuma kamar wutar lantarki ru-hun ba shi da motsin zuciya ko tunani. Iko ne ba mutum ba.Amma idan ba tare da ruhun ba ko kuma rai, ‘jikinmu sai yamutu ya koma tur�aya,’ kamar yadda mai zabura ya fa�a.

Da yake magana game da mutuwar mutum, Mai-Wa’azi12:7 ta ce: “�ura [na jikinsa] kuma ta sake koma cikin �asakamar da, ruhu kuma ya komo wurin Allah wanda ya bayar.”Sa’ad da ruhu, ko kuma rai, ya fita daga jiki, jiki sai ya mutuya koma inda ya fito—�asa. Haka nan, rai yake komawa wu-rin wanda ya ba da shi—Allah. (Ayuba 34:14, 15; Zabura 36:9)Wannan ba ya nufin cewa rai ainihi yana tafiya zuwa sama.Maimakon haka, yana nufi ne cewa ga wanda ya mutu, dukanwani begen rayuwa a nan gaba ya dangana ne ga Jehobah Al-lah. Ransa yana hannun Allah. Sai ta wajen ikon Allah ne kokuma ruhu, za a iya sake ba da rai saboda mutumin ya sake ra-yuwa.

Yana kwantar da hankali mu sani cewa haka Allah ya nufaya yi ga dukan wa�anda suke hutu cikin “kabarbaru” da Allahya yi niyyar tunawa da su! (Yohanna 5:28, 29) A lokacin ta-shin matattu, Jehobah zai sake ba da sabon jiki ga wanda yakebarcin mutuwa kuma ya sake raya shi ta wajen ba shi ruhu, kokuma rai. Wannan hakika zai kasance rana ta farin ciki!

Idan kana so ka �ara fahimtar kalmomin nan “kurwa”da “ruhu” kamar yadda aka yi amfani da su cikin Littafi MaiTsarki, za ka sami bayani mai muhimmanci cikin mujallar

nan Menene Yake Faruwa damu Sa’ad da Muka Mutu?da kuma a shafuffuka na375-384 na littafin nan Rea-soning From the Scriptures,duka Shaidun Jehobah nesuka wallafa.

A HARSUNANSA na asali, Littafi Mai Tsarki ya yi amfani dakalmar Ibrananci she�ohl� da kuma ta Helenanci hai�des fiyeda sau 70. Dukansu suna da ala�a da mutuwa. Wasu masufassara sun fassara su “kabari,” “jahannama,” ko kuma“rami.” Amma, a yawancin harsuna babu kalmomi da sukayi daidai da wa�annan kalmomin Ibrananci da Helenanci.Saboda haka, Litafi Mai-Tsarki ya yi amfani da kalmar nan“Hades.” Menene wa�annan kalmomi ainihi suke nufi? Barimu lura da yadda aka yi amfani da su a wurare dabam da-bam a cikin Littafi Mai Tsarki.

Mai-Wa’azi 9:19 ta ce: “Babu wani aiki, ko dabara, ko ili-mi, ko hikima, cikin kabari inda za ka.” Wannan yana nufine cewa Sheol yana nufin kabari takamaimai na wani ma-maci, ko kuma makabarta da muka binne wani da muke�auna? A’a. Sa’ad da Littafi Mai Tsarki yake magana game dawurin da aka binne mutum, ko kuma kabarin mutum,yana amfani da wasu kalmomi na Ibrananci ko Helenanci,ba she�ohl� and hai�des ba. (Farawa 23:7-9; Matta 28:1) KumaLittafi Mai Tsarki bai yi amfani da “Sheol” ga kabari da akabinne mutane da yawa ba, irin su kabarin iyali ko kuma ka-bari �aya da aka binne mutane da yawa a ciki.—Farawa 49:30, 31.

Wane irin wuri ne “Sheol” yake nufi? Kalmar Allah tanuna cewa “Sheol,” ko “Hades,” yana nufin abu ne da yafi babban kabari girma. Alal misali, Ishaya 5:14 ta ce Sheolya ‘fa�a�a gurinsa, ya wage bakinsa gaba da misali.’ Ko dayake Sheol ya riga ya ha�iye matattun mutane marasa iya-ka, kamar dai a kullum yana bukatar �ari. (Misalai 30:15, 16)Ba kamar wuri na zahiri da ake binne mutane ba, da zai iya�aukan iyakar adadinsa, ‘[Sheol] ba ya �oshi.’ (Misalai27:20) Wato, Sheol ba ya cika. Ba shi da iyaka. Saboda haka,Sheol, ko Hades ba wuri ba ne na zahiri. Maimakon haka,kabari ne na dukan ’yan adam, wuri na alama da yawancin’yan adam suke barci cikin mutuwa.

Menene Sheol da kuma Hades?212

Rataye 213

Koyarwar Littafi Mai Tsarki ta tashin matattu ta taima-ka mana mu sami �arin haske game da ma’anar “Sheol” da“Hades.” Kalmar Allah ta nuna nasaba da ke tsakanin Sheolda Hades da kuma irin mutuwar da za a sami tashin matat-tu.� (Ayuba 14:13; Ayukan Manzanni 2:31; Ru’ya ta Yohanna20:13) Kalmar Allah ta nuna cewa wa�anda suke Sheol, koHades, sun ha�a da wa�anda suka bauta wa Jehobah dakuma wa�anda ba su bauta masa ba. (Farawa 37:35; Zabura55:15) Saboda haka, Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa za a“yi tashin matattu, masu-adalci da na marasa-adalci.”—Ayu-kan Manzanni 24:15.

� Akasarin haka, matattu da ba za a tashe su ba an kwatanta cewa sunacikin “Jahannama” ba cikin Sheol, ko kuma Hades ba. (Matta 5:30; 10:28;23:33) Kamar Sheol da Hades, Jahannama ba wuri ba ne na zahiri.

YAYA kake tsammanin ranar shari’a take? Wasu suna tsam-manin cewa da �ai�ai da �ai�ai mutane biliyoyi za su zogaban kursiyin Allah. Saboda haka, sai a zartar da hukuncibisa kowa. Wasu za a ba su ladar salama a sama, wasu kumaa jefa su cikin wuta a azabtar da su har abada. Amma, LittafiMai Tsarki ya kwatanta wannan lokaci a wata hanya dabam.Kalmar Allah ta kwatanta lokacin, ba lokaci ba ne na tsoro darazana, amma lokaci ne na bege da yin gyara.

A Ru’ya ta Yohanna 20:11, 12, mun karanta yadda man-zo Yohanna ya kwatanta wannan Ranar Shari’a: “Na ga kumababban farin kursiyi, da wanda ke zaune a bisansa, wanda du-niya da sama suka guje ma fuskatasa; ba a kuwa samu musuwuri ba. Na ga matattu kuma, �anana da manya, suna tsa-ye a gaban kursiyin; aka bu�e littattafai: aka bu�e wani littafikuma, littafin rai ke nan: aka yi ma matattu shari’a kuma bisaga abin da aka rubuta cikin littattafai, gwargwadon ayyukan-su.” Wanene Al�ali da aka kwatanta a nan?

Mecece Ranar Shari’a?

214 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

Jehobah Allah shi ne babban Al�ali na ’yan adam. Amma,ya ba da aikin zartar da shari’a. In ji Ayukan Manzanni 17:31, manzo Bulus ya ce Allah, “ya sanya rana, inda za ya yima duniya duka shari’a mai-adalci ta wurin mutum wanda ya�adara.” Wannan Al�alin Yesu Kristi ne da aka ta da daga ma-tattu. (Yohanna 5:22) Amma, a yaushe ne Ranar Shari’a za tafara? Yaya tsawonta?

Littafin Ru’ya ta Yohanna ya nuna cewa Ranar Shari’a za tafara bayan ya�in Armagedon, sa’ad da aka riga aka halaka du-kan tsarin Shai�an daga duniya.� (Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16;19:19–20:3) Bayan Armagedon, za a �aure Shai�an da aljan-nunsa a cikin rami marar-matu�a na shekara dubu. A wannanlokaci ne, mutane 144,000 abokan gado na sama za su yi“mulki kuma tare da Kristi shekara dubu.” (Ru’ya ta Yohanna14:1-3; 20:1-4; Romawa 8:17) Ranar Shari’a ba abu ba ne cikinhanzari da za a yi cikin awoyi 24. Zai �auki shekara dubu.

A cikin wa�annan shekaru dubu, Yesu zai yi shari’a ga“masu-rai da matattu.” (2 Timothawus 4:1) “Masu-rai” sune “taro mai-girma” da suka tsira daga Armagedon. (Ru’yata Yohanna 7:9-17) Manzo Yohanna ya ga “matattu. . . sunatsaitsaye a gaban kursiyin” shari’a. Kamar yadda Yesu ya yialkawari, “wa�anda suna cikin kabarbaru za su ji murya [Kris-ti], su fito kuma” ta wajen tashin matattu. (Yohanna 5:28, 29;Ayukan Manzanni 24:15) A kan me za a yi musu shari’a?

In ji wahayin manzo Yohanna, “aka kuma bu�e littattafai,”kuma “aka kuwa yi wa matattu shari’a bisa ga abin da ke rubu-ce cikin littattafan, gwargwadon aikin da suka yi.” Wa�annanlittattafan sun �unshi abubuwa da mutane suka yi ne a da?A’a, shari’ar ba bisa abin da mutane suka yi ba ne kafin sumutu. Ta yaya muka san haka? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wan-da ya mutu ya ku�uta daga zunubi.” (Romawa 6:7) Wa�andaaka tashe su daga matattu wato za su fito ne babu zunubi.Saboda haka, wa�annan littattafai suna wakiltan �arin umur-

� Game da Armagedon, don Allah, ka dubi Insight on the Scriptures, Lit-tafi na 1, shafuffuka 594-595, 1037-1038, sai kuma babi na 20 na littafinnan Bauta wa Allah Maka�aici na Gaskiya, duka biyu Shaidun Jehobah nesuka wallafa.

Rataye 215

ni ne na Allah. Domin su rayu har abada wa�anda suka tsiradaga Armageddon da wa�anda aka tashe su daga matattu dolene su bi umurnin Allah, ha�e da dukan wani umurni da za abayyana a cikin shekara dubun. Saboda haka, mutane za a yimusu hukunci ne bisa abin da suka yi cikin Ranar Shari’a.

Ranar Shari’a za ta ba miliyoyin mutane zarafinsu na farkosu koyi game da nufin Allah kuma su bi shi. Wannan yana nu-fin cewa za a yi aikin koyarwa mai yawa. Hakika, ‘mazaunanduniya za su koyi adalci.’ (Ishaya 26:9) Amma, ba duka ba neza su so su yi nufin Allah. Ishaya 26:10 ta ce: “Ko an nuna mamugu alheri, ba za ya koyi adilci ba: a cikin �asa mai-gaskiyaza ya aika mugunta, ba kuwa za shi ga �aukakar Ubangiji ba.”Za a halaka miyagu har abada a Ranar Shari’a.—Ishaya 65:20.

A �arshen Ranar Shari’a, mutane da suka tsira za su “rayu”su zama mutane kamilai. (Ru’ya ta Yohanna 20:5) Sabodahaka, a Ranar Shari’a za a mai da mutane kamar yadda suketun farko. (1 Korinthiyawa 15:24-28) Daga nan, sai gwaji na�arshe ya biyo baya. Za a saki Shai�an daga kurkuku kuma a�yale shi ya yi ru�i na �arshe ga mutane. (Ru’ya ta Yohanna20:3, 7-10) Wa�anda suka guje shi za su more cikar alkawarinLittafi Mai Tsarki: “Masu-adalci za su gaji �asan, su zauna a ci-kinta har abada.” (Zabura 37:29) Hakika, Ranar Shari’a za takasance albarka ga dukan ’yan adam masu aminci!

�ALIBAN Littafi Mai Tsarki sun yi shelar cewa abubuwa masumuhimmanci za su faru a shekara ta 1914 na kusan shekara40. Menene wa�annan abubuwa masu muhimmanci, kumawane tabbaci ne ya nuna cewa shekara ta 1914 shekara ce maimuhimmanci?

Kamar yadda yake rubuce a Luka 21:24, Yesu ya ce: “Al’um-mai za su tattake Urushalima kuma har zamanan Al’ummaisun cika.” Urushalima ita ce babbar birnin al’ummar

1914—Shekara Mai Muhimmanci aAnnabcin Littafi Mai Tsarki

216 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

Yahudawa—mazaunin gadon sarautar sarakuna daga zuriyarDawuda. (Zabura 48:1, 2) Amma, wa�annan sarakuna sunbambanta da sarakunan wasu al’ummai. Suna zama ne bisa“kursiyin Ubangiji” suna wakiltan Allah kansa. (1 Labarbaru29:23) Saboda haka Urushalima alama ce ta sarautar Jehobah.

Yaushe kuma ta yaya al’ummai suka fara “tattake” sarautarAllah? Wannan ya faru ne a shekara ta 607 K.Z., sa’ad da Ba-biloniyawa suka ci Urushalima a ya�i. “Kursiyin Ubangiji” yakasance babu kowa a kai, kuma aka ta�a zuriyar sarakuna da tasamo asali daga Dawuda. (2 Sarakuna 25:1-26) Wannan ‘tat-takewa’ za ta ci gaba ne har abada? A’a, domin annabcin Ezekielya ce sarkin �arshe na Urushalima, Zedekiah: Ya “kawarda rawa-ni, [kuma] tu�e �ambi: . . . har lokacin da wannan ya zo wandawajibinsa ne, ni ma im ba shi.” (Ezekiel 21:26, 27) Wanda “waji-binsa” ne �ambin zuriyarDawuda Yesu Kristi ne. (Luka 1:32, 33)Saboda haka ‘tattakewa’ za ta �are sa’ad da Yesu ya zama Sarki.

“BAKWAI BAKWAI”

Shekaru 2,520

Shekaru ta 606 1/4Daga Oktoba 607 K.Z. zuwa

31 ga Disamba, 1 K.Z.

Shekaru 1,913 3/41 ga Janairu, 1 A.Z. zuwa

Oktoba 1914

607 & K.Z. A.Z. ) 1914

“Al’ummai zasu tattakeUrushalima”

“Wandawajibinsa ne”

Rataye 217

Yaushe ne wannan babban abu zai faru? Yesu ya nuna cewa’yan al’ummai za su yi sarauta na wani tabbataccen lokaci.Batun da ke cikin sura 4 na Daniel ya �unshi mabu�in sanintsawon wannan lokaci. Ya ba da labarin mafarki da Sarki Ne-buchadnezzar na Babila ya yi. Ya ga wani babban itace da akasare. Gindin sawayensa ba zai iya girma ba domin an �aure shida �arfe da jangaci. Mala’ika ya sanar: ‘A bar wokatai guda ba-kwai kuma su bi ta bisa kansa.’—Daniel 4:10-16.

A Littafi Mai Tsarki, a wani lokaci ana amfani da itace wa-jen wakiltan sarauta. (Ezekiel 17:22-24; 31:2-5) Saboda hakasare wannan itace na alama yana nuna yadda za a ta�a sa-rakuna a Urushalima wa�anda suke wakiltan sarautar Allah.Wahayin kuma ya ba da garga�i za a “tattake Urushalima”na �an lokaci—“wokatai bakwai.” Yaya tsawon wannan loka-ci yake?

Ru’ya ta Yohanna 12:6, 14 ta nuna cewa lokatai uku da ra�isun yi daidai da “kwana dubu da metin da sattin.” Sabodahaka, “wokatai bakwai” zai ninka tsawon wannan, ko kumakwanaki 2,520. Amma Al’ummai ba su daina tattake sarautarAllah ba bayan kwanaki 2,520 bayan fa�uwar Urushalima. Abayyane yake cewa lokaci na wannan annabci ya fi hakatsawo. Bisa ga abin da ke Littafin Lissafi 14:34 da kuma Eze-kiel 4:6, wa�anda suka yi maganar “rana guda domin shekaraguda,” “wokatai bakwai” zai kasance shekara 2,520.

Shekara 2,520 ya fara a watan Oktoba shekara ta 607 K.Z.,sa’ad da Babiloniyawa suka ci Urushalima aka tun�uke sarau-tar zuriyar Dauda daga kursiyinsa. Wannan lokaci ya �are ashekara ta 1914. A wannan lokaci, “zamanan al’ummai” ya�are, kuma aka na�a Yesu Kristi ya zama Sarkin Mulkin Allahna samaniya.�—Zabura 2:1-6; Daniel 7:13, 14.

� Daga Oktoba na shekara ta 607 K.Z., zuwa 1 ga Oktoba K.Z., shekaru606 ne. Tun da babu shekara ta sifiri, daga 1 ga Oktoba shekara ta 1 K.Z.,zuwa Oktoba shekara ta 1914 shekaru 1,914 ne. Idan aka ha�a shekara 606da shekara 1,914, sai mu sami shekaru 2,520. Domin bayani game da fa�u-war Urushalima a shekara ta 607 K.Z., ka dubi talifin nan “Chronology”(Tsarin Shekaru) a Littafin nan Insight on the Scriptures, da Shaidun Jeho-bah suka wallafa.

218 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

Kamar yadda Yesu ya annabta, ‘bayyanuwarsa’ Sarki a sa-maniya ya zo da aukuwa masu ban mamaki—ya�i, yunwa,girgizar �asa, annoba. (Matta 24:3-8; Luka 21:11) Wa�annanaukuwa sun ba da tabbaci cewa shekara ta 1914 mafari ce taMulkin Allah kuma mafari ce ta “kwanaki na �arshe” na wan-nan mugun zamani.—2 Timothawus 3:1-5

HALITTAR ruhu da ake kira Mika’ilu ba a ambace shi sauda yawa ba a cikin Littafi Mai Tsarki. Duk da haka, dukanlokacin da aka yi maganarsa yana yin wani abu. A cikin Lit-tafin Daniel, Mika’ilu yana ya�an miyagun ruhohi; a cikinwasi�ar Yahuda, yana jayayya da Shai�an; a Ru’ya ta Yohan-na kuma, yana ya�i da Iblis da kuma aljanunsa. Ta wajenkare sarautar Jehobah da kuma ya�an abokan gaban Allah,Mika’ilu ya ci sunansa wanda yake nufin—“Waye kamar Al-lah?” Amma wanene Mika’ilu?

Wasu mutane suna da suna fiye da �aya. Alal misali, ansan Ya�ub da Isra’ila, manzo Bitrus kuma, Siman. (Farawa49:1, 2; Matta 10:2) Haka nan kuma, Littafi Mai Tsarki yanuna cewa Mika’ilu wani suna ne na Yesu Kristi, kafin yarayu a duniya da kuma bayan ya rayu a duniya. Bari mu bin-cika wasu dalilai na Nassi da ya sa muka ce haka.

Babban Mala’ika. Kalmar Allah ta kira Mika’ilu “shuga-ban Mala’ika.” (Yahuda 9) Ka lura cewa an kira Mika’ilushugaban mala’iku. Wannan ya nuna cewa mala’ikanguda �aya ne. Hakika, furcin nan “shugaban mala’i-ka” ya bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki a ka�aici neba a jam’i ba. Bugu da �ari, Yesu yana da ala�a da ofi-shin shugaban mala’iku. Game da Ubangiji Yesu Kristi daaka ta da daga matattu, 1 Tassalunikawa 4:16 ta ce: “Uban-giji da kansa za ya sauko daga sama, da kira mai-�arfi, damuryar sarkin mala’iku.” Saboda haka an kwatanta mur-

Wanene Mika’ilu Shugaban Mala’iku?

yar Yesu da ta sarkin mala’iku. Domin haka, wannannassin yana nunawa ne cewa Yesu shi ne Mika’ilu shuga-ban mala’iku.

Shugaban Dakaru. Littafi Mai Tsarki ya ce “Mika’ilu danasa mala’iku suna fita su yi gaba da dragon; . . . kuma yayi gaba tare da nasa mala’iku.” (Ru’ya ta Yohanna 12:7) Sa-boda haka, Mika’ilu shugaba ne na dakarun mala’iku masuaminci. Ru’ya ta Yohanna kuma ya kwatanta Yesu da Shuga-ban dakaru na mala’iku masu aminci. (Ru’ya ta Yohanna 19:14-16) Kuma manzo Bulus ya fa�a takamaimai cewa “Uban-giji Yesu” da “mala’iku na ikonsa.” (2 Tassalunikawa 1:7)Littafi Mai Tsarki ya yi maganar Mika’ilu da “mala’ikun-sa” da kuma Yesu da “mala’ikunsa.” (Matta 13:41; 16:27;24:31; 1 Bitrus 3:22) Tun da babu inda Kalmar Allah tanuna cewa da akwai dakaru biyu na mala’iku masu amincia sama—�aya Mika’ilu yake ja-gora, �aya kuma Yesu—daidaine a kammala da cewa Mika’ilu Yesu Kristi ne a ofishinsa nasama.�

� Da �arin bayani da ya nuna cewa Mika’ilu yana nufin �an Allah a Lit-tafi na 2, shafuffuka na 393-394, na Insight on the Scriptures, Shaidun Je-hobah ne suka wallafa.

LITTAFIN Ru’ya ta Yohanna ya �unshi kalamai da bai ka-mata a fahimce su a zahiri ba. (Ru’ya ta Yohanna 1:1) Alalmisali, ya ambaci wata mace da take da suna “Babila Babba”a rubuce a goshinta. An ce kuma wannan macen tana zaunea kan ‘jama’a ce da al’ummai. (Ru’ya ta Yohanna 17:1, 5, 15)Tun da babu wata mace ta zahiri da za ta iya haka, wannanBabila Babba dole ne ta kasance ta alama. To, menene wan-nan karuwa ta alamar take wakilta?

A Ru’ya ta Yohanna 17:18, wannan macen aka sakekwatanta ta “babban birnin ne, wanda ke mulkin bisa

Gano “Babila Babba”

Rataye 219

220 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

sarakunan duniya.” Furcin nan “birni” na nuna �ungiya cemai tsari na mutane. Tun da wannan “babban birnin” yanamulki bisa “sarakunan duniya,” wannan mace mai sunanBabila Babba za ta kasance �ungiya ce mai rinjaya a dukanduniya. Ana iya kiranta daula ta duniya. Wace irin daula? TaAddini. Ka lura da yadda wasu �angarorin littafin Ru’ya taYohanna suka sa mu kammala hakan.

Daula tana iya kasancewa ta siyasa, ta ciniki, ko kumata addini. Macen mai suna Babila Babba ba daular siya-sa ba ce domin Kalmar Allah ta ce “sarakunan duniya,” kokuma ’yan siyasa na duniya sun “yi fasikanci da ita.” Fasi-kancinta yana nufin ha�a kai da ta yi da sarakunan duniya,wannan ya ba da bayanin abin da ya sa aka kira ta “babbarkaruwa.”—Ru’ya ta Yohanna 17:1, 2; Ya�ub 4:4.

Babila Babba ba za ta kasance daular ciniki ba domin “dil-lalan duniya” da suke wakiltan ’yan ciniki, za su yi matamakoki sa’ad da aka halaka ta. Hakika, an kwatanta sara-kuna da kuma attajirai suna kallonta daga “nesa.” (Ru’ya taYohanna 18:3, 9, 10, 15-17) Saboda haka, daidai ne a kam-mala cewa Babila Babba ba daular siyasa ba ce ko ta ciniki,amma ta addini.

Furcin nan ta yaudari dukan al’ummai da ‘sihirinta’ yasake jaddada cewa Babila Babba addini ce. (Ru’ya ta Yohan-na 18:23) Tun da dukan sihiri addini ne kuma daga aljannune, ba abin mamaki ba ne da Littafi Mai Tsarki ya kira ta “gi-dan aljannu.” (Ru’ya ta Yohanna 18:2; Kubawar Shari’a 18:10-12) An kwatanta wannan daula kuma da yin hamayya daaddini na gaskiya, tana tsananta wa “annabawa” da kuma“tsarkaka.” (Ru’ya ta Yohanna 18:24) Hakika, Babila Babbatana da tsananin �i ga addini na gaskiya da take tsanan-ta wa har ma da kashe “shaidu na Yesu.” (Ru’ya ta Yohanna17:6) Saboda haka, babu sauran shakka cewa wannan macenmai suna Babila Babba tana wakiltan daular addinin �aryana duniya, wanda ya ha�a da dukan wani addini da yake ha-mayya da Jehobah Allah.

LITTAFI MAI TSARKI bai gaya mana watan da aka haifi Yesuba. Amma ya ba mu kyawawan dalilai da za su sa mu tabba-ta cewa ba a haife shi a watan Disamba ba.

Ka lura da yanayi a Bai’talahmi a lokacin da aka haifi Yesu.

Watan Chislev na Yahudawa (ya yi daidai da watan-nin Nuwamba/Disamba) wata ne da ake yin sanyi da ruwansama. Watan da yake bin bayan wannan shi ne watan Tebeth(Disamba/Janairu). Wannan ne lokaci mafi sanyi a shekara,lokaci ne na dusar �an�ara a kan duwatsu.Bari mu bincika abin da Littafi Mai Tsarki ya gaya managame da yanayi a lokacin.

Marubucin Littafi Mai Tsarki Ezra ya nuna cewa wannanwatan Chislev wata ne na sanyi da ruwan sama. Bayan ya cejama’a ta taru a Urushalima “wata [Chislev] na tara ke nan,kan rana ta ashirin ga wata,” Ezra ya fa�i cewa mutane suna“rawan jiki. . .saboda ruwan sama mai-yawa.” Game da ya-nayi a wannan lokaci na shekara, mutane da suka taru da

A Watan Disamba ne Aka Haifi Yesu?

Sa’ad da aka haifi Yesu,makiyaya da kuma dabbobinsu

suna fili cikin dare.

221

222 Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

kansu suka ce: “Lokacin ruwa mai-yawa ne kuwa, ba mu iyatsaya a waje.” (Ezra 10:9, 13; Irmiya 36:22) Babu mamaki damakiyaya na wannan �angaren duniya suke rufe garkensucikin �aki a watan Disamba!

Amma, Littafi Mai Tsarki ya ce, makiyaya suna waje sunakula da dabbobinsu a daren da aka haifi Yesu. Hakika, kamaryadda marubucin Littafi Mai Tsarki Luka ya nuna, “makiya-ya . . . suna kwana a fili kuwa, suna tsaron garkensu da dare”a kusa da Bai’talahmi. (Luka 2:8-12) Ka lura cewa makiyayasuna kwana a fili, ba kawai suna fita yawo ba da rana. Sunatare da dabbobinsu a fili cikin dare. Shin kwatancin kwana awaje ya yi daidai da yanayi na sanyi da ruwa na Bai’talahmia watan Disamba? Ko ka�an. Saboda haka, yanayi a lokacinhaihuwar Yesu ya nuna cewa ba a haife shi a watan Disam-ba ba.�

Kalmar Allah ta gaya mana daidai lokacin da Yesu yamutu, amma bai ba da cikakken bayani ba game da loka-cin da aka haife shi. Wannan ya tuna mana kalmomin SarkiSulemanu: “Nagarin suna ya fi mai mai-tamani; kuma ra-nar mutuwa ta fi ranar haifuwa.” (Mai-Wa’azi 7:1) Sabodahaka, ba abin mamaki ba ne da Littafi Mai Tsarki ya ba dacikakken bayani game da hidima da kuma mutuwar Yesuamma ya ba da �an bayani kawai game da lokacin haihu-warsa.

� Domin �arin bayani, ka dubi shafuffuka na 176-179 na littafin nan Rea-soning From the Scriptures, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

BA LITTAFI MAI TSARKI ba ne tushen ranaku masu tsarki naaddinai da na gwamnati da suka yi kaurin suna a yawancin�angarorin duniya a yau. Menene tushen wannan bukuku-wa? Idan kana iya zuwa laburare, za ka yi farin ciki idan ka

Ya Kamata Ne Mu KiyayeRanaku Masu Tsarki?

duba abin da littattafai suka ce game da ranaku masu tsarkida suka yi fice a inda kake da zama. Ga wasu misali.

Ista. “Babu alamar an kiyaye bikin Ista a Sabon Alkawari,”in ji The Encyclopædia Britannica. Ta yaya Ista ta samo asa-linta? Tushenta daga bautar arna ne. Ko da yake an tuna datashin Yesu daga matattu, ayyuka da ake yi a Ista ba na Kiris-toci ba ne. Alal misali, game da fitaccen “�an zomo na Ista,”littafin nan The Catholic Encyclopedia ya ce: “Zomon alamace ta arna, alamar haihuwa.”

Bikin Sabuwar Shekara. Lokaci da kuma yadda ake yin bi-kin Sabuwar Shekara ya bambanta daga �asa zuwa �asa.Game da tushen wannan biki, littafin nan The World BookEncyclopedia ya ce: Barome Yuliyas Kaisar a shekara ta46 K.Z., ya kafa 1 ga Janairu, a matsayin Ranar SabuwarShekara. Romawa suka ke�e wannan ranar ga Janus, allahn�ofofi, da mafari. An samo sunan Janairu daga Janus, wandayake da fuskoki biyu—�aya na duban gaba �ayan kumabaya.” Saboda haka, bikin Sabuwar Shekara ya samo asalin-sa ne daga al’adar arna.

Halloween. The Encyclopedia Americana ya ce: “Al’adunwannan bikin an samo su ne a lokacin [firistocin Seltikawa]kafin lokacin Kiristoci. Bikin na Seltikawa suna yin shi nedomin allolinsu biyu, ga rana da suke bauta da kuma allahnmutuwa . . . , wanda ake yin bikin dominsu a ranar 1 ga Nu-wamba, a farkon Sabuwar Shekara ga Seltikawa. An saka bikiga matattu a cikin Kiristanci sanu a hankali.”

Wasu Ranaku Masu Tsarki. Ba zai yiwu a tattauna dukanbukukuwa da ake yi a duniya ba. Amma, dukan bikin da akeyi don a �aukaka mutane ko �ungiyoyi, Jehobah Allah baiyarda da wannan ba. (Irmiya 17:5-7; Ayukan Manzanni 10:25, 26) Ka tuna cewa tushen biki na addini zai nuna ko Al-lah ya yarda da shi ko a’a. (Ishaya 52:11; Ru’ya ta Yohanna18:4) Mizanan Littafi Mai Tsarki da aka ambata a Babi na 16na wannan littafin za su taimake ka ka fahimci yadda Allahyake �aukan ranaku masu tsarki na gwamnati.

Rataye 223

Za ka so �arin bayani?Za ka iya tuntu�ar Shaidun Jehobah a www.jw.org.

bh

-HA

13

11

22

MENENE AinihiLITTAFI MAITSARKI YAKEKOYARWA?

LITTAFIM

AITSARKI

YAKEKO

YARWA

bh-HA

Ka ce a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kai kyauta.

s


Recommended